GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

likinta tace Allahu Akbar ta rassu ne tace ta rassu kulu nabsin za ikatul maut ku gyaraman idan ba dai dai na fada ba
dukan mai rai mamacine muma tamu muke jira tace ina yan uwanta tace gani nice yar uwarta tace man ai naga ita ita kade ta kawo kanta ke kuma mujinki ne ya kawoki tace eh hakane aman ko A musulinci ai musulmi dan uwan musulmi ne ta gaya man bata da kowa ba yar nan qasar bace Abinda ya kamata kikira Asutur tata akaota gidanta na gaskiya
batce komai ba likitan ta fita sai gata da manyan ta maza da mata sun shigo waya suka sa sunata daukarta photo sai da suka gama daukarta sannan sukace baiwar Allah yanzu kinci ba yar nan bace to duk da haka bazamuyi gaggawar kauda taba dolle mutura photo nan ta A social media ko zamu samu informtion akanta tace to bawani Abu yanzu dai Allah yasa Adace Ameen sukace ita fa momy duk Abinda ake jinsu kawai take domin bata cikin hayacinda
Notocin kanta duk sun kwance Abu na farko da yafi daga mata hankali shine mutuwar matanan ba a ta6a mutuwa gabanta ba sai yau dolle Abin yata da mata hankali ya kuma tsaya mata arai sanan kuma Abu na biyu shine Amanar da ta barmata duk da tasan ta bangaranta ba matsala zata iya riqemata fatima Narim kamar yar da ta haifa aman abinji shine bahagon mijinta wanda take tunani da kamar wuya yabari ta ruqeta to koma dai mi zai faru zata ruqeta Amana kamar yanda tai Alkawari ko bakomai ai da na kowa ne tana cikin wanan tunani Nuraim ya kawo mata Narima ta dake kuka ita kuma Narim ta rugada ta yi barci ta gaji da kuka ya koma ya dau komata Narim din duka Amshesu ta rungumai tausayi Narim ya kamata nono taba Narima takama tana ta sha tana cikin shan nono Narim itama ta ta Shi
har zata bata nono kuma sai tafasa sakamon kon wani tunani da tayi Nuraim na tsaye yana kallon ta yasa hannun shi guda cikin Aljihun wandan shi sai kace wani babba sai yace” momy ita bazaki bata nono ba sai momy ta share hawany fuskarta tace ah ah Nuraim
sai dai mu shayar da ita madara yace ah ha momy kibata nono kamar yanda kikaba Narima kinga itama yarki ce kamar Narima kuma Aman kika amsa tace” gakane Nuraim ba zaka gane bane amn dai madara zamu bata dan shine gatan da zammaka yace to shikenan momy saboda baya muso da momyn shi yasamu tarbiya daga wajanta
aman shi cikin ran shi gani yake kamar an cuceta
muntuna kade likitoci suka sake da wowa wajan gawa suka ma momy zuje su shirya akaita gidanta na gaskiya domin kaf sociel media ba wani labrin wanda ya santa sai Adu,,a da fatan Alkairi da ake mata
momy ta fashe da wani irin kuka kamar ranta zai fita tace ” Allah ya jikanki yaruwa Allah yai maki rahama ai kin futa kiyin shada
Ameen suka Amsa mata shi kan shi Nuraim sai da ya fasa kuka duk da dau rewar da yake da shi aka kama gawar zuwa waje da shi akayi komai har kaita dashi Akayi momy sai hawaye domin sunqi tsawa tasa yaranta gaba tana kallo kuma tana tausayin yar marainiyar Allah
Wata likta ce ta shigo tace ” baiwar Allah ki daina kuka domin itako ta yi shahada Adu,,a zaki mata bayan hakan yawan kukan zai iya jawo maki matsala gaki da dan yan jego haquri zaki
Bayan An kaudo ta sai suka dawo kan butun yarta ya za ai da ita ko gidan marayu za su kai ta inda wasu daga cikin likitocin suka ce su suna son ta Abasu
Sai momy tace ha ha wannan diya tawa ce Amana tace nitaba Amanar ta suka basu yarda ba qarya take nan rugima ta kaure su sai sun Amshi diya momy ta hana Nuraim sai kuka yake yana fadin matarshi ce shi momy taba
Likitan da momy fatima Narim ta aika kiran momy Nuraim tace zai iya yuyuwa ita taba Amanar bbyn ta saboda da ta haihu ni ta aika kiranta Aman cinda baku yardda ba ai akwai cemara sai Aduba Agani Kowa yayi na am da hakan dan haka ta computer akaje ka duba duk Abinda ya faru sukayo zooming din shi sukaji kuma suka gani dan haka suka barma momy bbyn da fatanAllah ya tayata riqo tace Ameen duk da hakan sai da akasa hukuma Acikin lamarin saboda tsaro”
A qa’idar Asubitin ba’a zuwa wani naka bai zuwa tsareka sai dai in an kawoka wanda ya kawoka zai koma sai in buqatar wani Abu ya taso Akira wani naka inkuma 6an garan haihuwane sai ha haihu afada masu sanan kuma ba maizowa sai lokacin da suka diba ya yi kamar in ka haihu to sai kayi hutun awa data kai goma dan haka duk wanan Abu da ake dangin momy da kuma mijinta basu sani ba bayan komai ya lafa momy ta koma d’akin hutu sabe da yarta Narima shikuma Nuraim sabe da Narim
Suna zaune ba mai cewa komai Nuraim kade kema Narim wasa inda ta sarqa dan ya tsanta cikin na Nuraim suka qule shikuma yana dariya
Bayan mintina kaden sai ga Alahji isha mahaifin Nuraim yazo daukar su domin lakacin ya cika da murana ya Amshi yaran yana dubawa shi Atunanishi ko yar biyu aka haifa cikin murna yace kai Nuraim baka ceman yan biyu aka haifa ?”
Nuraim ya yi dariya yace” ddy wacce tafi kyau sai ddy ya duba wanna ya duba wanan sai ya nuna fatima Narim yace tafi kyau kuma itace ta wajena na za6i tawa Nuraim ya yi darita yace” yauwa ddy muna tare kenan Aman ba yan biyu bane yan guda guda ne ita momyn ta ta rassu yan zunnan mu tabarma ita ban gane ba mikake fada
Ya dube momy ke mi daniki ke fada i man qarin bayani tace Alhj duk mubar maganar nan sai munje gida ko zaifi yanzu nake son jin komai ya aje Narim
Likitane yai mashi bayani komai inda shikuma Alhj yace bai san zan can ba taya zai riqe yar da bai son Asalinta ba kawai daga gani mata ta haihu ta bar diya sai tace ta baki amana wasan ko batada uba shegiyace ya rufe ido yaita wulaqanici yace ba inda za a da ita ba agidan shi ban momy tarufe ido daman tasan Anruna wai ansaci zanan mahaukaciya
Aman komai zai faru sai tatai da Narim sai haquri ake bashi aman kamar anaqaramashi har saida sukayi fada da wani likita
Haka yafita daga cikin d’akin yace ki taso mutai aman kisan inda zaki kai ta dan ban ruqon dankowa
Momy taba likitocin haquri kuma tace masu ba abinda zai faru sai Alkairi sucekacemata indai yaqi riqe ta to ta kawo masu ita dan su suna so momy tai murmshi tace to shikenan
Haka suka shiga mota ba mai cewa komai
Sun isa gida lafiya wani shahararan gidane na gani na fad
bada labarin gidan6ata lokacine dan harda bene daga waje sanan ga jami an tsoro yan sanda guda biyue da mai gadi
masha Allah nace da naga cikin gidan Aljanar duniya komai yaji na more rayuwa
Dangin momy sun zo cike da gidan ganin momy da yara biyu gidan yaqara kaurewa da hayaniya Ashe yara biyu ta haifa daga ita har Nuraim ba wanda yace komai shida man Alhjn koda ya ajesu bai shiga cikin gidan ba gaba yayi saboda ciki. Haushi yake
Sai da momy tai wanka ta shirya ta dan sha tea sannan ta dan samu natsuwa duk da ka ganta kasan tana cikin damuwa sukan su yan uwanta sun lura da hakan
sai sannu suke mata Narim na kuka suka meqo mata ita sukace ta bata tasha yunwa take ji sai tsutsar hannu take momy ta karkada masu kai tace ah ah ahado madara ba ata basuce komai ba dan atunanin su ko ruwan nono ne bai zo ba aka hada madara aka bata sai sha take cikin fida da anjanye fida sai ta fasa kuka
sai da ta sha ta qoshi tai qyatsa sanan sai barci ya dauketa Nuraim yazo ya Amshe ta sai da Narima ta tashi momy ta fito da nono ta bata sukai mata cha da ido suka ya haka kin hana wannan kin ba wanna lafita momy hawaye suka zubo mata tace ita dolle ce tasa za’a bata madara momyn ta ta rassu nan ta basu labarin komai sun tau sayawa Narim kuma summa momy fatan Alkari na Allah ya kai haske qabarinta san itama momy su kai mata fatan Allah ya tayata ruqo