GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Kulum Ammyn ita kema Narim wanka domin bata iyayi da kanta Alwallar ma yanzu sai Ammata domin hannuwanta basu iya daukar komai
Narim tazama Abin tausai dan in kaganta sai ka koke ta Amar bai da aikin da ya wuce kuka da Adu,a haka ma Inna gani suke kamar Narim din mutuwa zatayi malam hardo ne kawai mai dan taurin zuciya domin ita kanta Ammy in tanama Narim din wanka har kukan take sai dai Narim din tai ta girgiza mata kai Alamar tayi shuru to duk Wanda taga yana kuka haka take mashi
Alhji Bello shima da yazo yaga halin da Narim ke ciki sai da ya koka kuma ya kira likitan shi ta duba Narim duk wasu Aune Aune sa gwaje’ gwaje Am’mata ba’a gano komai ba
Iya damu cikin damuwa suke
To haka Al’amarin jinnu suke duk yanda suka kai ga sonka to sai sun wahalar’da kai
To Narim sai muce Allah ya dawo sauqi ????????????????????
Bara mu leqa Nurem danjin shi wanne hali yake ciki
*Lagos*
Gidan Alhji Isah momy ‘momy duk inda Hankalinta yake to Atashe yake batada kwanciyar hankali ko kad’an .
Tsawon sati daya kenan tana fama da mafalkin mahaifiyar Narim kulum ta kwanta barci to sai tazo mata tana kuka da hawaye tana fad’n kincin Amana ta banyi tunani zaki watasar da Amanar da na bar makiba nayi tunani nama Narim gata na barinta wajanki Ashe bahaka ba ne na gode da Abinda ki kai man sai kuma ta6ace mata kokuma ita ta falka daga bacci yannan Abu yana matuqar da munta kuma yasata Adamuwa so sai
Kuma yanzu ta tabbatar da Narim duk inda take to tana rai da dai tana tababan hakan aman yanzu yawan mafalkin mahaifiyar ta yaqara tabbatar mata da Narim din na raye kuma duk inda Narim take to tana cikin wani hali marddadi saboda tana jin haka ajikinta duba kuma da mafalkin uwar da take da Narim na cikin qoshin lafiya ta tabbata bazatayi mafalkin uwarta ba duba da tarin shekarun da Aka dauka bata ta6a mafalkin Uwar Narim ba sai wannan lokacin da jikinta kebata da Abinda ke faruwa da Narim!!!!
Kulum adu,ar ta itace Allah ya bayyana mata Narim cikin qaushin lafiya
Yanzu da take wannan tunani jikar da mahaifiyar Narim din Ce taba ta tace mata komai Narim yana cikin kuma kar taba Narim jikar nan sai ta kai shekara Ashirin ko Ashin da biyar lokacin ta mallaki hankalinta
Tana son buda jikar Aman takasa sakamakon tunani da tayi na baika mata ta ga shin jikarba saboda haka ta maida ta ta Aje inda ta Adanata kuma haryau babu Wanda yasan da zaman jikar sai ita.
Tana cikin da muwa so sai Akan wannan lamari musamman ma ciwon Nurem da yaqici yaqicin yaiwa domin Narima ta fad”a mata duk halin da Nurem yakeci na rashin Lafiya Wanda itama taga hakan Atattare da shi
Domin a tsai tsaye ciwo ke cin shi da kagan shi ko ba’a fad’a ba kasan ba shida lafiya domin ba shida kuzari ko kad”an
Ya Rame ya qare bakomai cikin shi sai dogon wuya da tsini hanci sai uwar sumar shi data qara fito da ramarshi
Yanzu da ciwo yai tsanani sakamakon yawan bugun zuciyar shi da take buga mashi da qarfi qarfi kuma sai yaji zuciyar ta shi na tsira mashi tana mashi zugi kamar tanajan Ruwa
Ga tari daya Addabe shi daya Tara sai Aman jini jinine yake Amayowa baqi qirin da shi .
Nurem ya tabbatar da Narim din shi ba lafiya duba da mafalkin ta da yake cikin wani hali yake ganinta mar’musaltuwa kulum yana ganita A kwance ne cikin matsane cin ciwo
Wannan Abu ya qara hardasa tashi na shi ciwo .
Yau dai gidan A hargitse ya ta shi saka makon ciwon Nurem da ya tsanata
Narima ta shigo d’,akin shi da safe ta iske shi kwance ba numfashi ga Aman jinin yayi yana kwance A cikin shi ai da gudu ta fita ta gayawa momy da Abban su halin da dan Uwan nata ke ciki sai kuka take tana fada masu yaya Nurem ya rassu .
Da gudu sukyi dakin shi cikin kaduwa bakin gadon sukaja birki momy ta tatta6a shi takara kunnanta sai tin zuciyar shi taji shuru bata halbawa ta duba hannun shi nan ma shuru ai sai ta yanke jiki ta fad’i Narima ko ta sake Rushewa da kuka tai kan momy tana girgizata mommy momy mommmmmmmmmy kita shi dan Allah kar Ku mutu kubarni ta ta shi tayi kan Nurem yaya yaya yaya yaya Nurem dan Allah ka tashi kar ka mutu ta shi kaga momy ta fadi ta shi mu kai ta hospital kaji yaya yauwa yaya na ta ta shi yaya Nurem dina ta shi nice kanwarka ta shi dan Allah ta shi yaya ta shi na baka labarin Anty Narim ta shi kaji jiya munsha hira da ita har tace na gai’she ka kuma tace man tananan dawo’wa kaji to kaji yanda tace ko kayi farin ciki ko yaya LA yaya ta shi gama tanan ta so ..
Shuru dai ita keta ta sabbatun ta yaya ta fashe da kuka dan Allah yaya ka tashi ta kuma ta shi ta koma kan momy momy tana girgiza ta ta daubo ruwa ta zuba ma momy Aman INA momy batako motsa ba!!!
Dul Abinnan da Narima keyi Abbanta na tsaye kamar butum butumi kallon ta kawai yake Kallon shin Narima tayi race Abbah kayi tsaye lace wani Abu mana tayi wajan shi ta girgiza shi faduwa zanne Yayi idanun shi sakayi lum zai lumshe su Ah’ah ‘ah Abba Inji Narima ka tashi dan Allah tasake girgiza shi cikin kuka zuwa can ko ya dawo gaya cinshi momy ya sunguma yai waje da ita cikin mota ya sata ya dawo ya dauki Nurem shima Narima na biye da shi sai kuka take ma aikatan gidan sunyi cirko cirko suna jimamin lamarin ..
Hospital suka nufa An duqufa kansu dan veto Ratuwar su Anti Nasara momy ta dawo hawan jini nai yai mata mugun kamu jint ya hau sosai ..
Da ta ta shi ta dan ta take sai fadi take INA my boy INA Nurem Alhj Narima INA dan uwanki ko dai ya mutum da gaske likita yace kwantar da hankalin dan Allah Baki da lafiya jininki Yayi mugun hawa komai zai iya faruwa fake to likita taya hankalina zai kwanta INA Dana yana bai mutum gashi can Ana qoqarin gani An veto ranahi .
Said Adu,a Duke Narima baiwar Allah sai zaryya take bakn d’akin da Akasa Nurem Adu,a kawai take
Anyi Nasara numfshin shi ya dawo kadan sanan
BABBAN likitan Hospital din yai masu takarda dan FIta da shi qasar India. Yau yau dinnan yace masu domin INA aka wuce yau zasu rasa dan su Aljhi Isha ya tai gida ya hada duk Abin buqata komai sun shirya jirgin qafe 4 zasubi suna hospital din hudu tayi da mortar Hospital din Aka kai su air part
Yanzu dai jirgin su ya daga qasar India harda Narima da bada it’s za,aba gani kukan da take yasa Abbanta ta fiya da ita
*India Dalhi*
BABBAN Hospital na qasar India dake Dalhi nan suka nufa Shahararan hospital na *Dr Bhai Dharma Nana suka nufa*
Kwararan hospital ne sun Kware Afanni Matsalar zuciya ko A India suna Alfahari da Hospital din da kuma manya’manya kwaririn Dr.’s din su daga cikiko hard a mai hospital din wato Mrs sanje bhai sharma.
Cikin gaggawa Aka Amshi Nurem kwarin likito’ci da suka kware wajan Akin su suka duqufa ceto Ruyawar Nurem
Sun jima suka bincike Akan matsalar shi kafin sufara yi mashi Aiki Sun gano gyanbo ne Acikin zuciyar shi bi Ma,ana ciwo ne da zuciyar shi kuma ya jima a tare da shi tun ciwon na qarami har ya girma zuciyar shi Ce ta huje shine ta Tara jini Acikinta shine dalilin da yasa Iran Yayi tari yake Aman jin yanzu dai zasuyi mashi cikon zuciya.
Haka sukayima su momy da Abba bayani India Alhji Isah ya sa hannu A takardar Aikin .
Sukyi zanzaune suna jirna tsammani domin Aikine mai matuqar hadiri Aikine na tsakani Rayuwa da mutuwa Akin zuciya ba qaramin Abubane domin zuciya itace mutum To Nurem Allah yasa Ayi Wiki Lafiya