GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

Sun kira yafi sau ba adadi ba’a daga ba,Hajiyan su Adams aka kira mata mai kirki bata tsawaita ba tace ko wacece a shigo da ita

Hararansu nayi na shige ,Amma deep inside inama Allah godiya ne

Ina shiga naga gidan yayi mun faɗi ta ina zan fara ,karaf na ɗaga kaina sama ,yina tsaye dafe da belcony Ni ya zurowa ido yina mamakin liver na ,to me ya kawo Ni!?

“Malam zaka sakko ko sai na haɗaka da matarka “

Still idonsa zuru shi bai kawarba kuma ba uhm ba uhm ,a raina ne nace uhm to ko dai kurma ne? Tabbatarwa kaina shiɗin kurma ne nayi ,don haka na masa alamun kurame ,wato zan shiga in gayawa matarsa harda harɗe yatsu alaman aure ,sannan na nuna masa kaina ,na kuma yayyarfa hannu alaman duka
Kautar da fuska yayi ya bushe da dariya ,ganin zan ramfosa yasa ya shige da sauri

“Hooo Ni nadiya ,ashe dai zai gane” wata maid na gani cikin uniform da ganinta yare ce ta kwafa hula aka kamar moɗa ko irin cook ɗin nan ,ita tai mun iso zuwa ciki ,wani lafiyayyun faluka muka dunga ketawa wanda duk zamana a Abuja ban taɓa shiga irinsu ba ,ko wane falo da kalar adonsa da colours ɗin labulayen da kujerun ,a falo na uku muka tsaya ,ko ina glasses nan ta ajiyeni tai ficewarta ,kasa zama nayi na lankwashe hannuwana ina waige waige ,duk na tsarku to ko’ina glass bansan ko ana kallona ba,abu daya na aje a raina an kawoni gurin markade kaina ,dama ance masu mulki suna shan jini ,hannu na na saka aburgujejen gown ɗina wai ko na fito da wayata in kira momy ince su sakani a addu’a ,wayam na barota Hostel …..ƙiyyyyy aka wage glasses saiga wata hamshaƙiyar mace fara kwatakwal cikin arabian dress baki sak balarabiya ,ban gama ɗiban mamaki ba saidai ta washe mun baki

“Bakuwarmu sannu da zuwa zauna” kasa ɓoye mamakina nayi saida nace “La Madam Arab dama kinajin Hausa aw ƙalilan ƙalilan ” dariya ta fashe dashi

“Niko kejin Hausa gashi kinjima ” wata yarinya da batafi 10years ba ta fito tana ƙwalla kiran “Granny fofo want to collect my chuchu” ta ƙalƙalo da gudu bayanta Adams na Binta a sukwane ,da sauri ta maƙale a bayan matar da muke magana da naji ta kira da granny ,hannunta ɗauke da runtumemen teddy bear kenan shine chuchu ɗin
“Haba fofo leave her chuchu now” dariya ya fashe dashi yina sosa ƙeya. ,a raina nace Allah ya isanmu talakawa kyawawa na lilliɓe gidan mulki da kuɗi ,don Allah ji zuriya duk kyawawa ??

“Mom munyi baƙuwa ce?” Hangame baki nayi “kai baka gane Ni ba? ” Sai kuma nayi shiru cikin mamaki wai dama yinajin magana ba kurma bane

“Ga baƙuwa munyi Sweetheart” a hankali ma maimaita Sweetheart hu’um ,duk juyawa sukayi suka kalleni ,shikuwa ya sama kujera ya zauna ya cafko little Amal ya zaunar da ita a cinyarsa “wa na kama”
“Nine fofo”
Riƙe ƙugu nayi “malam wajenka nazo fa” ɗagowa yayi ya kasheni da ido ɗin sa wani ɗigon blue da ya ƙarawa idon haske haka yamun ɗau a cikin ƙwaran idona ,da sauri na kauda kai na waiga na kalli mamansa

“Ina yini Hajiya na kawo maki ƙaran wannan tuzurun ne don naga kuna mugun kama ,ƙila yaronki ne ” guntse dariya tayi jin na kirasa da tuzuru shikuwa ƙufula yayi “ke nine tuzurun”
“Ha’ah to tsawa zaka mun ko tsoronka kake so inji ? Kai ba tuzurun bane ,ji beka gote gote kana bin yarinya “

“Yawwa faɗa masa mu daughter kamar kinsani sa’oinsa a kauye yaransu uku uku” dafe baki nayi “Au hajja ashe kunsan kauye ?”
“Ke out from here ,don’t lay your rubbish here”
“Kasan Allah ,kwarankwatsa in kaga na fita a gidan nan to ko an ƙwatar mun encina akan fallatsa mun kwatami da kayi ka ɓata mun jikina “
“Ya Salam,i hakuri kinji” hakuri momy Safiyya ta shiga bani har saida naji kunya ,daga ƙarshe tace me kikeso in biyaki dashi indai zaki yafe masa
“Yaci arzikin ki da wallahi saidai in ya gama shigowa makarantar mu ,don saina sa an tararratsa masa mota an kyakyeta masa lafiyayyen fatar nan da yake sakashi jin kai “

Godiya ,tayi mun tace in zauna a kawo mun abinci kuwa zamana nayi ina hira da little ,yarinya mai wayau saidai ƙal ƙal da ita duk sai naji na muzanta ƙazanta ashe baida daɗi?

Ana kawo mun abinci na sauka ƙasa diraha ,na fara zuzzubawa a flate saida na zuba duka na sa hannu na fara danna ina korawa da chivita saida na shanye babban kwali da brown yam da rabin kaza yaji souce ɗin kwai da hanta ,na cinye fried rice ɗin da aka hado mun dashi tas na gungure anan ina juyi kamar falon uwata wani baƙiƙirin ɗin zufan datti yina tsatsafo mun ,Adams da mamaki ya gama isarsa rafka tagumi yayi yina kallona kamar zaimun kukan tausayawa saboda yanda yaga na buge abincin nan in shine daga dakin sai gadon Asibiti kila

“Sweetheart yanzu saika ɗauketa ka maidata inda ka ɗaukota ,kuma ka ba iyayenta hakuri ƙaryan taurin kai kakeyi badai kai ka nace bazaka rinka fita da guards ba ,watarana zakasha kara ba baki nayi maka ba”

“Mom iya gaskiyata na fada maki ban santa ba “
Wani doguwar gyatsa naja kamar gardiya ,

“Baka Sanni ba? So kake ina tona office ɗin en iskan da na kamaka a ciki”?

Miƙewa yayi yana nunani da yatsa “ke na tattaka ki ,waike wata irin baƙar daga ce ,bansan kiba kin manna mun sharri kuma…”

“Aah malam da bakina ba’a cuta na ,muje office din doctor Jabir din in bai sanka ba ,kuma abar cemun bakar daga don uwata bata haifeni a…” Ɗaga mun hannu hajja safiya tayi “ya isa kiyi haƙuri dota,a ina kike a kaiki gida yamma nayi”

“Yoo innayi dare wa ya damu dani take me like homeless child a hostel Nike wai lallai sai nayi Nursing” nan na fara wassafa mata labarina

Ji tayi a take ta na sona “wayyo ennan kiso Nursing kinga little mamanta nurse ce ,yarinyata ce ƙanwar Adams tana shekaranta na karshe tazo mana hutu bayan tayi arba’in ɗin little , a hanya sukayi accident ta rasu ,sai jaririyar a ka kawo mana ,gaskiya inason Nurse sosai a raina ina kallonki sai naga kamar ina kallon maman little ” rau rau idonta yayi kamar zatayi kuka “Allah sarki kiyi hakuri nayi Alƙawari zanyi karatun Nursing inzama nurse saboda ke” kaji kalan dangi irin na Nadiya???? Bata zama nurse savoda zaɓin iyayenta ba zata zama saboda Adams
Godiya tayi mun a take ta karbi Number mamana suka ƙulla ƙawance ,ta sa govement car ya maidani school

Saura page biyu Na kyauta ya ƙare ,ai ƙoƙari a biya kudin typing ,kar a jira na sata don Allah
Masu son biya chat me up via 09065990265
[6/20, 11:27] ????????????: GIDAN DAƊI
(Duniya)

Oum Aphnan✍️

Free page
009

Juya wayar momy ta ringayi a hankali ,har Anty nusaiba ta ƙaraso
“Momy dawa kika gama waya yanzu ?”
“Matar gomnan garin da Nadiya ke schooling”
“Ahhh momy ya akayi ta sama numberki”
“Haba nusaiba ya kike abu kamar baki san halin er uwanki ba? Taje tayi wani rashin jin ne ga dukkan Alamu shine aka karɓa numberna gashi yanzu naji tana roƙona wai in barta ta zauna a gidanta zatafi samun kula”
“Aah momy karki yarda zamani mai wuya daga kiran waya bai kamata ki saurin amincewa da ita ba ,ta je makarantan ta ta zauna yafi mata”

8.30pm
Koina na makarantar ya ɗauki haske wasu lafiayyun motoci sun cika ko ina da ina na love garden zuwa ta bayan Hostel ɗin mu , kausar ne ta fito saye cikin wani riga mai jikin roba ² mara nauyi ya sauka gwuiwarta kaɗan ,ba brazier ko pant a jikinta sai kimunu da ta ɗaura a saman kayan ta ɗaura wani jibgegen hula Dubai designers ,Dama lissafinta ba mayafi taxo ta raɓa ta sunsunawa security on duty kuɗi ta shige motar prof namadi suka wuce hotels ,hiran karatunsu sukayi sama ² inda ya bata ƙwarin gwuiwar indai suna cikin department din to ba ita ba daidai da ƙawayenta basu ba samun carry over in anyi jarabawa koda kuwa basu rubuta papern ba . Godiya tayi masa sosai suka cigaba da hira ,tana ganin ya soma tattaɓata ta fakaici idonsa ta danna recording

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button