GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

“Anty zoki kaini in siyo awara Mana”
Harara na tayi batace mun komai ba ta cigaba da dicing abunda ke gabanta
“Antyyyyy” na ƙwalla mata kira da ƙarfi da sauri ta ajiye wuƙar a kan chopping board ɗin sannan itama cikin buɗe murya tace “what?”

Kwaɓe fuska nayi kamar zanyi kuka “Anty haba manaa I’m craving for it”

“Ina aiki to” fushi nayi
“To bari in sama keke in je Ni kadai in ma na ɓace ai sai ki fito nemana “
“Aah karki fita nadiya ,kinga momy taje aiki inta dawo bakya nan Ni zatayi wa fada ba kowa a gidan”

Ko sauraron ta banyi ba na yi ficewata ,kafin tayima security magana har na fice dagani sai room slippers da Kitty band ɗaure a saman goshina gashina da relaxer amma fa da gani ba comb ,Amma ci saane gyaran Anty .

Saida nayi nisa nabar get ɗin estate ɗinmu kafin na sama keke na shiga masa kwatancen inda inda zani hannuna katakam da 400# yina tsayawa nace nawa kuɗi ka ?”
“Dubu daya”

“Sannu ɓarawo ka fara fashi da makami ne? To zo ka danna mun wuƙa ƙila innaji zafi in baka ,ko kuma muyi dambe wanda yasha wuya ya bari”

Kashe keken yayi ya nunani da yatsan sa “ke na fiki zama daƙiƙi yanzu zan tumurmusa ki anan ban kuɗina Malama”

“To dukana zakayi in ban bada ba dakanni to banza mai suffan Zomo ji kunninka fakal fakal mummuna kawai” harzuƙa yayi zai wanka mun mari ,da sauri wani saurayi dake cikin keken ya dakatar dashi “shikenan muje zan biya ” hararansa nayi ,na wuce abina ba tareda nama wanda ya biya mun godiya ba .

……A gaban shagon da ake awaran na tsaya wajen yayi kyau kamar wajen yin kabab wai just awara an masa adon wuta ko’ina glasses

“Anty a bani awara”
“Na nawa en mata ?”
“Anty na ɗari kuma a kyauta”
Murmushi tayi sannan ta fara faɗa mun farashinsu
“Wara mai ƙwai robansa 500# ,mara kwai 350# ” zaro ido nayi kamar ta faɗa mun abun tsoro “Gaskiya kayanku da tsada wallahi a garinmu biyar² ne yankan awara ,haba sai kace mutane zasu baki yanke talauci ,Hajiya bazaki taɓa arziki da suyan wara ba gwara ma kiyi arha haba don Allah ” tsit akayi nata kallona nikuwa sai yarfa masifa nikeyi kamar tace bani kuɗin ki dole

Shiru tayi mun tanata saka ma mutanen wajen takeaway din awaransu a ledan thank you tana sallamarsu.

“Malama wai haka ake attending costomer a garinku? In bazaki bani bane sai kice Nadiya awaran nan ban saida maki Kin ga sai in kama gabana ,baki tsayar dani kina sallamar wainnan ba sai warin rana sukeyi “

“Na nawa zan baki” saida na harare ta “Ai sai ki bani daidai kuɗina ko malamansu “

“Ke waike wata irin balaƙaƙƙiyar yarinyace ,nasan kuɗin ki ne sai kice na kaza “
“To na 350# tunda so kike kowa sai yasan 400# gareni” bata ce komai ba ta amsa ta saka mun a leda ta miƙo mun ,sannan ta ɗan rage murya “Ba canji “

“Me kike nufi ba canji to Ni ina ruwana nemeshi ki bani 50# ɗina ” miƙa mun hannu tayi ban kije ki samo ki kawo mun “
“Taf wallahi ban badawa ” na fiddo shi a ledar na saka na saka daya a baki ina muzurai ina zaro halshe ,nan kuma na dasa masifa ta cika yaji dole sai ta biyani kuɗina na fasa siya

Kamar an hurgo mutallib ta layin ya hango wata kamar Ni ,a ransa yace “Kamar nadiya ce can fa ” karya akalar motarsa yayi ,ya gangaro aikuwa nice Ina tsiya inda nike shiga ba nan nike fita ba ,nayi zufa nayi sharkaf

Janyo hannuna yayi ta baya ,da sauri na waigo na ɗaga hannuna zan mari Kawaï sai na gansa tsaye a hankali na sauke “Haaa ka Kuru da kasha mari Ba ruwana”
“Ai na sani shiyasa nayi gyaran murya uhm uhm” dariya na fashe dashi na kama masa waƙar da nike masa “Abokina mai kyau…..Abunda ya ɓata ka…….Danƙwalelen kai”

Sosa ƙeya yai cikin jin kunya duk mazan wajen saida sukayi dariya kuma Yes yinada ƙaton kai ɗin
“Mutafi in kaiki gida”
“Taf canjina Nike jira “
“Canji nawane canjin?”
“Hamsin mana”
“Haba jooooor ,muje kawai” ya kamo hannuna ,aikuwa masifa na shigayi ina diddirke ƙafa shikuma yace lallai sai mun tafi ko kuma mun ɓata daga yau

“To wai kai ina ruwanka ,kasan zafin kuɗi kuwa yanzu kawai saaaaa,sai in bar mata Naira har hamsin ,wallahi bazan yarda ba “
“Haba don Allah hamsin ne fa ,kamar ki big babe”
“Ba haba ba habu ,hamsin ɗin ne kake raina wa lallai ma mutallib ɗin nan to Allah bazan yarda ba sai an biyani do asi ban dashi bayan hamsin ɗin nan ita na cuceta ne ba kudinta daidai na bata ba iyeehhh?” Daidai nan muka isa gaban motarsa na fara jan handle ɗin ƙofar da ƙarfi kamar zan karya masa
“Ni buɗe mun ƙofa In shiga” saida ya shiga motar ta driver site ya cire securityn sannan na buɗe na faɗo ciki ina masifa ” na buɗe takeaway din awaran na ƙara saka ɗaya a baki, raina nace “Ba laifi akwai daɗi fa” amma a sarari na sake buɗe wutan bala’i “Aikin banza a 350# ga yaji anya matar nan ba mayya bace kuwa?”

“Haba babe ya wuce mana “
“Meye ya wuce ya zaka hanani magana bayan ka sa an danne mun 50# ɗina “
“Shikenan babe zan biya..zan biya duka Plz kiyi shiru fada saikace gwaggo”

Murmushi nayi na kamacin awarata ina enjoying dadin waran ,shikuma ya tsaya amsa waya kafin ya ja mu tafi

Wata kyakyawar budurwa na gani tsaye cikin wani doguwar fitted gown er lukuta da ita kamar Ni mai choco skin tayi kyau kamar me shirin zuwa party ,tsaye a bayan wata mota sai ɗan zarya takeyi kamar mai wani uzuri , a hankali na ajiye masa roban awaran a inda yikesa goran ruwa da phones ɗin sa ,na zura yatsuna a baki na fara tsotsewa na karkace na fiddo wayata iPhone 7+ “wow Babe kinyi kyau Bara in maki hoto na manna wayar a jikin glasses ɗin gaban motar ” da sauri mutallib ya taɓa hannuna duk da waya yikeyi official

Sauri nayi na gotar da kafaɗana “No plz Barni in ji dadin rayuwata ,mata tayimun kyau sai kace bazan ɗauke ta ba hu’ummm” tsaki naja “Ahshhhhh kaga taki tsayawa hoton yayi kyau ,bari ina mata video ,nan na maida video ba zato naga ya Hisham ya taho ta bayanta a hankali cikin sanɗa ya damtse mata ido ,a hankali tasa hannu ta zame hannunsa ta birkito ta juyo suka fuskanci juna kawai sai ta daka tsalle ta ƙanƙamesa suka rungume juna ,muryarsu na shigowa motar mu a hankali “Sweet I missss youuuuuu????” ta faɗa kamar zatayi kuka ,zaro ido nayi ina ƙaiƙaya ido wannan kamar ya Hisham ??? Na waiga ina kallon mutallib ,eh shine
“To wannan er uwarsa ce ko uwarsa ji wani iskanci a gefen hanya kamar Arne ,gaskiya bazai zubar wa yayata mutunci ba ace ta auri ɗan iska dole sai an fasa auren nan “
“Haba wait naaah kashe vid. Ɗin nan” waigawa nayi daidai sanda tace “Love ba wata masoyiya ko? Saboda kasan dai na daɗe ina kamu tun kafin in tafi Austaraliya” fiƙi fiƙi nayi da ido inason inji amsar sa

“Haba wata isa ta soni ga zazzafan lady irinku a town Singleton ,kinsan abunda ake kira Singleton ? To haka nike har yanzu I’m searchy”

Hangame baki nayi na ɗaura hannu a ka “Kenan ba wata masoyi ya ?” Ta tambaye shi cikin tsokana

Jan kuncin yayi “come on er lukuta muje Dalla wa zata ganmu” da gudu ta bishi da dukan wasa suna dariya ya maza ya buɗe car ɗin ya shiga itama ta shiga

Ji nayi kamar in fasa ihu “Ayya ba masoyi ya Ya Hisham amma kayi shuka a idon makwarma ,inji yanda za’ayi auran nan mugu mayaudari” da sauri na fara daddana waya zan yi kira “babe me zakiyi ?”
“Zan kira Anty Nusaiba mana”
“Haba don Allah karki hada Hisham da fiance ɗinsa “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button