HAUSA NOVEL

GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

*Narim* ta shigo “wallahi lafiya lau hajiya”.” Ah ah yanzufa mun 6ata ban hanaki ce man hajiya ba bakiji yanda Amar kece man ba kefa “yata ce *Narim* kamar yanda Amar yake dana ko baki dauke ni uwa ba”?

“Ba haka bane Ammi kiyi haquri mantawa nayi”.” yauwa ko kefa”

“Da safe banganki amsar koko ba mesa”?
“Ammi yau Inna ta matsa sai da mukaje bara kuma sai da malam yace” mubar zuwa bara mu bari muruqa saida kaba ta ishemu amman ta matsa muka tai ko naira ba musamu ba sai sanyi da mukasha nai tai mata kuka”

“Kukan me?”. Inji Ammi “tap ai kuka na fashe mata da shi uwar hanji na ta gulle tai ta kuka quuuuu qulululu ”

“Ko ta fiya na kasayi shi yasa nai tai mata kuka da ban mata haka ba to da yanzu ba mudawo ba “.”kai *Narim* ta inna”
“Ai ba maishiga tsakanin ki da Inna to yanzu menene aka kawo man cikin kula”
Ai yau romo muka sha”

Ina Amar yake shi na kawo mawa to lallai Amar kade Eh harda ke to bani qamshi ya cika man hanci nasan kuma diya ta a kwai iya girki”

Ammi ta buda naman kai qamshi ya baje falon ta iba ta kai baki sai da ta rufe ido
Itako *Narim* daya daga cikin kujerun ta samu ta zauna tare da daukar apple tana ci tana matuqar son apple”

Ammi tace” *Narim* wannan nama ya yi dad’i haka nake so ki dage kiko yi girki kinji ko ai Ammi duk Abinda kika koya man sai na yishi ai nagani har ma kinso kifini iya “.
” *Narim* Ammi yaza ai nafiki iyawa ke dai kina santi ne kifa ra gema Amar wai yana ina”.” ai dole na raga mashi nina isa na cinye shi bai dade da dawowa ba wanka yake to kingan shi gashinan ya fito

Ammi na wanne shagali ne ake qamshi ya cika man hanci to nama ne qanwarka ta kawo maka kai na gode kusa da *Narim* ya zauna

yana fadin yau ban ganki ba da yanzu nake son naje naji lafiya lafiya lau ya makaranta lafiya lau to masha Allah

shima yaci naman yana santi da ya gama yace kai wanna romo ban ta6a cen mai dadi irin shi ba itako sai murna take Amar ya yaba da romon ta” yace to yanzu ta shi mutai wajan karatu kafin la asar tayi malam yazo

to mutai wai tsaya ma inaso dama na tambaye ki jiya da naji kina turanci keda wannan waya koya maki
to kaji Amar humm bance karki qaraceman Amar to yaya hummm ni dai ba shi ba to my yauwa yanzu dai waya koya maki to ba kai ne ka koya man ba ah ah gaskiya bani bane ai nafima ban iyaba kin kusan muti shabiyar kuna turanci ni kuma ban iya turancin munti shabiyar kuma ni wanda nake koyamaki daga were are goine sai from were ke nanu dai ne nake koya maki ”

“humm ni dai bawani kai ka koya man ni wallahi ban koya maki bah duk abinda suke Ammi na jinsu sai tace” Amar na gaya maka lamarin *Narim* ka dai na yawan bin cike”

“wallahi Ammi abin na ban mamaki hakafa suke fama da ustaz in yazo koya mata karatu sai ya gama ya yi tambaya wanda bai gane ba ya yi tambaya sai kiji tace ni dai ya ustaz dan gyara ne sai yace to inne zan gyara maki sai tace ah ah kaii zam mawa inda kace kaza ba kaza yake ba sake dubawa ka gani kuma da ya duba sai yace” na,am sayyada *Narim* haka yake”

“to Ammi a kwai abubuwa maka manta wadannan dake daure man kai sai Ammi tace” to kabar su a dauran nade gaya maka yawan bincike akan lamarin *Narim* ka daina ba naka bane ta shikutai

sai *Narim* tace” wallahi Ammi shike koya man Ammi tace na sani qyale shi yata haka suka ta shi suka tafi wani dan lambu suka nufa dake cikin gidan gefe guda ga somun full nan cike da ruwa tsuntsaye farare sai shawagi suke sun kuka mai dadin saurare”

bisa wasu fararan kujeru suka zauna ya fito da books din shi ya fara koya mata hausa suka fara sai lissafi sai suka dawo turanci kuma duk Abinda ya koya mata ta ruqeshi kenan wani lokaci kuma ita ke mashi gyara musamman wajan lissafi ko turanci”

wani lokaci har tsoro take bashi duba da *Narim* bata ta6a zaman ajiba shine daman ke koya mata inya dawo abinda aka koya ashi sai ya koya mata”

aman da yazo koya mata mistake guda zai yi sai tace mashi ba haka bane kaza yake dole ne ta daure mashi kai bai mantawa wata rana Ammi ta aikesu shapping mall

to masu shagon basu jin hausa kafin ya ankara yaji tanata speech bayan sun fito ya tambaye ta ina ta koya tace” wajan shi kari biyu kenan yana ganin tanayi kuma tace” shi ya koya mata

hummm Amar kenan abinda baka sani ba *Narim* kusan yare goma takeji

bayan su kammala karatun su tace mashi zata gida la,asar ta gaba to in tai sallah sai ta dawo sannan ustaz yazo yace” mata to suka taso zuwa cikin gida tai ma Ammi sallama ta tafi gida

zaure ta yi ki ci6es da malam za shi masallaci dan haka sai ta kamashi ta kai shi sannan ta dawo gida inna ce ta fito daga ban d’aki da sanna tana daddogarawa”

*Narim* inna ta alwarlla zaki Eh *Narim* kin dawo na dawo inna nima sallah zanyi na koma to hakan ya yi ”

ta kama inna ta zaunar da ita kan kujera ta yi alwarllah itama ta shiga ta kama ruwa ta fito bayan sun gama takama sandarta zuwa d’aki dan yin sallah abinsa sallah ta shin fida masu suka tada sallah bayan sun gama

*Narim* tace inna niko in tambayeki inajinki *Narim* yauwa inna Allah yasa yau kin bani amsa tambaya ta wai inna kinji abinda na keji”?

mekikeji *Narim* baki ji anayi man magana cikin d’akin nan wani lokaci zakiji ana fadar sunana ko kiji ana cema sannu *Narim* ko kiji ana maganar dani banji mi sukecewa” inna duk kinaji wannan koko ni kade keji”?

” *Narim* kullum ina gaya maki ki daina sa komi garanki ni banjin komai kunnuwanki ne ke jimaki hakan aman bawani abu”. “Hummmm Inna kenan nifa ba wani kunnuwana ke jiman ba yanzu inna ko motsi ba kiji?”.” Eh banji *Narim* ki bar maganar nan”.” to shikenan Inna naji bakijin komai aman ai kinajin d’akinnan na qamshi ko shima bakiji ba?”.Inaji *Narim* hummmm Inna kenan in haka ne to shi qamshi wake sa shi ni dai ba turare nake siya ba sannan kuma shi wannan Alhaji malam din wanene”?
sai inna tace wanne kuma Alhaji malam?”.” wanda nake fadamaki”.

Inna tace” *Narim* ni ban san komai ba kamar yanda baki sani ba ki tattara komai ki aje gefe kita adu,a inda sabo yace ace kin saba dan ba yau kika saba gani ko jin abubuwa irin wannan ba tun kafin shekarunki su kai haka to ki barma Allah komai a matsayi na na mahaifiyarki zan tayaki da adu,a kinga dai mu makafi ne ba ido gare muba karkije wajan binciken ki nasani abinda baki sani bah kijawo mana wani abun ,kibar ma Allah komai shine masanin komai koma minene Allah zai bayya na maki shi”.” to shikenan Inna aman kinga *Narim* ta shi kije kar Amar suyi jaranki Allah yai maki albarka” ameen inna” bari naje nasan yanzu ustaz malam yazo yauwa to ki gaishe shi” to zai ji sai na dawo” to tafita

Inna ta yi ajiyar zuciya ita kanta lamarin *Narim* na d’aure mata kai sannan kuma duk abinda ta fada tanajin wani”

ta dai tana adu,a Allah ya bayya na masu komai kuma mafi alkhairi.

Koda ta isa gidan su Amar ustaz malam yazo ita kawai akejira dan haka inda suke d’aukar karatu ta nufa da sallama ta shiga suka amsa mata bayan ta gaishe da ustaz

sai ya gyara zama tare da fad’in su karanto inda ya gaya masu jiya suka karanto mashi yace na,am jazakumullahi kairan

sai yai masu qari daga inda suka tsaya saida ya tabbatar sunbiya sannan yasa suka qara karanto wa daga bisani yace” mai tambaya ya yi tambaya
sukace babu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button