GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Haka take haquri ta qyale did da tana yarinya A in Na damunta
Ba laifi yau da daddare ya danji qarfin jikin shi dan haka ya dauko takardun shi yaga ko zanan zaiyi harda Narima wajan taya shi Zane sun jima suna zanen Aman still bai yiba har wajan Sha day an dare suna Abu guda Zane yaqiyi yace Narima ta shi kike ki kwanta tace to yaya ni banjin barci ko musake gwadawa ya dubeta yaga barci cike da idanunta yai murmushi yace tashi kije qanwata goben mun sake gwadawa tace to yaya sai da safe ka’ kula yaya oky yace da ita yanzuko yana son Narima sosai Yar shaquwar da sukayi tana dan debe mashi kewa.
Haka ya kwanta da tunani zuci koko nace da kukan zuci Wanda ya zame mashi jiki kulum sai Yayi
Barci ya dan dauke shi yai mafalkin tsoho nan da yake mafalkin shi yanzuko ya jima Rabon da Yayi mafalkin shin An’dauwo shekaru tada shi tsohon Yayi yana mashi murmushi yace yaro tashi mu gaisa kwana biyu ba mu hadu ba Nuraiim ya murza idanun shi da barcci bai sake shi ba yace Baba da kanan INA katafi wanan ba kwana biyu bane shekaru me tsohon yai dariya yace hakane
Yaro nayi tafiya Ce mai nisa Aman kulum INA tunanika kana rai na da kuma irin Halin da kake ciki Na gaya maka ka dai na da muwa Akan Narim domin ita din ta kace komin daran da dewa zata dawo maka Amanfa Akwi qura baya dan sai ka dage sosai wajan Adu,a domin Akwai wani yaro matashi kama Wanda yake da kudanci da ita kuma shima yana sonta sosai kamar yanda kake sonta saboda haka ka dage da Adu,a lalai zata dawo maka Aman in kai wasa zata so maka Amatsayi matar wancan saboda haka ka dage da ga yawa Allah bukatunka bawai ka tsaya kana kuka da Zane Zane bah Nina zan tayaka Da Adu,a
Nuraim ya fashema tsoho da kuka yana fadin Baba wane ne shi yarasa wadda zai so sai matana haba Baba ya za yai man haka duk son da yake mata bai kamoni ba
Tsohon gani Hankalin Nuraim ya tashi ya jawo shi jikin shi yana buga bayan shi tare da to famashi Adu,oi domin jikin Nuraim har Rawa yake cikin sigar lallashi tsohon yace haba kazama Namiji magana ban San kana karaya ka kwantar da Hankalinka kayi yanda nace .
To shikenan Baba Cewar Nuraim yace Zane ta da nake gani yana debe man kewarta yanzu Narasa shi ya zanyi tsohon yace to shikenana zaka zana ta Nuraim yace Baba Nakasa zanata Ai Baba tsoho have dauko kayan Zane yanzu zaka zana ta Nuraim ya sauka kan gado yaje ya dauko kayan zanen shi ya dawo Baba tsoho yace matso nan kaga Nuraim ya matsa kuda da tsohon ya Rife mashi idanu sannan yasa hannun shi kan pencil da takardar yace ta cigaba da zanen ka Ai kana ganinta yanzuko Nuraim yai dariya yace sosai ma gatanan INA gani
To ciga ba da zananka haka yai ta zanata Tiyan tiryan kusan kalla ukku Yayi sai da ya gama sannan tsohon ya buds mashi idon shi yaga zanen shi lafiya lau ga Narim nan har yafi zanen da yakeyi Kyau sai tsohon yace mashi kayi farin ciki ko Nuraim yace sosai ma Na gode da tai Makon da kai man tsohon yace to kwanta kai barci ni zan tafi said wani lokaci Nuraim ya maida Zane shi wurin da take Aje Zane ya dawo yace to BaBa nima Na gode tsohon yace BABAN ka bai nan Aman zai zo maka Da Abin mamaki meyai shi inji Nuraim tsohon yace bazan fada ba sai yazo zaka gani Nina wuce said Anjima ..
Bugun qofar daki Ce ta ta da Nuraim daga Barcin da take qarfe ba kwai da Rabi Na safe ya makara ko sallah Asuba bai Yi ba bude qofar ya Yi Narima Ce cikin shin school yaya baka ta shi ba ko jiya Zane Kai tayi ba kai barci ba tuna mashi tayi da mafalkin da Yayi sai yace mata me INA tunanin nayi zanenan ai Narima tasake jikkar makaranta tana murna tace yaya yana INA da hannu yai mata nuni da ta kardun Zane da gudu tai wajan takardun ta dauka Rana tsalle wallahi yaya kazana ta tayi wajan shi ya Amsa ya gani ranshi ya Yi fari mafalkin da Yayi yazama gaskiya toilet ya shiga yai Alwalla yai sallah ita kuma Narima tai dakin momy tana gwada mata ita ma momy tayi murna sosai.
Bayan kwana biyu komai ya lafa Alhj Isah ya dawo saga dube Abin mamakin Nuraim shi me Abinda Abban shi ya kawo mashi Wanda shi har ya manta da shi bakomai bane said photon Narim Wanda Akai mata elage din shi shine ya tai da shi Dubai Aka sake gyara shi Akai editing din shi murna ga Nuraim da Narima Ba,a magana
Narima itace Abikiyar Nuraim da ita haka hira ita take gayawa da muwarshi Narima ta San sirin Nurai sosai ko momy bata sani in ta gan shi cikin da muwa ita ma tana Shiga damuwa sosai hirar Narim Ce kawai zatai mashi ya jidadi ..
Yanzu haka korar da yai mata tunani Amar ne ya cika mashi xuciya domin Yayi mafalkinta suna tare da Amar har nuns fada kanta shida Amar wannan. Mafalki ba qaraimin ta da mashi hankali ya Yi ba ..
Ko tafiyar shi qasar waje yasha mafalki irin haka na faruwa da shi kuma Abin mamaki Amar me nasara yasa damuwa so sai wadda ta kai har ciwon zuciya ya kwantar da shi Yayi jinya so sai batare da Sanin mahaifan shi ba saboda qin gaya masu Yayi yanzu haka sati biyu suna bashi. Ya dawo za ai mashi Aiki Azuciyar shi Aman. Gashi. Sati biyun ya cika bai koma ba
*more comments more typing*
Ammyn khairat Ce golden girl
*GAMO DA KATAR*
(Yar makahi)
*NA*
Yar mutan jibiya
*Ammyn khairat*
*LABARI MAI TA6A ZUCIYA*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*PAGE 1️⃣7️⃣*
*wannan page sadaukarwa ga yan group gamo da katar na gode da qaunar da kuke man da kuma novel dina musamman su Ummul khairi da Nusaiba da sauransu na gode INA jin dadin comments dinku Allah yabar so da qauna Ammyn khairat na godiya????????❣️*
___________________________
*ABUJA*
_____________????Narim kwana biyu kenan bata jin dadin jikinta; Amman dai ba kwance take bah yau ta d’anji dama dama bayan ta gama aikin ta ta gyara komai sai ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya kanta cikin riga da suket yan kanti sunyi mata Kyau so sai colour din sun colour Ce mai kyau peank da White simple kwalliya tayi ta tufke lallausar gashin kanta mai tsawo da tsansi yanda India kema kansu gyara haka ta gyara na ta ta tufke shi ya sauka a gadan bayan ta
Ta kawo hulla bandana tasa irin Yar hullar nan ta yara wadda Ake sawa tsakiyar kai ko kuma nace gaban goshi????itama peank ce tayi kyau so sai shigar ta fito da zallar yarintar ta kasan cewar sket din ya tsuketa daga qasa Aman ya bude hips dinta ya fito so sai hakama rigar mai dogon hannu ce itama ta kamata nonuwanta das dasu irin kyan da tayi sai wanda ya gani kamar yar India zahiri ni kai na ta birge ni turare ta fesa sannan ta koma kan kujera ta zauna saboda jikin ta ba qarfi bata jin dadin jikin koka d’an ga faduwar gaba da takeji ita kanta INNA ta San Yar tata bata jin dadi kwana biyu domin ta rage wal’wala bata zuwa ko Inna kuma ta tambaye ta tace ba komai jikin dai ne bata jin dadin shi
Amar sai da ya kira Dr. Din gidan su ya duba ta yace maybe zazza6e ne domin shi bai gano komai ke da munta ba Amar ya shiga da muwa so sai da rashin wal’walar Narim shima duk jin shi yake A dame kulum yana gidan su ya sata gaba da tambayoyin mike da munta Aman Amsar daya ce bata jin dadin jikin ta take cewa