WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 3

 ????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                  Free Page    

               03

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

  

  Zaune yake a bakin ruwa yana shan iska,sanye yake da ƙananan kaya irin na turawa,gaba ɗaya hankalin shi na kan waɗansu turawa dake rawa abikin ruwan daga su sai ɗan kanfai (Pant) hankalin su kwance,kallon su yake a zahiri amma a zahirin gaskiya ba a kansu hankalin shi ya ke ba,domin yayi nisa wurin tunanin ta yanda zai samo ma kanshi mafita a wannan lamarin,duk ta in da yake tunanin lamarin zai zo da sauƙi,amma abin nema yake yafi ƙarfin tunanin shi, 

Jin ƙarar wayar shi ne yasa ya dawo haiyacin shi,ya sauke ƙarfaffan ajiyar zuciya,

Ɗaukar dalleliyar wayar shi yayi Samsung S21 Al/Tra,wanda a ƙalla kudin ta zai tasarma dubu dari bakwai,cikin yanayi na kasala irin na wanda ya gaji da tunanin niman mafita ya ƙara wayar a kunnen shi, 

“Uncle”

Cikin masifa na ɗayan ɓangaren yace” HARIS ZAMIR,ka fita a ido na fa, wai me yasa kai ba kajin magana ne? 

“Uncle!! 

” Pls ya isa haka ba na son jin wata magana daga bakin ka,dan haka na baka daga nan zuwa gobe ka baro Malaysia ka dawo Nigeria,duk ma yanda za ayi ayi, haba ace sayin shakara uku kenan har yanzun ana abu ɗaya yaki ci yaki cinyewa,to a gaskiya na gaji,gara ka dawo a san abin yi, dan wannan karon banga abin da zaisa in daga ƙafa ba”yana gama faɗar hakan ya kashe wayar. 

Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa,kai shikam Allah ya nuna mashi ƙarshen wannan abin kowa ma ya huta,, tashi yayi daga bakin ruwan yana karkade jikin shi,saboda yashin wurin,a hankali yake ta fiya,har zuwa bakin wata dalleliyar mota, wanda yana isa wani Bature ya buɗe masa kofar motar da sauri, shi kuma ya shiga,wani madaidaicin gida aka buɗe masu Get din suka shiga,gaskiya gidan ya haɗu ba ƙarya,ƙarami ne madaidaici amma yana yin tsarin gidan kadai ya isa ya tafi da imanin mutum,,kamar dai dazu haka ma yanzun yazo ya buɗe mai motar ya fita,kai tsaye cikin gidan ya shiga,dan a zuciyar shi yake raya gara yaje ya fara haɗa kayan shi  kafin Uncle ya ƙara kira,dan ya san wannan karon in bai koma Najeriya ba ys tabbatar yana iya biyo shi ya koma da shi. 

          GIDAN ƊAN NANNE

Sai da ta tabbatar ta daku tukunna sannan ta kyale ta, tana ci gaba da masifa, yayin da Baba Sani ke taya ta”yar banzan yarinya,wacce ake gudar mata wahala amma ita tana rungumar shi,to in ƙara ganin ki da ita,in ba shashaba duk cikin yaran gidan nan wakike gani tare da ita in ba ke,ba gasu Karima, Maimuna,Salma,amma baka ganin kowa kusa da ita sai ke,tunda su sunfi ki wayau,to ba da ni za ayi wannan ba,in ƙara ganin koda kafar ki ne a shiyar bama tare da ita ba saina kusa kashe ki a gidan nan”ranar dai Islamiyar da Hafiza bata jeba kenan.

Tun bayan wucewar Hafiza take zaune a binta,can kamar kuma wacce aka tsikara ta tashi ta shiga haɗa kayanta, sai da ta haɗa iya wanda zata iya ɗauka,sannan ta daura a kai ta fito,dakin Inna Saude ta leka,ganin bata ciki yasa ta nufe kicin dan ta san zuwa wannan lokacin ta na kicin din, ai kuwa anan ta tarar da ita, 

“Inna”

Da sauri ta juyo ganin ita ce yasa ta sauke ajiyar zuciya,dan sam ba ta ji zuwan taba,sai Sunnan ta da ta ji an kira gata kuma a tsaye da kullin kaya a kai, 

“Na’am Asma’u, ya aka yi ne, ina kuma zaki da wannan kullin kayan? 

Dariya ta yi wanda ya ƙara baiyana fararan haƙoran ta, wanda suke jere a bakinta da ɗan wushiryan ta sama da ƙasa” Inna zan koma ne gidan Malam ”

Kallon ta Inna Saude ke yi tana salati”Ya Allah daga gareka muke,kuma daga gare ka muke niman taimako,wai ni Allah ka gwada min ƙarshen wannan abin”ƙara kallon Asma’u ta yi, wacce ke tsaye sai wage mata baki take yi. 

Wani miyau na fargaba ta haɗiye,,dan ta san yanzun tsayar da Asma’u ba ƙaramin abu bane a yanzun, to ya zata yi,wani dubara ne ya faɗo mata,kallon ta ta yi,cikin duba ta ce “yauwa Asma’u dama akwai wani tsakon da nake son in baki ki kai ma Malam”

Dan waro ido waje ta yi “da gaske Inna”

Itama murmushi dole ta kakaro,domin Allah ya gani tana tsoron haukan Asma’u,sai dai kuma ba yanda za ayi tana ganin ta ta barta ta fita ta koma gidan Malam bancin an raba auren su ko,ita tana tsoron mai zai je ya dawo,sai dai fa duk da haka sai ta gwada ta gani. 

“Sosai ma, zo muje ki karɓa”

Da murnar ta kuwa tabi bayan ta, har cikin ɗakin Asma’u suka shiga,kamar gaskiya kuwa ta fara dube buɗe,”Inna a dakina kika ayiye abun”

“Eh A’a kai ina zuwa zauna a nan ki jira ni”har ta juya sai kuma ta dawo ta riƙe hannun ta suka zauna bakin gado,” Asma’u na”

“Na’am Inna”

“Kin ga dare yayi, mai zai hana ki bari  gobe sai mu je tare in raka ki gidan Malam din”

Ɓata fuska ta yi,tana fisge hannun ta, cikin magana irin na wanda ya ji haushi ta ce”A’a ni ba zan bari sai gobe ba,Malam na jira na, kawai in zaki ki zo mu tafi tare”

Ajiyar zuciya ta sauke”to ina zuwa,bari in dauko maki,, zauna nan ki jira ni”

Da sauri ta fita,tana fitowa kuwa da sauri ta kullo mata ƙofar ta saka key ta datse ƙofar da shi,tana jin yanda Asma’u ke dukan kofar kamar zata balla shi tana kuma ihu ta zo ta buɗe ta zata koma gidan Malam ne, 

Banza ta yi da ita,”da in barki ki tafi gidan nan,ai har gara ki ta haukanki a ɗaki,kuma Allah ya kai mu gobe da kaina zan faɗa ma Yaya Mudansir ya ja masa kunne karya ƙara kawo mata wani abinci a gidan nan tunda bata rasa komai ba anan,kuma haka kawai bancin ansamu yarinya ta dan fara manta shi,shine yanzun ya ke bullo mata ta haka,dan ta  lura yanzun da zaran ta ci wani abu na hannun shi, to ranar ta dungan hauka kenan akan sai ta koma gidan shi, haba ita ta gaji da wannan lamarin dole a taka mai birki. 

 Daren ranar Ahalin gidan Nanne basu yi barci ba,domin irin haukan da ta kwana tana yi,yayin da wasu suka kwana tsine mata Albarka, a kuma wannan lokacin tsohuwa Nanne ke zaune saman Darduma tana nimar mata sauki wurin Ubangiji,ranar dai haka suka wayi gari.

      Washegari da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana jirgin su ya sauka a Abuja,yana fitowa daga cikin Airport din kalle kalle yake ta ina zai ga masu kai shi gida, 

Ji yayi an rungume shi ta baya, da sauri ya juyo,ganin wanda ya ke tsaye yana mai dariya ne yasa shima yayi dariya ya jawo shi jikin shi suka ƙara rungume juna, “ai nasan sai kai, to sake ni karka karya ni”

“Yaya Haris kana kallon kanka kuwa a madubi, kaga kuwa yanda ka zama”

Dariya yayi”kai ni kan mu je kar ka cika ni da wannan surutun naka”buɗe masu ɗaya daga cikin jerin motocin da  aka zo dashi domin daukar su aka yi,suna shiga aka ɗauki hanyar Minna da su, jifa-jifa suke hira da Asim har suka iso cikin garin Minna wanda kai tsaye unguwar Millioniar Cutters,wani tangamemen Get aka buɗe masu suka shiga,ganin su a gida yasa ya sauke nauyayyen ajiyar zuciya yana kuma hamdala a zuciyar shi,bude masu kofofin a kayi suka fito,

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button