GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Ta shirya tsaf da ita riga da suket ne tasa mu kyau da tsada ba wata kwalliya tayi bah mai ne ta shafa da hoda sai gazar sai hijab din ta dan garami dai dai kafad’arta .
Tayi kyau sosai duk da kasancewarta yarinya sai baza qamshi take na wani mayan turare
Baba na shirya to ta hada igiyoyen wuri guda ta daure tabarmi ma ta hadasu da igayar ta daure su duka waje guda” inna taso na kai ki d’aki nan rana ta yi yawa kafin mu dawo kuma zata kawo maki”.
*Narim* kenan kina shagwab’ani in banda abinki ko rana ta kawo ai zan iya ko mawa d’aki i naji ni dai tashi na mai daki tunda ina nan
Ta kama hunnu ta su kai d’aki tare da kai mata ruwa ga buta da roba mai fadi lokaci walaha yayi Inna tace “.to *Narim* Allah yai maki albarka yanda kike mana Allah yabaki masuyi maki kema “.ameen Inna ta”.sai mun dawo to ku dawo lafiya Allah ya kiyaye”.
Kayan data daure ta dauka ta aza ga kai ta kama sandar Baba ta dauki kofin maishayi dan kai mashi abinshi,
Suna ta fiya duk inada ta wuce sai kaji ana fad’in ‘yar makahi
Sai ta yi murmushi tace”na,am dan musu ido ko ‘yar masu ido in macce”
wajen mai shayi ta biya ya kwashe kayanshi amman sunan shida abokan shi masu zaman majalisa” rumfa cike take
haka tai sallama ta gaishesu ta bashi kofin shi Ah Ah *Narim* sai ina haka wallahi kasuwa zamu” saida kaba to nima ina siya inji mai shayi to tabarma kake so ko igiya”?
“Duka ma ina so da tabarma da igiya nawa suke?”.” to duka bada naira dubu an ragama”. to shikenan abani to”
Ta kwance daurin ta ba shi shima nan wani yace yana so Abashi ”
Mutum biyu ya siya dubun su biyu ta daure sauran suka tafi wasu kuma sadaka duka basu”
Wasu ‘yan iska daga cikin su kai yarinyar nan ba dai k’yau ba tun yanzu ke nan ina ga ta qara girma” ko yanzu dai bata rasa na latsawa wata rana sai na latsata ”
nan ko rigima ta barke tsakanin su musu san *Narim* na kareta sun fada ”
hummm ita bata san Abinda ke faruwa tafiya take tana cewa Baban ta yai mun fito a sa,a tun kafin mu kai munyi dubu biyu ga kudin sadaka”
hakane *Narim* kin san na Allah bai qarewa indai za kai dogaro da kan ka to Allah zai da famaka” hakane Baba shiyasa na guji kwadan Abin wani yauwa yata haka Akeso Allah yai maki Albarka Ameen Baba”
yace kinga in muka sai da sauran kudin ki riqesu ki sai duk Abinda kike so kai BaBa na gode yau za ai wash sha gare wallai”
Baban ta ya yi dariya yace”minene kuma wash sha gare wallai” *Narim*
dariya ita ta yi tace dadi man za musha dadi BaBa
to dadin shine wash sha gare wallai *Narim* Allah ya kai ki gidan hutu inda zaki shadadi”
Daku zan tafi ai duk wanda zai Aure ni sai na fada mashi daku zan tafi in ya Amine meyi Aure in bai Amince ba ya qara gaba dan ba inda zani na barku”
Ah Ah *Narim* kin taba gani mutum ya yi Aure ya tai da iya yan shi i Baba A fara kai na Baba mubar maganar Auran nan
ba isa yin shi naiba bari na baka labarin Abubuwan kan hanya”to *Narim* ina jinki mike wakan kan hanyar
nan dai wajan yan Aski ne to shagon Askine i shine kai nima inson yin Askinnan to BaBa bari mu dawo Asawo reza nai maka”
to wai da ki bari cinda munzo wajam masu Askin mu biya su yiman”
Ah Ah Baba ni ban son Askin da Aska daya ce kowa ya zo da ita za ai mashi sai mutum ya kwashi cuta shi yaa kaga ban kawo ka nafi so nai maka da kai na ko idi wanzame ban son yana maka
ranar da naga yana maka Aski har kuka nayi saboda wani naga ya yi mawa kan shi cike da guraje kuma da Askar da ya yi mashi ce yai maka tun daga ranar nace ba mai qara yi maka Aski sai nî
*Narim* *Narim* *Narim* na,am BaBa Allah yai maki Albarka ameen BaBa
sun kai igiyar su da tabarmar su wajan yan sari suka bada sarin su Aka basu kudin su sukaje wajan yan naman kai ta siyo kan rago na dubu ukkû da cefane da biredi da talliya da shinkafa ”
sabili omo ba abinda bata sawo ba sau ran dari biu ta sama baban cikin Aljihu
suyo gida da zowar su kayanta ta cire tasa na aiki ta ta zuba ruwa ta wanke kan sosai ya yi haske
säi ta kunna gas ta dora wankakar tukunya ta dora ta zuba ruwa ta yanka Albasa magi gishiri ta zuba”
ta koma ga kayan miya ta rugü tashi kadan citta da ta farnuwa karanfani kadan sai gyadar miya guda biyu
sai daddawä guda daya sai danyan tummatur shima ba mai yawa ba ta gyara su ta daka
na man kanta nata tafasa ta da kau kayan dä ta gyarä ta zuba ta qara ruwa ta rufe ta dauko majinta kalar wanda takeso ta qanqare mintain kadan ta budê ta zuba ta rufe ta ta shi zuwa sallah Azahar
bayan kai ya dahu gidä sai qamshi yake ta däuko wata kula mai kyau ta zuba ta rufe ta dauko wani pilat mai fadi da zurfi ta zuba saurän ta barshi cikin tukunya ta kashe gas din
mahaifanta na cikin d’aki suma sunyí tasu sallah malam ya dawo shine limami masallacin unguwar
gaban su ta kawo wanda ta zuba a filat sai ta fita ta debo ruwa cike da kofin sulba ta kawo ta ajr biredin ta dauko tazo ta zauna gaban
tai bisimilla ta fara basu a baki in sun cinye sai ta basu na man kan haka tai tai masu in tabasu biredi sai ta basu nama inna sai santi take tana cewa dadi nada
*Narim* ba dai iya sanwa ba kî dän rinqa dan gwalo mani miyar sosaî
dariyä *Narim* tayi tace kaji inna nan kikace kar asiyo naman kai gashi nan kinfi kowa sänti
inna i cinda nace kar asiyo kuma an siyo ai qara na more hahahaha kajifa BaBa Abinda take cewa
kyaleta *Narim* da man na son haka za ai sai suka qoshi tace inna kin qoshi BaBa ka qoshi sukace i tace”to Alhmdllh”
bari nima naci nawa sukace da baci kike ba tunda zun mukike ba tace” i ingä kun qoshi shi ne samun na tsuwata Allah sarki suka ce
basu sake cewa komai ba sukai shuru suna tunani ita kuma ta ci gaba da cin romon ta tana säntin Abinta tana cewa Ashe da gaskiyar inna ya yi dadi umum
bayan ta gama ta wanke pilat din ta sha ruwa ta dauki wanda ta zuba a kula tace da su na tafi in kaima amar na shî ina yanzu ya dawo makaranta kuma zan tsaya daukar karatu su duka su kace to sai kin dawo Agaishe da hajiya da Alhaji to za suji tace ta fita zuwa gidan su amar da kûla a hannu
_Comments d’inkû shi zai sä na cigaba ina jiran ruwan comments._
*GAMO DA KATAR*
(yar makahi)
*Na*
*yar mutan jibiya*
AMMYN KHAIRAT
*Dedicated to sarauniya beelat*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*Bismillahir-rahmanir-rahim*
Page4⃣
Gidansu Amar nan ne *Narim* ta nufa gida ne na alfarma wato had’ad’d’en gida duk unguwar *gwarinpa* dake *Abuja* babu gidan da yakai nasu Amar had’uwa *unguwar gwarinpa dake Abuja*
kowa yasan unguwa ce ta talakkawa”
Alhaji Bello shine mahaifin Amar da matar shi hajiya Jidda
masu kudi ne sosai kuma masu tai makon talakawa mutane unguwar na jin dadin zama dasu duk kuwa da suna da kudi baisa su wulaqanta talakawa ba tai makon su suke sa6enin sauran masu kudi”
Da sallama *Narim* ta shiga gidan su Amar”bayan mai gadi ya bude mata get”
hajiya Jidda wadda Amar kecema Ammi tana zaune bisa kujera taji sallamar *Narim* ta amsa mata tare da fad’in”‘yata shigo mana yau idona ya yi ja wajan ganin ina zanga kin 6ullo shuru lafiya”?