GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

*ABUJA*
Inna na samun kulawa ita da Narim yanda ya kamata Hajiya Jidda Ammyn Amar na basu kulawa malama hardo kuma yana harkar tufkar igiyar shi domi. Yanzu ya kware yanayi yana siyawawa kasuwa suke zuwa in sunyi da yawa suna sari kuma yanzu shine limamin masallaci gidan su Amar saboda limamin masallacin ya Rassu sai Aka nada maalam hardo @Ama’Tsayin limamin,
Inna ruwan mono sunzo wada’tacci yanzu Narim ta bar shan madara sai nono Alhji malam yana kawo mash ziyara sai suna zaune suji ya masu sallama suna dadewa suna fira da shi yana rungume da Narim said zai tafi yai ta kwarara ma Narim Adu,oi yana tofa mata..
Basu da matsalar komai yanzu Narim watan’ta bakwai ko rarrafe bai tai ba ta fara tafiya Ta mulmuje Abinta wani lokaci sai Inna na aiki taji diya na wasa ita kade tana dariya Abin ya fara bata tsoro baya ga haka tanaji motsin Abu cikin dakinta yana tafiya wani lokaci tai tajin tsuwa kamar kukan Tsun tsun shi kan shi malam yanaji watara na da Amar ya shigo Inna ke Ce mashi sai Amar kanji tsuwa daki nan Amar yace Ah Ah to bakaji tafiya ga tafiya nan inaji kamar qadangare Amar yace baiji komai ba kai Inna sai da tasa Aka kira mata maman maryam tai mata gyaran d’aki da kuma bin cike ko tawa qadangare ba,a ga komai ba sai wata rana da Alhji malam yazo yake ce mata kar da tadamu Abokan Narim ne suke taya tawa wasa sannan Inna ta bar da muwa..
*Lagos*
Nuraim ko lokacin da Narim ta fara ta fiya sai da yai mafalkin ta fara wai har yana koya mata ta ta tata tana ta dariya ..
Da safiya Yayi sai yaje yace ma momy din shi yanzu su Narima watan su nawa da haihuwa duk da da man bai ya mance wataninsu bane qarin bayani yake son ji daga momy tace mashi wata bakwai dariya Yayi ya Kali Narima dake rarrafe yace”momy matana ta Ruga diyarki tafiya dan yanzu ita tafiya take Har da gudu momy tai murmshi tace”kai masha Allahu Nuraim iyye kace tafiya kai Lallai Abu ya Yi Gaskiya sai munyi sadaka ei momy Har da party zamuyi momy tai dariya tace ga garumin party ko ..
Sai murna yake itama momy mur na take domin in dai kaga Nuraim na magana ko yana farin ciki maganar Narim Ake shiya sa dan farin cikin shi suke biye mashi,
Sunyi daka ta musamman ta kudi da ta gayan Abinci Har gidan maryu sun kai gudu’muwa duk na murnan Narim na tafiya sai party na musamman da suka hada..
Momy harda gayyatar mutane
Zane da ya Yi maishegen Kyau ga Narim nan tsaye sanye da yan kanti gashinan yasha dauri da bant kowa ya yaba da zanan kai Alhji Bello sai da ya kai wajan masu photo nan Aka mai da shi qaton elage Anyi editing din shi ya Yi Kyau kai kace itace zahiri Aka dauka photo nan…
*Agurguje* kulum Nuraim da Photo na Narim take kwana Aqirjin shi Said Bayan da yaci kukan shi ya gaji sai. Barci ya dauko shi har yanzu ya kasa haqura da rashin Narim,
Yanzu shekaru sunja Su Narim Nada shekara bkwai da haihuwa ya zuwa wannan lokacin duk yana zanta gefe guda kuma ga diyari din shi yanzu yanda shekara sha Biyar ya fara mallakar hankalin shi Abu ga mai girman jiki kai kace dan shekara Ashirinne gashi mata kin secandry karutu yaki ba qaqautawa 6an garan Zane kuwa sai Abin da yaci gaba dan har da na gidaje yakeyi Ana ba shi kudi dan kwanaki har zane wata makaranta yayi Aka ginata Aka ba shi maqudan kudi
Kulum sai ya Yi bitar diyari din shi inda yanzu ya Yi copy din rubutun daga book dina shi zuwa BABBAN book
Yanzu Inna Narim kan taya ta da Aiki ko toilet zata Narim kejan sandar ta tana kai ta haka ma malam ita ke Jan sandar shi tana kai shi masallaci da Rumfa da take zama ,
Tana zuwa gidan Ammy da kanta wani lokaci Amar ya za ya tai da ita yanzu shima Amar ya zama saurayi yanada shekara sha shidda
Ya shaqu da Karim so sai itama ta shaqu da shi haka yake zama in ya dawo makaranta sai yai ta koya mata itama gata da kwakwalwa dan danan ta ruqe hajiya Jidda wato Ammi duk sati take ma Narim gyaran gashi ta wanke shi ta tufke mata shi gida biyu saboda sul6en shi da santsin shi bai kitsuwa kayan masu Kyau da tsada take siya mata.
Inbaka sabi ba baka cewa Narim Yar makahi Ce saboda kulawa da take samu .. Kawarta data maryam Yar gidan maman maryam itama shekarunta bakwai da wata biyu .
Yanda Narima me jawo sandar malam ta kai shi masallaci shine yara suke Ce mata Narim Yar makahi ita kuma tace masu yan masu ido..
Inna itama malam yafara koya mata tufkar igiya ta iya itama tanayi,
Narim tana yawan gani qaramin macije cikin dakin su fari qar da shi Aman bats ta6a gawa kowa ba tasaba da shi ttunkan ta kai wannan shekarun har dauka shi .
Take tana wasa da shi domin shine Abin wasan ta in Amar bai nan ba Abin da me birgeta da shi irin tsuwar da yake to shine Inna kejin kukan shin run Narim Na qarama
Wani lokaci sai Inna taji Narim Narim na guje guje ita kade cikin d’aki tana surutu tana fad’in Wallahi sai Na kama ka to haka za suyi ta wasa ita da macijinta yana gudu tana binshin tana fadin sai taka mashi In Inna ta tambaye ta menene sai Ce ma Inna Abin wasanta ne….
*more comments more typing* *takuce mai son ganin far in cikin Ku da nushadin Ku golden girl*
Ammyn khairat❤????????????❤
*GAMO DA KATAR*
Yar makahi
*Na*
Yar mutan jibiy
*AMMYN KHAIRAT*
*LABARI MAI TA6A ZUCIYA*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*PAGE 1⃣6⃣*
________________???? To dai haka Rayuwa taci gaba da ta fiya Narim Na girma Shekaru Naja Narim Nada shekar takwas Alhaji malam ya fara zo mata A mafalki yana ta fiya da ita makarantar shi
Ahalin yanzu Narim ta sauke qur,ani da litattafe da dama.
Kuma Amar yana ko ya mata Karatun boko wandda dan danan ta harda Ce Saboda harda karatun bokon Ana koya mata A makarantar Alhaji Malam.
Alhaji BELLO shi ya samo ma su Narim da Amar mai koyar da su darasin isilamiya Malam sayyadi..
*Agurguje*
Narim ta fara girma India Inna zaman gida ya ishe ta Ba surasa Ciba Ba surasa sha Ba
Aman tace ma “Malam hardo so take ta fara zuwa Bara saboda zaman da take gida gajiya take da shi ga qafafun ta suyita ciwo Malam ya so hana ta Aman uzurin da ta bashi yasa shi barin ta
Dan haka ta fara Jan Narim suna zagayawa Bara Narim Na ruqe da sandar ta
Ranar da Ammy taji Inna taja Narim zuwa Bara Ba taji dad’i Ba sai take gani kamar INNa Basu gode Abinda take masu Ba ko kuma Abinda take basu ya masu kad’an
Maganar gaskiya bai kamata Ace Inna najan Narim suna zuwa yawon Bara Ba Inji Ammy dan Haka Ammy ta yanke Shawara zuwa wajan Inna taji dalilin ta Na zuwa Bara?
Haka ko Akayi Ammy ta samu Inna da maganar sai ” Inna tace “mata wallahi Ba wai dan kasawarki Ba Ah Ah ai kin mana Abinda ko dan uwanka sai Haka mun gode Allah yasakami da Mafificin Alkairi.
Ka waide saboda ind’an Ruqa motsa jikina da qafafuna kin San zama waje guda NASA qafafu lalacewa.
Wannan shine kawai dalili Ammy ta nisa tace to shikenan Inna kema kince wani Abu Aman dai kin San Bara nada matsala ni dai Inna badan San raina Ba dan dai Babu yanda zanyin INA tsoron diya ta Narim saboda 6ata gari.