HAUSA NOVEL

GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Sai inna Anzarnahu filailatul qadir itama kulum ki tofa Aruwa kina sha kafa bakwai kije kiyi nan da sati daya sai ki dawo muji…

Tayi godiya tace to malam mizani bada na sadaka yace keje ba sai kinbada komai ba iyaka kiyiman Adu’a tace ta gode

Itama dayar tabada tata sadakar yace da ita kema taki matsalace ta Aljani shike’saki sace sace da dauke dauke Aman ke sai kin sake dawo’wa aikinki domin sai kin kawo Mani mono marar’hadi cikin shi zammaki Adu’a kije kina sha zaki kawo ma Fatima farin zakara domin shine ladan aikinki tace to sukayi sallama ya tafi da Narem ta dawo sukayi mata bayani komai tana dubwa gefenta sai taga garin magani qulle da qyallen Atamfa ta buda shi hayaqi ne ta qullama Matar sukayi salma suka tafi…..

 

*India*

Amar jiki ya fara sauqi domin ya fara motsa yatsun qafar shi kuma ya bude idanun’shi yana ganin kowa sai ‘dai bai”ma kowa magana..

Sai dai ya bika da ido.
Tunda ya fara ganin kowa ya fuskanci khaziya na mashi shi’shigi sai shi’shige mashi mata kulum bata ai sai kallon shi dayi mashi yan ta6e ta6e shi har mamaki take bashi ga shegen surutu duk da acikin harshen English take mashi shi dai iya karshi ya bita da ido intaga yana kallon’ta har wani daga mashi gira guda take. Yauma kamar kullum ta shigo bayan an sauya mashi kaya wasu fararen kayane masu guntun wando da Riga itama mai gajeran hannu antado mashi da kan gando ya danyi zama kadan Dan yayi dadin kwanci gashi fatarnan ta shi tayi fresh da ita yayi Kyau ba kadan ba tunda taturo qofa ta shigo ya dago kanshi yaga itace ya dauke kan’shi daga gare ta ta jima tsaye tana kallon shi ba qaramin Kyau yai mata ba yanaji idanuta Akanshi yayi banza da ita Dan haryanzu ba magana yake ba takowa tayi wajan gadon shi ta fallo magunguna ta miqa mashi ya Amsa ta bude robar ruwa ta kafa mashi A Baki har qwarewa yayi wajan shan magani domin ta sama shi ido sai tari yake ga ruwan duk sun wanke mashi jiki sai haqiri take bashi eiyyyya sorry sorry please …

Ta kama hannun shu ta ruqe tare da shafa sumar kanshi qwace hannun shi ya’yi ya gyara kwanciyar shi ya juya mata bata ..

Itako khaziya murmushi tayi Dan ita har ga Allah sonshi take ba kadan ba musammn yanzu da ya tashi ta qara ganin kyanshi …

Cigaba tayi da aikin ta ..

Yanzu Alhaji isah shi ya koma Lagos wajan harakokin shi domin dai yanzu jikin Nurem da sauqi Momy hankalinta ya kwanta kulum sai godiya ga Allah take tare kuma da kai’kukanta Ga Allah ya kawo masu Narem aduk inda take Allah yasadasu da ita domin dai itace cutar dansu..

Da yamma Narima ta shigo tayi ci kwaliya domin zamanta da khaziya har gidan su take binta sanye take da sari yayi matuqar Yi mata kyai domin ta koyi SA sari a wajan khaziya tayi Kyau so sai Abin ta yanda ba India Dan dai ita Narima baqace Aman ba wuliq ba ..

Nurem ya dago suyi ido hudu da ita ya qyafitota da hannu ta qarasa wajan shi ta kamashi ya tashi ..

Yace my sis wannan irin gayu kinyi Kyau so sai yeyyyyyyyye Narim tace tayi tsalle ta fada jikin shi tana murna Yaya Nurem yau kai ne kayi magana kai Allah na gode maka Alhamdulilla Allah na gode maka….

Shima dariya yayi gani far in cikin qanwar’shi shima yayi farin ciki so sai domin yana son qanwar’shi so sai yanda take kulawa da shi sumar tsaye khaziya tayi ba qaramin Kyau Nurem yayi ba da yayi dariya dumful din shi ya lotsa ga haqoran shi farate tass dasu da siririyar woshiryar shi ..

My Nurem jiki yayi sauqi ko ya daga mata kai yace ina Momy ta Narima ta Fita shikuma ya lumshe idanun shi gani khaziya ta nufo shi Momy ta shigo jikin ta har rawa yake tana fading Alhmdll sauqi ya samu ta rungume shi ..

Tana mashi sannu da ya jiki sai murna suna ta fira cikin yaren Hausa khaziya tayi kasaqe tana jinsu domin ita dai bajin Hausa take ba sai Hausa tasu ta birgeta taji tana sha’awar koyan Hausa …

Inda Nurem yace ma Momy shifa ya gaji da hospital dinan Asalme shi cinda yajik sauqi kuma jinkinshi ya bashi ya kusan haduwa da Narem kwananna Dan haka shide A Salme shi Momy tace to insha Allhu Aman ka qara haquru jikinka ya qara murmurewa ..

Nima ba kai’ba ni kai’na inaji ajikina yarta ta kusan dawo’wa inajin hakan Allah dai ya sadamu da Alkairi Sukace Ameen…….

 

 

Ammyn khairat

 

*GAMO DA KATAR*
Yar makahi

*NA*

Yar mutan jibiya
*Ammyn khairat*

*LABARI MAI TA6A ZUCIYA*

Daga Alqalamin golden girl
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*wannan PAGE sadaukarwane ga yan group gamo da katar inajin dadin sharhinku*
@musamman ma
Aminiyata Maryam

*mmn Ilham
Ummul khairi
Nusaiba iliyasu
Mmn mardiya
Feenar
*Mmn Nusaiba*
*Dakukan masoyana na group gamo da katar golden girl na godiya da comments* *dinku mai* *matuqar sata nushadi*

*PAGE2️⃣4️⃣*

__________????bayan kwana biyu jikin Nurem yayi sauqi Aman dai har yanzu yana Aman jini domin shine matsalar’shi Abin ciken Sanje babban likitan ya sanar dasu zuciyar shi ta warke bawata matsala Aman abinda yasa shi shiga damuwa shine aman jinni da yake Wanda har yanzu basu gano musabbabin shi.

Yayin da shikuma yaji garas ya matsa da a sallame shi haka ko akayi yau an rubuta masu ta kardar sallama

Sun shiga garin na India domin shaqatawa ya siyi sari kala kala masu shegen Kyau da tsada ga zobuna diamond da na zinari ya siya guda biyu masu Harafin N&N

Momy sai kallon shi take wani lokaci sai tai ta ganin Dan nata kamar zautacce .

Haka Narima tai’ta tayashi suka judo kaya kamar mai’shirin hada lefe.

Duk Abinda ya siya sai domin Narem sai yaji farin ciki ya kama shi dudine suka kasa bakadan ba sudawo A gajiye Allah sarki khaziya duk ta shiga damuwa so sai Dan tunda take aikin jinya bata ta ta6a jinya marar lafiyan da ya shiga ranta ba irin Nurem tana jin shi cikin jini da 6argo..

Itama ta hada ma Narima tsaraba sari kala kala da qananu kaya sarqa goal da A warwaro zobuna da yankune masu kyau na fashation

Narima sai zuba mata godiya take inda sukayi exchange din number
Dan suriqa gai’sawa momy sai da khaziya tai mata Alkairi duk ta damu domin hotal zasu su kwana da safe subi jirgi .

Inda Nurem yake ta nufa duk ta da birce tarasa miza tace mashi gani haka Nurem yai mata murmushi yace cikin harshen su na India domin yanaji yaran ido yace da ita khaziyyyyyyya sai da yaja sunanta itako harda rufe ido jin take Nurem yafi kowa iya fadin sunnan ta

Yaci gaba da yimata magana da indiyanci Wanda ita A tunanita ko baijin India Ashe yanaji Dan yanda yake yaren nasu Kai. Ka dauka shima ba India ne

Godiya yai mata Abisa kulawa da taba shi inda yace da ita zasu tafi Allah yaqara qaddara saduwar su da Alkairi kuma shi zai runqa dawo wa lokaci zuwa lokaci domin gani likita ..
Hawaye suka zubo mata ..

Ta kawo wani Dan qaramin Abu nade da wata Leda mai’walkiya ta bashi ya Amsa yai mata godiya..

Da motar ta ta kai su har hotal din da zasu kwana Dan taso suje gidan ta su kwana Nurem yaqi suna zaune a hotal sai kallon shi take indashi kuma yaqi kulata sai satar daukar shi photo take ya dago suka hada ido domin yaji qara daukar shi photo da tayi kuma ita da Narima yanaji tana fadamata tanasan yayan ta inda Narima tace to ta fadama shi khaziya tace tsoron shi take bai’dariya kulum cikin tsare gida yake harda kukan ta ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button