HAUSA NOVEL

GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Abuja yau kwana biyu kenan Narim ke fama da mafalkin shi duk ta shiga da muwa domin yana cikin matsala duk da har’yanzu takasa ganin fuskar shi … Aman halin da yake ciki tasan yana cikin hali na mugun ciwo ..

Iya da muwa ta damu bugu da qari Amar nata shira shiran ta fita Malaysia duk Kansu A cikin da muwa suke shi yana damu zai’tai ya barta itama tana da muwa da rashin’shi A kusa da ita gakuama tunani majin yacin da bata San inda yake ba balle taje ta tai maka mashi.

Yanzu Amar saura kwana ukku ya tafi duk wani Abun buqata ya gama shirya komai ranar kawai yake jira.

Ya siyoma Narim yawa ya kuma buda mata WhatsApp wanda zasu ruqa chart in ya tafi ta kuma ji dadinta so sai ko bakomai zata ruqa dai be mata kewa yau da yamma maman Umar ta dawo itada dan ta Umar domin yi’ma Narim godia danta ya dawo tare suka shigo da maman maryam suyi mata godiya .
Kuma Ana cikin haka Yar Miro ta hau sukayi magana da ita ..sannan Yar Miro tace Akira mata Ammyn yanzu yanzu nan maman maryam ta taje ta kira tazo bayan su gai’sa Yar Miro tace dalilin da yasa nace Akiraki shine ke uwace ga Narim dan haka dolle ne Ai’ma Narim girka dolle ne mutane su’san da narim na bada magani sanan Abu nagaba shine inaso ki samu gero ayi gumbar shi asa mata sugar gobe Atara Mutane gidannan Araraba masu ita idan Allah ya kai’mi gobe da safe zamuyi magana daku daku kan Wanda ya halarta nizantafi sai Allah ya kai’mu suyi ban kwana ta sauka

Ammy tace da maman maryam to sai kizaga ko inana makwafta duk kifadama kowa daganan har bayan Layin mu nima zan gayyace duk Wanda ya dace kema mman Umar ki gayyaci naki mutanan Ammy ta fito da kudi daga cikin jakkarta dubu biyu taba maman maryam tace sai gero da sugar aiyi gumba .

Bayan sun tafi sai Ammy tace da Inna to Inna kin dai’ji yanda maryam tace Inna tace naji Allah shi’kai mu Ammy tace Ameen Inna to Inna yanzu dai dolle ki’kira dangin Ku ki sanar da su halin da ake ciki dan suma su samu zowa ai gaban idon su inda tace INA Narim Ammy tace ta fita Inna tai Ajiyar zuciya tace dan Allah bari maganar nan karda Narim taji Kedai Kawai a cigaba ba sai An fadomasu ba dan dan’ gina Baku sa suke ba

Ammy ba tace komai ba dan tun ba’yauba ta ta fuskanci Akwai Abinda Inna ke boyewa game da Narim domin ita kan’ta Narim tasha fad’a mata tun’da tatashi batasan wani dangi nata ba Inna bata kai’ta kuma wani bai’zo wajan’suba ita she’da Ce saboda tun’da suka zo da Narim tana goye basu ta6a zuwa ko ‘ina ba kuma wani nasu bai’ta6a zowa ba Ammy tayi Ajiyar zuciya tace to shikenan Inna bari ni na koma gida sai Allah ya kaimu gobe n Inna ta’”to Nagode Allah shi’kai mana Ran da lafiya Allah ya bar’zumince Ba Abinda zamuce sai’dake sai dai Allah ya biyaki da gidan Aljannar Firdausi Ameen Inna ba’komai Ai An’zama yiwa kai’ne Narim yarta Ce .

Tun’da safiya tayi gidan su Narim yake cike da dan mutum sai kace ana biki sai hayaniya ke ta shi ya’yun’da kowa kefad’in Albarkacin bakin shi Wanda mafi yawancin’su yan gulma sunfi yawa wasu kuma kejin tau’san Karim suna ganin tayi yarinya qarama .

Sai da gida ya gama cika da dan mutum sannan Ammy tasa Aka shin fid’a babbar tabarma tsakar gidan tsakiyar Mutane yanda kowa zai’ga Abinfa ke faruwa Ammy tace da Narim tazo ta zauna tafara Aiki da yake Narim tayi mafalkin Alhaji malam yace da ita shi zai’fa sau’ka dan haka kafin ta zauna sai ‘da yai Alwalah ta shafa turare so sai Ajikin ta sannan ta shimfid’a darduma kan tabarma sannan ta budeAl’Qur’ani sannan ta sake fashe turare ko Inna sai ta dau cabzi tafara kamar yanda’shi malam ya sanar da ita bayan tayi salati ga Annabi Muhammad (S.A.w.) sai tafara fa falaqi da nasii kafin kace me sai tafara gyratsa qeeeeeeeey tana tayi kowa ya’yi shuru an’natsu Ana kallon sarautar Allah zuwa can sai ta fara hammma sai kuma tayi shuru idanun’sun cika da gwalla domin Alhaji malam Akwai qarfi gare’shi shiyasa yafi zomata A mafalki dan in yace ko da yaushe ya Runqa hawa kanta to wahala za’tai .

Bayan su muntina qalilan dan sai da Alhaji malam din Yayi karatun dan laf6an narim din suna motsi Aman bakaji mitake fada to karatune Alhaji malam din ke’yi zuwa can sai ya’yi masu Salama cikin natsuwa da kwanciyar hankali yan’da yake magana kamar kana magana da mutum gaba daya suka Amsa mashi salama inda yace da su bai son hayaniya su Natsu suji mike tafe fa shi .

Wuri ya qarayin tsit yace da farko sai mun shiga jikin wannan yariya ne badan mu cuta mata ba dan mudin ba ma’cuta bane haka Allah ya’qaddara mamu zama jikin’ta dan da tai’makon Allah da tai ‘maku da ita kanta domin muma mu bada tamu gudumuwa A gareku Bil’Adama gumuwar’mukuma itace ta irin ‘baiwar da Allah yai’mana tasani wasu magunguna na cutitika dake damun Al’umma ..da sauran kuma wasu matsaloli na yarn Uwammu masu shiga Jikin Bil’Adama dan cutar dasu saboda Akowacce qabila da Allah ya halitta Akwai mutanan kirki A kwai na banza to haka ma muma A cikin mu Dana kirki da na banza ‘kai tsaye bazamu iya ba da magunguna ba da tai’makon da muke sonyi sai munbi ta hanyarku han’yar kuwa itace ta shiga jikin daya daya daga cikin’ku Wanda Allah ya qaddara’ma hakan kamar dai ita Fatima to wannan shine dalilin Tara Ku Anan dan kusani mai’wata matsala ko shi ko wani Nashi Insha Allahu yana iya zowa domin mubashi tai’makon da zamu iya ba shi Aikin mu ba shirka A cikin shi dan mu ba mashirika bane wannan shi no zantafi sauran bayani yan uwana suyi maku yanzu dan muna da yawa sai Anjiman Ku . bawan da ya iya cewa qala daga cikin mutanan basu gama wannan tunani ba suka sake jin wata murya irin ta yar’bawa ta masu salam sun Amsa sallamar inda gaba daya zaman Narim ya canza sai kada kai take bakin ta ya dan turo laf6anta suka qara tsawo yace” da su mommma da kannene sannuku da fatan kunzo lafiya kuma kuma muna maku barka da zuwa kuna Gane hausana nifa ba Hausa so sai Aman inaji small small .

Yana magana yana kada kai suka ceda shi munaji muna gane yace ayhenn yawa yawa to to to ni dai sunana soja ne soja Ake ke ce man kuma kuma nima musulmi ne kun gani dai wannan yarinya muna tare da itace ne domin murinqa tai maka maku daga maganin kamar yanda Alhaji malam yace daku ai kun gaisa da shi ko sukace da shi ei mun’gai’sa yace to to yawa yauwa to to shi Alhaji malam duk shine babbanmu kuma shi bai’son hayani haka yake ko cikin mu kuma shi Adu,o’i ne yake badawa mukuma muna bada itatuwan maganine Ai yamaku bayani ko ya mana sukace yace”yauwa yauwa to to ya’yi ya’yi wannan shine dalilin ta raku Anan domin kusani ita wannan yarinya tana bada magani Niyam Niyam koko nifa nifa sunana ta yana man wuya suka Narim take OK OK hakane Ammy ya kira sunan tare da juyawa inda take Ammy ta Amsa mashi da na’am soja yace yauwa yauwa daman dan infada maki kayan Aiki nane Wanda yarki zata siye ta Aje mani yauwa zata sai Mani bindiga da Mayan sojoji Yauwa yauwa sai ta Ajemani bari na tafi dan yan uwan suma su gabatar da Kansu Ammy tace to shikenan soja Angode sai Anjima kuma za a sai maka kayan ka yauwa yauwa na gode to to sai anjimanku .

To shi dai soja haka yake maganar shi ba ba haushe bane Aman musulmi ne kuma soja ne A cikin su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button