GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Inna tace gskiya ne Ammy kema kinyi magana to Amman yawon namu Ba mai nisa bane iyakarmu cikin unguwa to shikenan Ammi tace” Allah ya tai maka “Ameen” cewar Inna .
Haka Ammy tayi gida jikinta Asanyaye saboda bata so wannan Bara Ba .
Haka dai Inna duk safe da yamma take Jan Narim zuwa Bara Wanda kulum sai sunyi fad’a kan hanya wani lokaci in Narim bata so zuwa Bara Ba ko sun kawo kwata bata cema Inna kwatace sai ta barta ta cha6a qafafunta ciki,
Abunka ga makaho haka Inna za tai ta bala,I kan hanya, wani lokaci kuma sai sunyi Nisa da ta fiya Narim zataja ta tsaya ta kuma fashe ma Inna da kuka tace” ita ta gaji yunwa take ji su koma gida,
Ita kuma Inna tace bata komawa ita kuma Narim sai ta samu waje ta zauna tai ta rusa kuka tace”Ba inda zata ita yunwa takeji kokuma tace Rana ta isheta Inna tayi tayi Narim ta ta shi su tai Narim taqi ta shi duk Wanda yazo wucewa sai ya masu magana Wanda da qyal zasu lalla6a Narim sannan ta ta shi wani lokaci ko tace itafa yunwa takeji uwar’hanjinta ta qulle bata iya ta fiya sai A tambaye ta mitake son ci sai tace shayi haka za,a siyo shayin Akawo mata wannan durama tasu Ba qaramin birge Mutane take Ba ,
Narim Nada farin jini so sai Na jama,a duk inda ta wuce zakaji Ana fadin Narim Yar makahi itako ta kance Yar masu ido ko dan masu ido
In kaga yanda suke da Inna in zasu bara to dolle sai kadara mutune har tsayawa Ake kallon dirama su saboda farin jini Narim Inna na samun kudi so sai
*Agurguje* Yan zu Narim Na da Shekara kusan sha Ukku da Haihuwa Abu ga mai girman jiki inka ganta za kai tunani ta kai sha shidda A kwai qugu da nonuwa Aman ba tada qiba doguwace wankan tarwad’a
Ko ba,a fada ba kunsan Narim kyakyawa Ce so sai
Ya zuwa yanzu Amar Na da shekara Ashirin da shidda ya gama karatun shi na secandry… Yana shin zuwa malaishiya qaran karatu kuma yanzu soyayyar da take ma Narim Abin Ba,a magana yana sonta so sai yake matuqar sonta kulum yana tare da ita haka ita ma barci kade ke raba su
*Lagos*
Nuraim kyakyawan mata shin saurayi dan kimani shekaru 25
Kyakyawa ne so sai fari Wanda farin shi har wani yellow yellow yake dogone mai mujajen jiki da faffadan qirji mai yalwan sumar kai baqi qirin da ita idan kaga Nuraim bazaka ta6a cewa ba haushe ne ba saboda bai Yi kama da hausawa ba yafi kama da larabawa.
Nuraim kenan hamshaqin mai kudi kuma yasha hara Akan drowned na komai jahar Lagos da kewayan ta suna Alfahiri da Nuraim .wajan Zane
Yanzu haka satin shi biyu da dawo wa daga qasar waje wajan qarin sanin hanyoyin Zane Alhmdull ya zama qwarare ta fanni Zane
Yanzu haka zaune yake cikin wani Hamshaqin d’aki
Kan kujera ya qurama waje guda ido
Wani qaton photo ne nagani na wata kyakyawar budurwa sanye da sari ya Yi matuqar Yi mata Kyau shi ne sai kallon photo n yake ko qyaftawa bai Yi .
Sai da Na kalli photon da Kyau na Gane Ashe ba kowa be Narim Ce duk illahirin daki photo nan tane gasu nan da yawa su tun tana jaririya wasu tana zama wasu tana Rarrafe wasu tana tsayuwa wasu shekara ukku .
Ga sunan birjet photos kala kala tundaga na shekara daya har yanzu da take da shekara sha,ukku,
Wata kyakuawar budurwace Naga ta shigo d’akin da sallama ta zauna kusa da shi ba tai magana ba photon da yake kallo ita mashi tabi da kallo ta jima tana kallon photon sannan tai Ajiya zuciya tace Gaskiya Anty na Ba dai Kyau ba..
Aman duk Kyanta A dai Nafi ta Kyau naisa ba kusa ba
Sai A sannan ya bar kallon photon ya maida kallon shi ga budurwa da ta shigo murmushi yai mata sannan yace ke ma dai kin fad’a ne ban hanaki shigo man d’aki A wannan lokacin ba in INA ganawa da iyalina na fad’a maki ki dai na shigo man ? Kai yaya Nuraim dan Na shigo shine laifi ko dan Nace nafi Anty Narim Kyau to Yi Haquri Ai kasan kai ma fada kawai Nayi Ai har’ yanzu
Ba a haifi maccen da zata kai kyan Anty Narim ba kuma Baza A haife ta ba ko ya ya Murmushi ya Yi sannan yace Narima naji ta shi fita ban cikin yanayi mai dad’i fita in anjima zanne meki cikin tausa yawa tace to yaya Aman dan Allah ka kula kaji ta qarashe idanuta cike fa qawlla na tausayin yayan nata okay yace mata ita kuma ta ta shi ta fita.
Narima kenan yan Matan momy Shekarunsu daya da Narim ba laifi ita ma tanada nata kyan sai dai baqace man ba baqa wulik ba tanada tsayi da jiki tanada yan nonuwanta ba laifi sun cika hannu tanada qugu da hips yanzu Narima tana babbar makaranta Aji ukku A secondary.
Tunda Narima ta fara mallakar Hankalinta tasan halin da yayan ta yake ciki na qunci da rashin walwala bai da lokacinta A matsayin ta na qanwarshi ba shida time din kowa sai na photon Narim
Wata rana bai nan ta shiga dakin shi duk wani photo na Narim sai da ta jiqashi da ruwa barna tai mashi sosai lokacin Tanada shekara 8. Kuma momy ta bata labarin Narim da yanda yake matuqar sonta
Ita kuma Narima taji haushe haka dan haka taje tai mashi Wannan Aika Aika
Dawo warshi kenan daga makaranta ya tarda tana mashi wannan barman A rana Narima race bugu Wanda tunda tazo duniya ba,a ta6a Yi mata shi ba
Dan sai da ya sumar da ita ran momy ya6a matuqa da bugun da yai ma Narima dan haka ita ma cikin Fadi ta Runqa dukan shi baji bagani Nuraim ya bugu.
Nuriam ya Yi fushi sosai Wanda har ya kai da ya Rife kan shi cikin daki baci ba sha
Ita momy ta Yi Nata Fushun taqi kulashi gashi Aljahi Isah bai nan yana Dubai
Narima na San yayan ta kulum sai tazo qofarshi tana buga mashi ya bude mata Aman shuru ta shiga da muwa sosai Alokacin duk da Qarancin Shekarunta tasan Abinda tayi bata qyuta ba..
Shiko Nuraim yaci kuka har ya gode Allah da Abinda Narima tai mashi saboda yanzu ya kwana biyu baiyi mafalkin Narim ba balle ya qara ganini kamaninta ya zanata .
Bai da Aiki sai na zanan ta sai yazana yaga baiyi ba bai kai Zane da Narima ta 6ata mashi ba haka zai ta kuka duk ya 6ata dakin da ta kardu momy Na bude dakin da key bata Ce mashi komai saboda cikin haushin shi take tana Aje mashi Abinci da Ruwa ta fita da yaga ta fita zaije ya sake Rufe dakin shi Abinci dai bai ci Aman yakan ta shi ya Yi sallah ya koma Aikin Zane shi haka momy zata dawo kawo mashi wani Abinci sai ta tarar bai ci Wanda ta kawo ba Abinna damunta sosai duba da yanda yarame
Wasa wasa kwana biyu Nuraim ya kasa zana photon Narim Wanda kala yana kuka da hawaye har ta kai da ya dai na sai Na zuci har qagara yake dare Yayi ya kwanta barci yaga koyayi mafalkin Narim Aman Ina baiyin mafalkinta zazza6e mai zafi ya rufe tare da tari mai tsanani Wanda da Yayi tari sai jini bai ta6ari momyn shi ta gani ba da dai momy taga Abi bana lafiya ba ne ta sauko daga fushin da take tana kula da shi da kuma kwantar mashi da hankali ta kira likita ya duba shi yabashi magani masassara
Kuma Narima tazo ta bashi haquri sannan ita Narima da ta dawo makaranta tana wajan shi kala bai kulata har ya kai yana kulata kuma har yanzu momy bata San yana Aman jini ba wata rana suna hira shida Narima yana bata labarin Narim da kuma irin yanda yake son ta tari ya kamashi kafin yai wani yunquri ya tai toilet har jini ya zubo mashi hankalin Narima ya ta shi sosai ta fashe da kuka yaya Nuraim jini. Ba jini bane Narima wallahi yaya jini to shikenan Aman kada ki’saki kigayawa momy in’kika gaya mata zamu 6ata.tace to yaya bazan fada mata ba in dai bamu 6atawa yauwa qanwata bazamu ta6a 6atawa ba kinko sau tari Narima na ganin jini ga yayan ta sai tayi kamar tafadma momyn ta sai ta tuna da yace kar tafada