GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

ustaz yace “yau sayyada *Narim* ba tambaya tace Eh sai yace Alhmdll sai suka koma kan sauran littafe bayan ya magama to nan *Narim*
tai tambaya ko nace gyara dan kamar kullum ce mashi ta yi” ya ustaz inada tambaya “.Sai yace” na,am ina jinki aman ki gyara harshenki akullum ina ce maki ba ustaz ba ne sayyadi ne “.Yana magana yana shafa gemonshi to
“ya sayyadi daman dan nace ka duba ka gyara waje kaza inga kaza yake”. Ustaz yace” to”. Ya kuma duba yaga gaskiya ta fad’a
bayan ya gyara ce mata nima” ya sayyada *Narim* in ba damuwa zan maki wata ‘yar tambaya kad’an”.
Tace” malam ina jinka mi nene?”. tambaya sai ustaz yace “wato ainahi tambayar da zammaki bayan ni wake koyar dake karatun qur’ani,ani da sauran littafai”. Sai *Narim* tace” wato ainahin ya sayyadi bayan kai a kwai wani babban malami da ke koya man sunan shi alhaji malam”.
“wa nene shi wannan Alhaji malam d’in kuma wace makaranta ce wace unguwa yake?”. Sai tace” mashi makarantar Allo ce sai dai ban san sunan unguwar ba”.” To kuma kike zuwa?”.”Eh shi ke zowa ya tai dani”.” Shiwa?”. Shi malam d’in”.”To da wane lokaci ne yake zowa ya tai dake dan nima inson na hadu da shi dan na qara daukar darasi wajan shi”.
“aiko dai ya sayyadi da ko ya koya maka dan makarantar cike take da masu daukar karatu dan nima acan har koya mawasu nake”.
Amar yace” ke *Narim* har kina koya ma wasu karatu baki ta6a gayaman ba kuma ni ban san ma kina zuwanta ba”.
“wacce makaranta ce ta Alhaji malam da har kika shiga baki gayaman ba?”. “Nifa yaya Amar ba fa shiga nayi ba shi ke zowa yana tafiya dani”.
“to naji da yaushe yake zowa in yazo mu tai tare?”. Sai tace masu “da daddare yake zowa tafiya dani kuma da fararan kaya ake zuwa k’arfe biyu na dare sai ku shirya tunda kuna zuwa!”. “K’arfe biyu na dare”. Suka fad’a tare da zare ido.
“karfe biyu na dare *Narim* ina zai ganki ?”.”Aiko shike zowa ya tadani kuma shi zai ta daku in zakuje”. Sai ya sayyadi yace” wato ainahin ni ba zanje ba ki gaida shi”. “in yazo malam ko kuwa”. Nace
ya sayyadi ya d’auki qur,aninshi da sauran littafenshi yai masu sai anjima ya qara gaba yana ambaton wa innahu mi sulaimanu dan yazu magana ta gaskiya *Narim*
al’amarinta harda jinnu a ciki shiya wasu abubuwa nata kebashi mamaki……..
*kai na gaji gaskiya inga ruwan comments inba haka ba na barshi dama biyu na hada bayan shi ina wani*
taku ce golden girl????
*GAMO DA KATAR*
Yar makahi
*Na*
Yar mutan jibiya
*Ammyn khairat*
`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*page 7*
Bayan Narim tagama komai na aikin gida sai tayi sallama da inna ta gaya matacewa zataje ta kai ma Amar magani inna tace sai kin dawo ah ina kika samu maganin sai Narim tacewa inna Abbah ne ya banishi jiya da daddare cikin daji mukatai harma na d’ebo wasu gasu can na shanya inna ta nisa tai shuru batace komai ba sai zuwacan tace Abbah kuma waye Abbah Narim?”
Sai tace mata shima tare suke da Alhaji malam sai inna tace to jeki Allah ya bashi lafiya Narim tace”Amme” inna sai na dawo.
Inna tace”to” inna cikin ranta tace Narim kenan mai jinnu da yawa.
Da sauri ta nufi gidan su tana shiga ana rabon koko dan haka kechine ta nufa ta dauko cop taje aka zuba mata koko sannan ta nufo parlour da sallama
Ammi ta fito daga d’akin da Amar ke kwance tace”Narim kece tace nice Ammi ina kwana ya mai jiki Ammi tace” lafiya lau mai jiki da sauqi zamuce Narim .
Sai Narim tace “Allah ya bashi lafiya da man maganine na kawo mashi na hausa Da koko akesha ko hura ko nono zai sha kamar sau ukku a rana sai a jiqa kad’an da ruwa Ashafe mashi jikin shi Ayi kwana ukku Ana mashi insha Allahu zai samu sauqi
Ammin tace” to Narim da man ba a gwada mashi na hausa ba nima nayi tunani haka Allah ya shige mana gaba ina kika samu magani sai tace wallahi Ammi nima jiya Abbah ya bani shi kuma ya shaida man cewa ciwon Amar ba na asibiti bane duk inda za.a dashi kashin kudine sai yace inkai mashi wannan da yardar Allah zai samu sauqi sai Ammin tace” to Allah yaba shi lafiya shiga yana ciki sai kibashi ganinan zuwa sai tace to” tayi gaba zuwa cikin d’akin ya yin da Ammi ta bita da kallo.
Ita lamura Narim bata cewa komai tun tana yarinya ta fahimce Narim na tattare da Abin Al.ajabi wato tana tare da mutanan boye dan bata mantawa wata rana tana qarama da ta sa aka amso mata ita dan saboda ta shiga ranta bayan an amso mata ita sai ta Ajeta ta shiga kichine za can sai taji diya tayi garau da kuka
Sai tafito da gudu koda da fito Abinda ta gani ya tsora tata wato wani qaton macijine ya laulaye ta ita kuma ta zata Abin wasane da tazo zata kamo kanci sai ya noqe ya juya mata bindi shine take kuka dan ta kasa kama Kanshi dan tayi wasa Ammi ta tsoro ta ba kad’an ba cewa take Na shiga ukku ku tai makaman d’iyar mutane maciji zai sare ta ba mai jinta saboda ita kadece cikin gida kuma duk ihun da take ba Aji kuma tsoro ya hanta ta fita sai kuka take wiwiwi
Tare da Ambaton duk adu ar datazo bakinta shiko macijin ko ajikin shi wasani shi kawai yake da Narim itama da tabar kuka takoma dariya tana wasa da bindinshi.
Ammin sai tayi tunani Ada anama maciji magana kuma yaji dan kakarta ta ta6a bata labarin wani maciji lokacin Akwai wani k’aton tabbaki qauyan su wada ake d’ibar ruwa cikin shi domin amfani.
Sai take cema wata rana tun da safe taje d’ibar ruwa sai ta isko wani qaton maciji ya yi gammo waje guda ya kwanta ya tare ta ida zakabi kad’ibi ruwa ta ce koda naga naji tsoro Amman ba sosai ba sai na daure nayo wajanshi sai nace mashi kai sarki tunda safe haka kazo tatare hanya halan yau baza Abarmu d’ibar ruwana inko akai haka ba a tai maka mana ba dan in banan ba ba inda zamusamu ruwa yanzu manan da kaga nayo wannan saukon ba muda ruwa ko anini gashi ammana haihuwa tunda safe ko d’iyar ba.a wanke ba saboda ba ruwa inka hana d’bar ruwan ina zamu samu wasu Atai makamani sai ya dago kai ya kalleta sai kuma ya koma ya maida kanshi qasa kamar yanda yake sai taqara cewa dan Allah ka tai makamana kodan tsufana shuru tagaji da tsayuwa bai bata hanya ba sai tace to shikenan cinda na hada ka da Allah kaqi to bari na tafi anjima na dawo sai taga ya sake dagowa ya kalleta duk ta yi kalar tausayi sai taga ya saisad’a ya tafi nesa da ita yabata hanya taje ta d’ebo runwa ta dawo har inda shike kwance tace” mashi to saraki na gode kallonta ya yi ya maida kanshi ya kwanta ita kuma ta tafi tana tafiya tana waiwayanshi sai taga yatashi daga inda yake yakoma ai nahin inda ta isko shi wannan ya nuna cewa macizai naji magana koda Ammi ta dawo tunani da take sai itama tai qarfin hali da tarin adu.oi. cike da bakinta ta dan qara matsawa kad’an sai tace bawan Allah karka cutar da yar mutane nima ba yata bace yar Amana ce na amso ka taimakaman na mai da yar mutane gidan su lafiya kaga ita yarinya ce bata san komaiba kaji saraki nida kebabba ai kaga na tsorata dan Allah ta hade hannuwanta waje guda Alamar ban haquri ga mamakin ta sai taga du laulayewar da yayi jikin Narim yana warwarewa sai yai gamo waje guda ya maido kan shi inda Ammi take ya kalleta ido cikin ido itama Ammi ta kalle shi daga nan bata sake sani mike faruwaba sai bayan mitina kusan 30 sannan ta tashi Ashe summa tayi sai nanufi Narim sai barcinta take kan kujera gawani mayen qamshin turare da take wanda shi kanshi d’akin qamshin yake nan ne Ammi ta gane cewa ba maciji bane jinnu ne duba da suma da ta yi ga kuma qamshin da Narim ke yi kuma har yau Ammi bata gayamakowa Abinda ya faruba ko tazo zata fad’a sai bakinta yai mata nauyi.