GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

7days Later
Yau Jumu’a ne don haka da wuri na dawo makaranta ,sosai naga gidan akwai en canje canje alamun anyi baƙi ,amma basu dade da watsewa ba ,caɓe baki nayi “ko su waye oho ,koda Ni Nadiya da nike a raɓe kamar saifa meye damuwana da matsalar gidansu? Barema gidan mulki da kullum suke karɓan baƙi”

Jakata na yar akan kujera takalmina ɗaya a bakin ƙofa ɗaya kuma saida na kai kan gado na cire don haka a nan kan gadon na yar ,na cire brazier hijab ɗina na wullashi kan dressing mirror ha tsaya ina kallon kalbar kaina da yayi wata biyu a kitse ya danƙare ba alamar tsaga ,wani kuka naji cikina yayi mun ƙululu alamar yunwa ,ga fitsari ya cikamun mara wanne zan fara? Dama dai na saba matse fitsari ,don haka nawuce kicin da gudu inci abinci

Namiji na gane tsaye da gajeren wando da farar riga kunnensa ɗaya da bluetooth yina gyaɗa kai yina yanka plantain ga wasu a wuta yina soyawa gefe ,ɗaya Yayi ganishing fried rice da be wuce 15spoon ba da kaza ,sanɗa nayi saɗaɗaf na sunkuce plate ɗin na fita falo a daga tsaye na cinye abincin ,Adams da yaji kamar an gifta masa da daddawa dube dube ya kamayi baiga komaiba don haka ya ƙarashe abunda yikeki ya juye a plate ya ɗauko kwalban kechup ya fito dashi falo ,ya ajiye ,nikuma ina ganinsa na maƙale a bayan labule saida ya shiga ɗaukan plate din abincin da ya ajiye da baisan na cinye ba na fito saɗaɗaf na sunkuce dayan plate ɗin na tsalala kechup ɗin na fara cuccusawa a baki,shaye da mamaki ya fito ,a ransa yina cewa Aljanu garemu a gidan ne?
Zare ido yayi ganin ba filet ɗin abincin da ya ajiye sai ruwa ,sannan a hankali yake shaƙo warin daddawar nan a falon ,buɗe bututun hancinsa yikeyi yinason shaƙo inda warin yike fitowa ,ɗif na ɗauke numfashina saidai abinda ban sani ba bin warin jikina yikeyi ,caraf ya fizgo Ni a labule aikuwa sauran abincin ya ɓare ,Ihu na fasa shikuma yai saurin cikani ya liƙe hanci
“Ke ! ” Ya daka mun tsawa
“Ke ke zuba warin nan? Kamar daudawa …wait ba wannan ba nayi kama da saanki ko ɗan aikinki da zan girki ki ɗauka kici ?” Hura hanci na kamayi na mike na fara tafiyan fankama zan shige ɗakina

“Heyy who the fucking idiot are you Ina magana kina tafiya ,so You don’t have manners abi,you the stupid she-goat”
Caɓe baki nayi na juya na yarfe masa hannu kamar mai yanga ,ko irin er daudu ɗinnan
“Arab blood ,turancinka ya cika ƙalƙale da yawa kai mun turancin hausawa ƙila in iya ji amma wannan lanƙwashe Muryar da kake yi sam bana fahimtar ka”
“Amma kina fahimtar Bulala ko? Ƙazama kawai “
“Hmm kanka akeji mahaukaci ya faɗa rijiya ,nidai yanzu na sama releif tunda na rage yunwa inje in rage mara inje kuma innema abinci”

Tsaki yayi ransa a ɓace don ji yake in ya biyemun zai iya shaƙoni ya daki banza amma kuma ,bazai iya tunkarana ba saboda warin jikina

Ɗakin momy ya nufa tana cikin waya ya shigo ɗakin cikin ƙaraji yake magana “mom waccan stupid brat ɗin me takeyi a gidan nan kuma ba an bata haƙuri ta koma inda aka ɗauko ta ba”
Haƙuri taba wanda suke waya ta kashe a hankali ta fuskance sa
“Sweetheart wa kake nufi”
“Waccan mai warin daddawar”
“Subhanallh wai Nadiya kake nufi? Allah sarki ta dawo gidan nan ai da zama”
Zaro ido yayi kamar an watsa masa wuta “momy my warin daddawar ? Na shiga uku ,mom ta cinye mun abincin da nayi spending hours inayi in just few minutes ” guntse dariya tayi tana mamakin yanda Adams ya hakikance yike masifa Wanda Sam hakan ba halinsa bane
“To kayi haƙuri bata sani bane ,dama kaine da fitinarka wai baza kaci abincin masu aiki ba ,amma bari insa a maka wani “
” Oh haba mom ,Taya zakice Bata sani ba ,wlh ta sani ,sanɗa fa tayi ta ɗauke abincin ta cinye “
“To kayi haƙuri zan mata magana bazata sakeba”
Hanyar fita yayi baice komai ba ,sai kuma ya dawo kamar wanda aka zungura
“Mom don Allah kice tayi wanka bazan iya gwama numfashina da ita a gidan nan ba she’s nasty absolutely “
“Wayyo nayi magana har na gaji nadai lura nadiya tana gaba da tsafta amma ƙila in kai kayi mata magana zata jika ,kai mata maganar Plz”
“Mtsew Ni? Allah shi kyauta ashema Ni tsara ta kenan”
Shiru tayi ta ƙyalesa ya fita yina sababi abunda ya zame mata banbaraƙwai wai Adams ne ke long sentence akan ƙaramin bacin rai yike ƙorafi


Yau saturdae ,kowa yina barcinsa Nikam idona ya soye yunwa kawai nikeji ,innayi nayi in kalli agogo in fita in kewaye ba wanda ya farka har ƙarfe goma daga nan ne fa haƙurina ya ƙare ,nan na miƙe cimik na futo kicin na sama bread na hada tea na zauna dirshan a kasan tayis ina karyawa sai nishin wuya nikeyi inajin kamar ana ƙwaƙule mun en hanjina

Kicin ɗin ya shigo yina ganina kamar yaga dodo ya fito da sauri ,ya je gefen store inda akwai terho a maƙale da jikin bango Ya daddana ya kira room din momy ,hajja safiya da farkawanta kenan daga barci a kasalance ta ɗauka duk kawowanta cooks ɗin ta ne suke magana
“Hello haba Madam Jerry kinsan ranar saturdae Bama fitowa sai 12pm meyasa zaki kirani yanzu bayan nasan komai akwai shi akicin”
“Momy its me”
“Oh sweetheart ya na jika a kicin”
“Momy good morning,momy zoki koran mun yarinyar nan a kicin zan girki”
“Subhanallh wallahi banason clashing dinda kuke samu kaida nadiya ,she’s so friendly don’t mind her silly lapses”
“Silly? Momy kikace silly ? Ƙazama ce fa ,momy zan bar gidan nan kawai in bakuson ganina kawai”
“Shikenan on my way” hanging yayi ya koma can falo ya zauna

Tundaga ranar muke samun matsala ,ya soke ma kansa cin abinci tare damu saboda wai ina wari ,tun abun na maidashi wasa ban damuwa har raina ya soma ɓaci saboda yanda yike tsinkani ko acikin jama’a ne ,nadai lura shiɗin rude ne ,ga ƙalƙalin tsafta kamar mace sam baya hada shirginsa da en aiki tsabagen tsafta kuwa baicin abincin en aiki saina mamansa
Yau ina kwance ba zato naga wullaye sun shigo mun ɗaki da kayan aikinsu a kwalaye ,zumbur na miƙe ina gyara kallabi ,fuskewa yayi fuskarsa maƙale da baƙar shade ,yina directing ɗin su a cikin toilet ɗina

Tashuwa nayi zan tsiya “malamai lafiya zaku shigo Mun ɗaki ba neman izini “ke karki matso nan ƙazama kawai fitinanna ,me za’a gani a jikin naki dasai an tambayi izini ? Ji kanki ? Ko a gidan mahaukata ba’a barin gashinsu da ƙazantan nan ,Mtsewww mahaukaciya kunji kui aikinku ku fito” yina dasa aya ya juya ya fita

Tsayawa nayi ina ƙarewa kaina kallo ,yau raina ya ɓaci sosai ,a take wasu muggan ƙwalla suka sirnano mun a fuska ,yaune ranar farko da akaci fuskana akan ƙazanta ya dameni ,yaune ranar farko da wani ya zageni raina ya ɓaci ,a take naji kewan Anty Nusaiba ya dasu mun a rai ,Allah sarki sister tana mun magana da rarrashi bata taɓa zagina why ya zama Arrogant to me?”

Ɗaukar wayata da littafi nayi na fito falo zan zauna a kujera cike da hantara yace “he.. he…he karki zauna anan baki ganin belongings ɗin mai tsafta ne a wajen ?” Girgiza kai nayi cikin damuwa na tsaya ba tareda na zauna ba , na kira Anty Nusaiba ,saidai hatta katse bata ɗaukaba ,shiru nayi nidai Banson komawa ɗakina saboda maza da suka shigar mun toilet , kawai sai na jawo tim Tim naje can nesa dashi na zauna ina ɗan dudduba littafin hannuna ,haka saiga mazan sun fito zasu wuce “Hajiya zamu wuce” a hankali na waiwaya na kallesu “ok sorry Ina zuwa” naɗan ja fasali inason in fahimci sheɗarar da nike
“Dalla jacan daƙiƙiya basu waje ,kin wani takarkare don ace mai karatu nan kuwa bahuwa ce ɗumama benci ake ko anje makarantan “
Ɗagowa nayi nayi mitsi mitsi da ido zan masa rashin mutunci “zagina zakiyi ko ƙaƙa? Ohyeah spit it out,yanzu in maki duka “
Nuna masa kaina nayi alamun ƙwalwarsa ba lafiya ,na kwashi kayana zan wuce ,a zuciye ya biyoni ,nakuwa danna a guje na kulle ƙofata daidai nan momy ta fito “haba sweetheart me yarinyar nan ta tsare maka ,Plz ka ɗagawa Nadiya kafa plz amana fa aka bani ita tanada gatanta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button