GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

“wai Inna in kina bashi ki bashi ya had’a man wa kike nemarwa kud’in bani ba kuma ai naga nike kaiki kina samo kud’in”.
Ta juya ta kalli Mai shayi tace”kai Mai shayi had’a man”. Yace” to Inna yanzu kud’in duka zaki canyesu cikin cikinki ki duba kiga jiya wahalar da muka sha da k’yar muka had’asu ai gara yau na mori abin mu “.
“ki dai mori abinki nida makanta keda cin kud’i”.”Kaji Inna to ai harda ke za,aci dad’in ko baki ci?”. Inna dai ko qala bata qara cewa ba.
hahahaha Inna fa anaso a d’an lasa shiyasa akayi shiru. Mai shayi yana jinsu sai dariya yake bayan ya kammala sai yace”‘ yar makahi an had’a tace “to “.
Inna naji tasa hannunta cikin kwagiri ta fido mashi kud’inshî NARIM ta amsa ta mik’a mashi” .Inna tace “yanzu ko na goro baki ragaman ba?”.”Yi haquri Inna Allah ya bamu kafin muje gida sai ya sake bamu”. Inna tace” hummm”.
“NARIM tashi mutai gida na karya dan qamshin wainar k’wan nan ta cika man hanci baki na sai cika yake da yawu”.
Taja sandar Inna tana cema mai shayi zata maido mashi kofin shi yace” to zo ga sadakar hamsin a saima Inna goro”. tace “yauwa mun gode kin gani ko Inna Allah ya sake bamu “.
Ahaka suka isa gida da sallama malam na zaune kan tabarmar kaba yana saqa tabarma ta kaba da kuma tubar igiya yayi kusan guda ukku,ya d’ago kanshi ya dube su tareda amsa sallamar idanu shi fes dasu aman bai gani dasu aman in ya kalleka za kai tunani yana gani dasu.
NARIM tace” mun dawo malam”.Ta zauna Inna ma ta zauna kan tabarmar da yake zaune nan suka zauna. NARIM ta fito da biredin ta da waina da man had’e suke waje guda tai bisimilla ta fara ci.
Malam yace” yau ‘yar tawa shagali ake”. Inna tace” humm ‘yan kud’in baran jiya ne ta kashe yau ko kwabo ba mu samu ba”.
Malam yace”ai sai da na ce maki kuyi zamanku yanzu bara da kike gani ba,a samun komai cikinta sai qasqantar da kai wani wurin yana maka wulaqanci shiyasa banason kina fita bara na fiso kuyi haquri na saida kabata na kawo maku kud’in ku sarrafa “. Inna tace” aiko malam yau bana yarda inyi tafiya da yarinya nan kaji yanda tai tai man tijara iri iri wai ita yunwa zata kasheta”.
malam yace”NARIM kenan ‘yar Inna da malam in tana jin yunwa kinsan ba lafiya “.
NARIM najin su qala ba tace masu ba duk kiran yunwa da take ruwan shayin tafi sha sosai saboda ita tafi son tasha abu mai ruwa da safe kuma mai zafi.
Sai naga ta dauko biredin da shayi ta dawo gaban mahaifan nata ta zauna tace “Inna kiyi haquri kinji naga kamar ranki ya b’ace inda sabo ai munsaba muyi fad’a muyi shirya ko inna ta”.
Inna tace”ah ah wane irin fad’a, mu ba muyi fad’a ba bari ma fad’i kar ajimu” yauwa Inna ta”.
Biredin ta ciro had’e da k’wai tai bisimilla tana basu a baki inta ba wannan ta ba wanna tare da had’a masu da ruwan shayi duk da ba mai yawa bane haka sukaci kuma ya wadatar dasu suna ci suna sa mata albarka da adu’o’i gareta na Allah ya shirya masu ita ya kuma kare masu ita daga sharin masu sharrin.
Bayan sun cinye sai ta tashi tareda fad’in “Alhmdulillahi ala kulli halin”.
D’aki naga ta nufa d’akunane k’ananan irin nada d’in nan qofar qarama ce sai ka duga ka shiga
wanin qamshin turare ne naji d’akin nayi mai dad’in gaskey tsaye naga tayi tare da ruqe qugu tana dube dube komai take duba oho d’akin tsaf dashi ‘yar katifa ce guda da zanen ta gefe guda kuma da lallausan bargo ne dai an aje gefe.
sai wasu akwatuna guda biyu saman su kuma ga darduma nan ta sallah,zuwa can sai naji tana magana ita kad’ai tana cewa “yau ma kunzo kenan nifa banason haka nan taya ba,a zowa sai na fita ko nayi barci shi wannan qamshi na meye kuke saman adaki?”. Zuwa chan sai naji tsuwar wani abu na kuka d’akin kamar kukan tsuntsu wanda sai ka saurara kaji ba kukan tsun tsun bane!.
Ga binda yake fada cikin kukan nan shi wanda haka muryar shi take” barka da zuwa NARIM “.Shine abinda yake fad’a .
sauran magangaanu kuma ban san miyake fad’a ba NARIM ” ashe kana nan dan Allah ka fito in ganka ni banji abinda kake cewa ba sunana kad’ai na fara fahimtar mi kake cewa kafito in ganka ni kawai ban ganika sai dai inta jin motsinaka kuma ko na duba ban ganinka waye kai?”. Zuwa can sai taji kamar anyi tsoki bata qara jin komai ba sai tace” hummm kullum da nayi maganganuna ko tambaya sai ka yi tsaki kayi nima tsuuut ????”.
“Indai tsaki ne shima ina gane shi karde a qara san yaman qamshi cikin daki ayyhee na dai fad’a maku “.
Tofa kuta yani gani da ji mizai wakana?
ku biyo
golden girl kuji…
Ina son ruwan comments in ban ganiba saina barshi.
~comments d’inku shine k’warin gwiwata~
_vote&share_
*GAMO DA KATAR*
(yar makahi)
*Na*
*yar mutan jibiya*
AMMYN KHAIRAT
*Dedicated to sarauniya Beelat*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*Bismillahir-rahamanir-rahim*
Page 3⃣
*Narim* bayan ta gama magana da mutanan b’oyenta kayan wanki ta fido na mahaifanta domin ta wanke masu bata bari su tara kayan daud’a,ko kala biyu ne suka cire sai ta wanke su ita ke masu wanki yarinya ce mai tsabta,kujera naga ta d’auko tareda botikin wanki da roba.
Ta zauna ta fara wanki tareda waqarta sai naji inna nace mata” *Narim* ba dai wankin bane kike cikin sanyi nan ba?Gashi mura ta sha maki kai dan Allah maida shi sai zuwa azahar rana ta fito”.”Inna ai basu da yawa kala biyu ne na yau da kuka cire, sai nawa kala ukku kenan yanzu na wanke su”.
“To *Narim* Allah yai maki Albarka wai dan saboda mura da kikeyi ne”.” Karki damu Inna mura kuma ai ta riga data kamani sai dai tai man sauqi.”
“To Allah ya kawo maki sauqin”. Amin Inna”.”Yauwa gama kizo ki sayo maganin mura” .”To Inna kin san nifa ban shan magani ita mura kuma maganin tana man kai”.
“Na man kai Inna mai dan romo romo”. Tofa kee *Narim* bakinki ya san makwantar dad’i”.”Hahaha Inna kenan wayaqi dad’i sai in bai samu bah ko baba?”. Babanta yace” haka ne *Narim* kowa ma yana son dad’i maza gama wanki mutai kasuwa naga tufkar igiyar nan da tabarmar sai mu saido sai mu biya ki sawo naman kan”. “Yauwa Baba yanzu kuwa zan ida yau zamu sha dad’i d’anye zamu sayo Baba ni zan dafa mana shi”. Yace” to”.
“Gama sai mutafi”. Inna tace” yanzu malam biye mata za kai kuka so kud’in maimakon ayo cefane da siyo kayan abinci sai ka biye mata asiyo nama gaskiya da zakaji shawarata kar asiyo naman nan”.”Kaji Inna kuma in ansiyo sai kinfi kowa ci”.
“Hummmm *Narim* kenan Malam kada ka biye mata dan Allah qara ayi malaiji kaga bara nan ko anje basa mowa ake ba balle muci in mun canye anjima mu koma”.
Malam yace”ba komai ni daman ban son kuna zuwa bara nan in dai kana sana,a ai komai mai sauqi ne tunda Allah ya bani baiwar yin abubuwa ko kana gida anzo asiya”.
*Narim* tace “haka ne baba Allah ya bada sa,a muruqacin gumenmu kulum muna shan dadi kama gidan su Amar”.
Baba yace”. Ameen ‘yata”. Bayan ta gama wanki tayi wanka duk kuwa bala,in sanyi da ake sau ukku take wanka kuma da ruwan sanyi da safe da zasu bara tayi yanzu kuma gashi tayi *Narim* kenan ba dai tsafta ba ‘yar ga Inna da malam ‘yar makahi inji mutane sunan da suke mata kenan itako tace” maka d’an masu ido”