SULTAN HAUSA NOVEL COMPLETE

SULTAAN 8

 ???? *S U L T A A N*Mss Flower????

*FITATTU HUƊU????*

_RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE_

*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

           *08*

*ZEENA POV*

Bayan kammala aikin abinci ta samu ta ci, sannan ta samu waje ta kwanta, tana nan kwance matar ta shigo da fara’a a fuskarta ta ce “sannu kyakyawa, sannu kin sha aiki” 

Ta ɗan yi murmushi tare da cewa “ba komai” 

Hannu matar ta saka ta ɗebo coins a aljihu ta ce “don ke na samu alkhairi sosai, ina kika yi ne?” 

Ta saka hannu ta amsa tare da godiya sannan ta ce “ban san inda zan nufa ba, ba ni da kowa, ba ni da wajen da zan je” 

Matar cikin jindaɗi ta ce “ki yi zamanki a nan, kike tayani aiki, sai nake biyanki tare da ba ki abinci”

Hawaye suka ɗigo mata ta share sannan ta ce “ba zamana ne damuwa ba, sai dai babu alkhairi a zamana a nan don idan da kin san abubuwan da ke dabaibaye da ni da kin koreni tun wuri musamman da maza ke kawo min hari” ta ƙare hawaye na ɗiga a idonta 

“Ki bani labarinki, da alama akwai abubuwa ƙudundune cikin rayuwarki” matar ta faɗa 

“Tabbas, sai dai babu na alkhairi, zama da ke kuma a nan ba zai taɓa zama alkhairi gareni ba, don haka kar ki matsa ki ji sirrin rayuwata, tamkar fami ne na mikin da yake zuciyata” ta ƙare tana rushewa da wani irin matsanancin kuka. 

“Zan taimaka miki kin ba ni tausayi, da me kike gani zan iya taimakonki?” Matar ta ce

Da sauri Zeena ta kama hannunta hawaye na fita a idonta ta ce “ki taimakeni da wajen da zan ƙare rayuwata ba tare da farmakin ɗa namiji ba, ko wani irin aiki ne zan iya muddin zan samu abincin kai wa bakina sannan na tsira daga wani namiji” 

“Da kyawunki za ki kashe rayuwarki a aiki?” 

“Shi ne zaman lafiyata, zaman lafiyar duk wanda ya raɓeni, wani kyawun ba ya zamowa alkhairi, kamar dai nawa” 

Matar ta nisa ta ce “zan turaki wajen aminiyata da ke aiki a *WHITE PALACE* tun da cikin masarauta ne ina ga za ki tsira daga abin da kike gudu” 

Wasu hawaye suka saukar mata sannan ta ce “Na gode miki, na gode miki, yadda kika faranta min zan miki roƙon farin ciki har tsawon rayuwata” 

“Babu komai” matar ta ce tare da miƙewa ranta babu daɗi sosai, ta so Zeena ta tsaya. 

*AFUWAN ZAN DAWO SALON DA NA FI AMFANI DA SHI, ZANCE DAGA BAKIN TAURARO, KU MIN UZURI, YANZU KUMA ZANCEN ZAI KOMA BAKIN ZEENA NE*

*SULTAAN POV* 

Gabaɗaya jama’ar jirgin sai iyo suke cikin ruwan, tun suna yi da ƙarfinsu, har jikinsu ya soma sanyi wasunsu suka shiga nitsewa, Sultaan ya jima yana ƙoƙari kafin shi ma ya sare tsananin gajiya da galabaita, ruwan ya ja shi. 

*2 WEEKS LATER* 

*ZEENA POV*

Idanuna na sauke kan matar da muka yi sabo da ita cikin ƙanƙanin lokaci wadda ta yi min halacci duk da kuwa Ni ma na aikatu a hannunta, na kama hannunta na riƙe na ce “yanda kika kyautata min Allah Ya kyautata miki, na gode sosai” 

Ta yi murmushi ta ce “babu komai, Allah Ya kaiki lafiya” 

“Ameen” na ce tare da rungumeta, sannan na shiga jirgin da aka gama lodi sai mu ƴan tsiraru ake jira. 

Ban san dalili ba tun da aka shaida mana mun kusa isa garin gabana ya shiga wani irin faɗuwa, hannuna na ɗora saitin zuciyata na ce “Amma ina jin tsoro, ya zan yi?” 

Wata tsohuwa da ke gefena ta dafa ni ta ce “halan WHITE PALACE za ki?” 

Nodding kaina na yi ba tare da na kuma cewa komai ba, idanunta da ke ta yawo kaina ne duk da kuwa ɓoye fuskata da na yi da baƙin yadi saboda kallon, idanunta ƙurrr suka tsaya a wuyana, ta miƙo hannu ta taɓa sarƙar da ke wuyana ta ce “You are a princess!” 

“A’a!” Na ce a taƙaice 

“Amma kike ɗauke da shaidar jinin wannan masarautar, and look at you, you are so beautiful like an angel, even if you dress in rags you don’t look like a pauper” ta ce idanunta na going round my face 

“Does the necklace belong to the palace?” Na ce 

“Tabbas duk mai sarƙar nan ɗa ne a wannan masarautar” ta ce 

Na ja doguwar ajiyar zuciya yayin da na ji wani irin ɗaci na taso min, tabbas mai sarƙar nan da hannuna zan ga bayansa, shi ne silar komai, hawaye suka shiga zirarowa daga idona, duk yadda matar ta so mu tsawaita hira ban kuma tankata ba, baya ma na juya mata ina kukan zuci yayin da hawaye suka shiga zuba a idona. 

*THE WHITE PALACE* 

Bayan an gama min screening haɗe da caje har na bala’i suka bar ni na shiga gate ɗin, sosai na zama baƙauyiya don tsaruwar da masarautar ta yi tamkar ba a duniya nake ba, haka na shiga kalle-kallen abubuwa don ban ma san inda za ni ba, bigewa na yi da wata da ke sanye da koren yadi wanda na ga kusan kafatanin masu aikin irinsa suke sanye da shi, da hanzari na duƙa ina tayata kwashe kayan da suka zube, bayan na miƙa mata na ce “ki yi haƙuri”, ɗan zaro ido ta yi tare da cewa “You are so beautiful” 

Murmushi na yi na ce “ko kin san inda zan ga Jani?”, Matar da aka ce na zo za ta sama min aiki ke nan. 

Ta gyaɗa kai tare da cewa “mu je na raka ki”, muna tafiya tana satar kallona har muka isa. 

Bayan mun gaisa da matar na gabatar mata da kaina tare da sanar mata wadda ta ce na nemeta, cikin jindaɗi kuwa ta ce “ta shi mu je”, na bi bayanta tana ta tambayata matar da na baro, wani katafaren gini muka nufa wanda komai na cikinsa ya kasance white da ratsin silver, bayan mun shiga aka yi mana iso sannan muka ƙarasa wani ƙaton ɗaki wanda ya wadatu da kayan more rayuwa, kan farin carpet ɗin ɗakin muka zube, mun jima sosai kafin wata mata tsohuwa wadda a ƙalla a shekarunta na haihuwa za ta yi tamanin da ɗoriya, sai dai ban da tamushewar fata irin ta fararen fata ba za ka fahimci tsufan nata ba, tsohuwa ce mai cike da kwarjini da sakin fuska, da fara’arta ta zauna kan kujera. Yadda Jani ta gaisheta, Ni ma haka na gaisheta 

Jani ta yi gyaran murya tare da cewa “Kala dama sabuwar ƴar aiki ce aka samu, shi ne na ce bari in kawota ko akwai abin da za ta miki” 

Kala ɗin ta ɗago da idanunta ta tsura min su, sosai ta shiga kallona babu ɗauke ido yayin da na sunkuyar da kaina, can ta nisa ta dubi Jani ta ce “kina iya tafiya” 

“Na gode” Jani ta ce bayan ta kuma gaisheta sannan ta fice, dubana ta yi sannan ta nisa ta ce “mene sunanki?” 

“Zeena” na ce kaina a ƙasa

“Daga ina?” Ta tambaya

“Andala” na ba ta amsa 

“Kina da sirri?” Ta tambaya tana tsareni da idonta 

“In sha Allah, zan zama kurma, makauniya, bebiya ga kowanne al’amari da na ji, ko na gani” na ce 

Ta murmusa ta ce “da kyau!” Sai kuma ta yi shiru 

Na ɗan ɗago na kalleta, da sauri na sauke kaina don wani faɗuwa gabana ya yi duk da ban san dalili ba. 

“Za ki kular min da mara lafiya, cin shi, shan shi dukka suna hannunki, haka ko da ya fara samun sauƙi ya zama sirri tsakanina da ke, idan kika kuskura kika haɗa baki da wani aka cutar da shi, na rantse da wanda raina yake hannunsa sai na datse jijiyoyin numfashinki!” Ta ce tana ƙura min idanunta cike da tsoratarwa. 

Kaina a ƙasa na ɗaga mata kai. Ta jima tana jadadda min wanda hakan ya sa na fahimci muhimmancin wanda zan yi aikin wajensa sosai, inda hankalina ya kwanta shi ne da ta ce min mara lafiya ne. Bayan nan ta kira wata daga cikin ma’aikaciyar sashenta tare da cewa ta kaini sashen Prince ɗin. Godiya na yi na bi bayan maid ɗin hannuna ɗauke da ƙunshina. 

Nuni ta yi min da wani madaidaicin building sannan ta ce “nan ne” 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button