GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

[6/20, 11:24] ????????????: GIDAN DAƊI
(Duniya????)

Free page
001

Na…Oum Aphnan✍️

I’m back to the game my fans ,I hope and I promised this book will give you a maximum satisfaction ,and you will Neva regret for investing your money into the journey…As you knw and ah knw it’s oum Aphnan dai,That unnanimous writer that published more and more books that makes you to rejoice such as , Akan dadiro na , Hariji , Auren sha’awa, Jarababben namiji and on and on. So am here again ,Humm Ah dunno if you can endour my lazyness buh d only thing I knw I prepare to make your dayz….so plz matured head ! Matured head!!,if u really like Humble story go for Bariki gadona,buh this book is actually Hot,Manyan mata a karkaɗe zani a sha karatu bana labarin na gwaskayene???? mu ɗin dai Nurses’ na taɓo mu, Hhh Allow me enjoy d moment and sip a sip for a while….lolz

Bismillahir rahmanir rahim

“Out from my shade lousy gurl” yayi maganan cikin wani kalar murya mai amsa kuwwa

Da sauri ta tattare file ɗin da suka kasance nata ta fice da sauri tana share ƙwalla

Tsaki yaja ya koma ya kwanta a jikin kujeran office ɗinsa yina ɗan juyawa dashi a hankali ,fuskarsa maƙale da tabarau ,yina kallon sama cikin ɓacin rai .

A hankali aka Turo ƙofar office ɗin ,sam bai kalli wajen ba don yasan mutum ɗaya keda zarran shigo masa office oga Nazeer

“Adams meye damuwarka ,I said what exactly your problem?”

A hankali ya gyara zamansa ,ya rafka tagumi da hannu bibbiyu ya watsa masa fararen Idanuwarsa

“Adam itama ɗin batayi ba?”

Jinjina masa kai yayi
“Inajin a sake nemo wata Nazeer”

A fusace nazir ya magantu “Kasha giya Oga Adams ,ko wata mace batayi ba ko wacce batayi ba inajin wacce tafito daga dajine kaɗai can satisfy you”

Caɓe baki yayi sannan ya ɗage kafaɗunsa sama “Eh inajin hakan saboda bazan iya sex da macen da bana samun yanda nikeso ba a wajen ta see I don’t mind er bukka ce ko daji what so ever inason mace mai strong hip and heart in tayi mun shikenan bandamu da Muninta ba Ni zan iya aurenta a hakan”

“Shiyasa nace maka kasha giya”

“Look Nazeer zan samu ko In fara nema da kaina?”

A hasale yace “Gaskiya ina ganin hakan zaifi “

“To fitar mun a office”
Bai ja da tsayi ba ya fita yaja masa ƙofa, yina mamakin jaraba irin na oga Adams

………………..
Female Hostel Nursing department
8.00am

Gabaɗaya Hostel ɗin ya gama kacamewa da hayaniyar ɗalibai masu damben shiga toilet wanka su tafi aji karsu makara , Nikam har yanzu juyi nike akan er gadona ina barci na kifa ciki Banda niyyar tashi na rufa ruf da bargo

Kasantuwar ɗakinmu room of 6 ne yasa hayaniyar en ɗakin ya fara damuna don haka na ɗan leƙo da kaina ta cikin bargon kamar munafuka ina ƙarewa en ɗakin kallo ,daga masu karyawa sai masu saka uniform sai kuwa masu assignment ɗin da aka bada jiya

A hankali zainab ta ƙara so gaban bed ɗina

“Nadiya kinyi Assignment din malamin Anatomy ɗin nan kuwa?”
Zaro duk jikina nayi na koma na zauna daɓas na ɗakko text book na fallo wajen drawing ɗin heart ,idona a lumshe na ɗaura drawing book ɗina na fafara zanen heart ɗin ya cika fyalle najajja labelling na maida na ajiye na ɗauki buta timtimtim na nufi hanyar bayi zan fitsari

Ina fita suka kuwa bushe da dariya “Hhh inji dalilin da baza’a kori yarinyar nan a makarantar nan ba ,angaya mata Nurses’ en iska ne ,basu da aiki sai barci ?”

Nan Nasy ta fixgo drawing ɗin da nayi suka kuwa bushe da dariya don sunsan tabbas zaaga hauka ,haɗa kai sukayi a tare suka kai dubansu kan zanena ,amma abun mamaki yayi kyau fiyeda nasu da suka kwana suna ƙalƙalewa ,jin zan shigo yasa suka maida suka rufe suka cigaba da dariyar shaƙiyanci .

Daɓas na daɗa komawa na zauna ina lumshe ido ina jin wani mugun barci na neman saceni ,da ɗaya da biyu naga suna fita da shirin ajinsu nikuwa na ƙara kimuwa a gado na cigaba da barci ban farkaba sai ƙarfe goma saura shima,saboda yunwan cikina da ya ƙwaƙuloni ,da sauri na miƙe na kunna gas na ɗaura Dahuwar jolof rice ,na saka ruwan zafi a kettle na dama custard na juye a flask na Sha tea ,Abinci yayi na zuba a good flask na watsa tarkacen spoon da sugar da sauri na saka yamutsatsun uniform ɗina a tsatsaman jikina da niketa buga wari

Shinshinan hamatana nayi naji ina tsami da sauri na toshe hanci na lalubo turare na duddula a wajen na yayibi takalmina duk ƙura na zura ,na goya jakan bayana na riƙe basket ɗin abincina hannu bibbiyu ,na fice zuwa aji timtimtim kamar ÿar doki

Da HOD na fara cin karo ɗalibai kowa ya gansa yina gudu nikuwa da ÿan waƙe na nazo zan wucesa ,Aikuwa tuni ɗalibai suka shiga leƙen mu ta taga “Lallai yarinyar nan tanada liver,jiba bazata ɓuyaba ,kuma ga jakarta tabbatuwar yanzu take zuwa?”

Wani irin kallo HOD ya bini dashi kana yace “Daga ina ke waye ke?”

Daddagewa nayi na sauke kwandunan abincina guda biyu na yarfe hannu ina kiran Washhhhh

“Who dare are you?”
Turo baki nayi kamar zan cijesa sannan na saita yatsun hannuna aka na shiga ranƙwashin kaina saboda ƙaiƙayin da yike mun “Student Nurse “

Nuno Ni yayi da abun hannunsa “You are stupid,ji beki?”

Raurau idona yayi da hawaye ina ƙarewa kaina kallo Tundaga sama har ƙasa ,tabbas nayi squeezing Amma ya zanyi tunda ban iya guga ba? Don haka na sunkuyar dakai ban cemasa komai ba

“Wainnan kwandonan abincin fa kamar zaki ciyar da gari?”

“Wannan custard ne a ciki dasu kayan haɗinsa in ba malami a aji zan karya dashi …wannan kuma wajen ƙarfe ɗaya zan ci abincin rana “

Sakin baki yayi galala a ransa yina raya wannan tanada matsalar ƙwaƙwalwa Amma m waya bata Admission…

“Shikenan in tafi?”
“Kenan yanzu kike zuwa aji,kuma a hakan ma baki karyaba kina Hostel ba upk ba?”

“Aahhhh ai in ban karyaba da yanzu jiri ya kada Ni,aini sau biyu nike karyawa a safe to dole sai nayi guzuri haka maama na take mun in zani makaranta tuntuni”

Raɓani yayi ya wuce ,yina tunanin kiran board meeting akan tsarin bada Admission,taɓe baki nayi na ɗauki kayana na wuce aji .aiko nan kallo ya koma kaina ko a jikina na sama kujeran baya na zauna ,daidai malamin ƙarfe goma ya shigo ,nan na soma gyangyaɗi daga nan wani barcin ya sureni ban farka ba sai shabiyu ,aikuwa da malami haka na tuge hijabina na aje a gefe na fara haɗa custard Ina Sha

Tsawa malamin ya doka mun ,firgigit na miƙe tsaye da cup ɗin farau farau ɗina a hannu

Faɗa ya kama yimun daga ƙarshe yace ina tsaya a tsaye kuma in daina shan abunda nike sha ,ina kallon abuna na ajiye ,amma sai in fakaita idonsa in kurɓa ,haka har wannan period ɗin ya ƙare ban fahimci komai ba ,haka dai akayi tayi har wannan ajin ya ƙare inda coordinator ɗinmu yace idan ina barci a ringa tashina suna hasashen inada cutar tripanasomiasis (cutar barci)


Ƙarfe taran dare idona yayi ƙarƙar ba sauran barci sai sannan na kunna laptop ɗina na fara game ,har asuba ,daga nan na soma barci na na Farilla nidai haka life cycle ɗina yike dare shine rana ,kazalika rana na shine dare,karatun aji bansan me ake koya masu ba ,ban taɓa ɗaukan littafi da sunan zanyi karatuba ,nidai ganinan saidai in kewar gida ya isheni in ta kuka ,ga daini bunkumemiya amma girman iska ba wayo

A Hostel kuwa dare nayi ɗaliban suka karkasu duk suka fice a Hostel ɗin ,wasu sun tafi karatu ,wasu love garden ,wasu common room yin Kallo,wasu kuma sun fita da samari ,Abunda ya kasance da ƴan ɗakinmu kenan sun watse saura Ni kaɗai ,kamar wasa ɗakin kusa damu nike jin hayaniyarsu sama ² ,sai kuma kiji tafi da shewa ,da dararraku ƙyal ƙyal ƙyal ,tsorone ya kamani jina Ni kaɗai gashi inada tsoron kaɗaici da duhu ,da sauri na fito waje daidai nan naji ƴan makoftanmu suna kitsa yanda za su sace wata yarinya

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button