GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Zamanta keda wuya sai ga maryam kawarta ta shigo ita ma tayi tata kwalliyar Bayan sun gaisa da Inna ta nufi d’aki inda Narim ke zaune
Kawata ya jikin Maryam ta tambaye ta jiki da sauqi wallahi Baki ga yau harna danyi kwalliya ba ei na gani kinyi kyau so sai wallahi sai qamshi kike ina mutumen bai shigo ba maryam ta tambaya wallahi bai shigo ba to dan halak kaqi Ambato Narim ta fad’a saboda suna maganar Amar ne sai gashi tsaye bakin qofa
Sallama yai masu ya shiga bayan sun gai’she shi ya samu daya daga cikin kujerun d’akin ya zauna
Karku manta yanzu gidan su Narim An gyara shi Amma shi gini na zamani so sai d’akuna biyu ne ciki da parlour da toilet ga kujeru na Alfarma An zuba masu shegen kyau
Duk wannan gyara Aikin Amar ne da tai makon mahaifin shi,
Tunda Amar ya shigo hankalin shi naga Narim baqarimin kyau tai mashi ba sai kallon ta yake shi kade yasan miya keji game da ita jin gina Yayi da kujera ya lumshe idanun shi tare da karkad’a qafafun shi My Amar lafiya kake ka shigo kayi shuru “? Inji Narim take tambayar shi idanun shi ya bude ya zuba su Akanta itama shi take kallo zuwa can ya janye idon shi yace mata lafiya lau nima ban jin dadin jikina yau cikin tausayawa tace Ayya mike da munka my Amar gani zata tada hankalin ta yace mata kai na ke ciwo nasha magani zai sauka karki damu tace da muwa dolle ce Allah ya baka lafiya maryam tace Ameen
Maryam ta kallo Amar tace yaya Amar ko dai ko dai
Ko dai ko dai me
Yace da ita ko dai Antyn muce ta ta6o ka idanu ya waro yana kallon su itama Narim kallon shi take sai Fiji fiki yake da ido kamar Wanda yai ma sarki qarya dariya ya basu suka bushe da dariya Narim harda ruqe ciki take.
Ba qaramin farin ciki Amar ya samu kan shi ba gani Narim cikin farin ciki yanda take dariya ya sa shi jin dadi ba kad’ab ba domin Aduniya ba Abinda yake so irin yaga Narim cikin farin ciki domin farin cikin ta shine na shi Wal’walar ta itace wal’walar shi jin dadin ta jin dadin shi da muwar ta da murwa shi ko wanne hali ta shiga shima ya shiga yana mahaukacin San Narim so sai yake mugun son ta so mar musaltuwa sau tari yana son tun karatta da maganar sai yaji ya kasa gani yake kamar bata isa soyayya ba dan haka ya barma zuciyar shi har yazuwa wani lokaci,
Tsaida dariyar su sukayi tare kuma da karun Baki suka nuna shi da ya tsa ya ya Amar daga anyi maganar budurwa sai kai ta Zara ido kamar Wanda yayi qarya
Murmushi yayi sannan yace dasu to ai tambayar ce taku ta zoman bazata ni yaro dani ina ni ina budurwa balle har’ta6a taman rai,
Maryam ta far da idanu tace lallai ma yaya Amar kai’d’in ke yaro komu dake qannan ka ai munada samari sake zaro ido Yayi tare da dafe gaba samari kuma kuna yan yara daku hardake Narim yaushe kika fara samari ban sani ba na shiga ukku ni Amar .
Ah ah to kai dai ke ba kasani ba dan yanzu zowar danayi dan naba ma qawata labarin New saurayin danayi kaga nama manta cewar maryam tace Kawata mama fa tace nazo naga in kinanan zasu zo ita da kawata zaki basu magani kinga ni nama manta .
Aman na San dan kawartata bata zoba da yanzu sun shigo oky sai sunzo inji Narim .
Amar yayi gyaran murya yace dan Allah Narim fada man gaskiya wai da gaske ne kinada saurayi duk ya marai’rai ce Yayi kalar tausayi .
Narim tace my Amar zolayar’ka take ita dai keda samari ni ba ruwa na da samari duk Wanda yazo ban sauraran shin dan daga cikin su babu kalar saurayin da nake so kai ni har’yanzu banga kalar mijin da zan Aura ba domin ni INA son mijin da zan Aura ya kasance yana da wadannan Abubuwan .
1
Ya Kasan ce yanda Aji mai ilimi ne na isilam da na book
2
Ya kasan ce yanajin ya ruka da dama
3
Ya zamana cewa dogo ne shi kuma fari
4
Yakasan ce kyakyawa ne so sai
5
Ya zamana cewa kyawon shi tamkar balara be
6
Yazama yanda wata baiwa ta musamman
7yazama cewa duniya ta San da shi kokuma jahar shi
8
Yazama ba cewa yana matuqar sona zai iya bada rayuwar shi domin ni
9
Ya zama mai tausayi
10
Yama mai tai makon Al’umma
11
Ya kasance mai matuqar haquri da jajir cewa
12
Ya zamo mai kishin iyalin shi
13
Ya zama mai man Uzuri Akan komai Na Rayuwa ta
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta Dora da cewa ba suke nan Abinda nake so mijina ya kasance da duba .
Wannan kad’ane daga cikin su
Tapdi maryam tace gaskiya kawata kin d’aibo da zafi yanzu A wannan zamani ina zaki samu duk mai wad’annan Abubuwa da kika lissafa Narim taye dariya tace kawata kenan zan samu insha Allahu ina fad’a ma Allah domin shine mai badawa idan har’za6ina Alkairi ne INA rokon Allah da ya cika man burina
To shike,nan cinda kin ce Allah ai magana taqare shiko Amar tunda ta fara lissafin kalar mijin da take so kan shi ya kulle yama rasa ta cewa .
My Amar kayi shuru Ai dai zan same shiko ko kafin ya bata Amsa sai ga sallamar maman maryam da qawarta sun shigo .
Inna dake dayan d’akin tana tufkar igiya itama ta Amsa masu sallamar da sukayi tare da fad’in maman maryam maraba lalai maman maryam tace yauwa Inna Aiki Ake tayi Ina yarannan naki ko ba sunan tundazun na aiko maryam wajan Narim ta sanar da ita zamuzo da kawata ta bata magani Aman shuru bata koma ba Inna “tace wallahi maman maryam kin San Sha ani yaran nan sai su in suka hadu man tawa ma suke da komai kuwuce suna ciki to shikenan bari mushiga daga ciki Inna tace to d’,akin dasu Narim suke suka isa Bayan sun gai’sa
Sai maman maryam tace Narim da man kawata ce narako wajanki akan wata Marsala Aman tai maki bayani da bakinta kiji Narim ta nisa tace ni kuma mama to ni wanne taimako zan iya Yi mata mike da munta wacce irin matsala ce kuma ni ai bawani Abu nake badawa ba har qara magani da nake ba yan nan unguwar na matsalar kuraje ko wanin Abun. Ei duk da haka ki saurata dai kiji ta bakin ta Nita fara gaya man cewa wai ko mafalki tayi Ance tazo wajanki Aman dai kiji daga gara ta zafi ke maman Umar Yi mata bayani taji
Wadda Aka kira da maman Umar ta gyara zama tace yata kamar dai yanda tai maki bayani haka Abin yake yau kimani kwana ukku kenan INA mafalki dake na inzo wajanki Akan wata matsala dake damu na
Ni dai Ahalin yanzu banda Aure mun Rabu da mijina dan mu daya da shi kuma chan na barshi gidan urban shi to yanada Mata Aman matar tana cuta mashi tana bashi wahala so said
To yanzu dai A ta qaice An nemi yaron Anrasa kimani wata biyu kenan Abin na damuna dukk inda Ake tunani yaron Anje ba’a same’shi ba Any in shelar yaron har’ gidan redio Aman bawani labari to kinji Abinda ke tafe dani.
Narim ta jin jina kai tace naji aman Ni babu wani Abunda zan iya Yi maki face Adu,a Allah ya bayya na shi Ameen suka ce su duka domin sun tausayawa matar matuqa hankalinta duk A tashe yake Inna ce ta shigo d’akin tana dogara sandar ta Amar ne ya kama ta ya zaunar da ita kan kujera .
Matar tace dan Allah Narim ki tai maka Mani saboda nasha mafalki dake Akan kece zaki gano Mani India yaro na yake ni kuma cewar Narim ei ke .
Narim tayi shuru bata sake cewa komai ba tsawon wasu mintina d’akin ya Yi shuru kowa da tunani da take na wannan Al’amari sai suka ga Narim tayi zumur ta ta shi kamar An’tsikare ta da ido suka bita da kallo darduma da turare da cabzi shine Abinda ta dauko ta dawo gaban matar nan ta shinfida ta zauna Akan dar’dumar sannan turaran da ta dauko ta feffesa shi a cikin d’akin gabas da gamma kudu da Arewa sannan ta komo ta feshe jikinta da shi so said take fesama jikin ta turaran musamman ma kanta duk sunyi zuru sun zura mata ido Suna kallan sarautar Allah harda Inna daba gani take ba