GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

Lokacin da na zana jamb ɗina a shekaran Anty Nusaiba ta dawo 9ja da shaidar kammala degree ɗin ta a medicine ta fara inten ɗin ta anan Abuja
Sosai taga rashin jina yayi gaba don haka ta fara jana a jiki saidai Nikam ina nayi nesa

Anty Nusaiba tunda ta gama degree dinta ta fara tunanin yin aure saidai kowani saurayinta yazo nice nan mai kora mata su da baƙin halina ,abun yina damun Antyna amma ya zatayi dani…..?
Ni Nadiya ƙazamace Ni kaina na sani don akan wanka kullum sai munyi faɗa da Anty Nusaiba ,akan ɗakin kwana kullum sai munyi dambe don takance mai warin maza bazata kwana a ɗaki da itaba sai nayi wanka ,in tsiyan ya ishi Iyayenmu sai su roƙeni inje in wanka to sananne zanyi ,Abu ɗaya Anty Nusaiba ta mora girki, subhanallh duk cin abinci saita take table da abinci munci naci a fitar da ragowa, wannan yasa na liƙe mata tanayi inaci tun a wuta ,hakan yasa nasan yanda ake sarrafa abinci amma yiɗinne dai banayi kuma ko an sakani haka zanta kuka wai ai ga Anty Nusaiba nan

Don’t think Ni yarinyace shekaruna Sha bakwai a duniya ,amma childhood characters suna wulwuli da rayuwata

Akwai wataranan Asabar ba aiki kowa yina gida tun safe yaya Nusaiba ta gama mana abinci ta shiga wanka ,ta fito tana ta en gayunta a gaban dressing mirror ,juyi nayi na wuce dinning na lafto chips da farfesun kaza ba brush nahau cusawa saida naci na ƙoshi nayi gyatsa sannan na haɗa tea mai kauri cikin cup ɗin who send you ,tamkar dai gejin cin abincin wani gardin shima haka na ɗaura da bread da butter ,warwas nayi akan kafet ɗin bedroom ɗin mu sanyin fanka na hurani saboda yanda zufa ke tsatsafo mun a duk gaɓɓan jikina to Ni abu ba kaɗanba ƙatuwa.

Anty Nusaiba raɓeni tazoyi gamida liƙe hanci ta ɗauko riga da wandon fakistan milk da maroon ta saka ɗauko mayafin kayan ta taho gaban mirror tana rolling ,pillow nayi da hannuna ina kallonta har ta gama shiryawa kana nace “To sai ina isashiyar kanta ,fita zakiyi da sassafen nan iyayenki na barci? To kina saka ƙafa kika fita a kunnen dady dama kin riƙa kin zama riƙaƙƙiyar kuɓewa anje an kaiki Sudan kin iskance ” ɗaga hannu tayi ta make bakina

“Ke nice kike zagi nifa yanki ne” wani ihu na ƙwalla da ya tsorata Iyayenmu aiko sai gasu a guje “Lafiya ?”
“Mum…dady Anty Nusaiba Bata sona nace zan bita inda zata wai bazata daniba wai Ni ƙazamace bla…bla”

Juyowa mamana tayi ta kalli Nusaiba “wai ke me yasa bakida hali keda yar uwan taki ma ?” Shiru kawai ya Nusaiba tayi ta girgiza kai batace komai ba inaji anata mata faɗa haka kuma duk sai naji ta bani tausayi ,ƙarshe akace in shirya in bita sai sannan tace “Dady plz kace tayi wanka da brush to ,don wallahi a haka zatace zata bini kuma wari takeyi “

Harara na banka mata “Kin haɗiya reza a gicciye nice zanyi wanka a sanyin nan ? Bazata saɓuba”

“To mumy kinjiko ,nikuma in har da ƙazanta zata bini ina likita gwara in haƙura na fasa siyan cosmetics ɗin”

Yafitoni Dadyna yayi ,nakuwa shagwargwaɓe naje na haye cinyarsa ,shafa kalbar kitsona da tsagon suka haɗe saboda daɗewa ba kitso yayi yina mun magana cikin rarrashi

“Mamana ai kinajin yawo ko?” Ɗaga masa kai nayi da sauri
“To maza nadyn dady aje ayi wanka kar Anty ta fasa fitan”
“Kambu to sai kuma dady ka ƙyaleta ? Ai dole taje ko?” Murmushi yayi “ƙwarai kuwa tunda kema wankan zakiyi “
“Eh nadaiji ” hakana dai na tafi naje na rage datti wankan 2mns badon na fita ba ,ina fitowa naga iyayen namu sun fita sai ita dake zaune akan stool ta ɗaura jakarta dazata fita dashi akan cinya tana chart da wayarta ,tsaki naja naje na ɗauko Vaseline ɗina na shashafa fuskana caɗai kamar ɗanwake ,itadai sai bina da ido take ,saida naje na hangame kwabana ina lalubo wasu cukurkuɗaɗɗun kaya marasa guga kafin ta maza tace “Ga kayan na ciro maki my love”

Kallon banza na wulla mata “Anty banason saka wandon jeans ƙaiƙayi yikemun baki ganina ƙatuwace ?”

“Amma inkinsa yina maki kyau don kina fina kyau Ni bakiga kayan larabawa na sakaba,Ni basamun kyau” caɓe baki nayi “Kumafa haka ne kece ya Nusaiba akwai rama ga muni,to zuciya ba hali,Ni ban insa ” itadai murmushi tayi wai itace nadiya take kiranta da mummuna yarinyar da a Sudan sajewa takeyi da en ƙasan har kalan skin ɗinsu ɗaya wai itace mummuna? Wayo tai mun ta lallaɓani nasan marasa squeezing tamun rolling nan kuwa cikina yayi tuiii a waje ga manyan ass ,inda zaka gane ba wata babba bace shine Banda cikan ƙirji kuma fuskata kwaɓa² yike irin na shafwaɓaɓɓun yara ,ipad ɗina na ɗauka mara sim don Banda mai kirana na saka cambas irin na zuwa ball na fito na wuce car na tsaya ina jiranta

Ɗakin mumy ta shiga amsar makullin mota,suna liƙe suna hira kamar wasu Romeo ba masu manyan en mata ba,A sannan ne take bata haƙuri tana ƙara nuna mata niɗin dai eruwarta ne tana haƙuri dani

“Shikenan mumy amma dai in kun sama lokaci a kaita Psychiatric hospital taga likitan ƙwalwa ke likitane kinsan alamomin hauka ,kuma Nady ta ɗebi kaso da dama ” babanmu dake gefene ya kwashe da dariya “Lallai Nusaiba kin tsorata da lamarin er uwarki “


A mota ƙira’ar sudais tasa har suka isa Suhash shopping mall ,nan tayi parking suka fito ,tana tafe tana mata nasiha kar tayi tsiya da kowa ,aiko bata rufe bakiba wata mata tazo wucewa da ɗan ta riƙe da ice cream yaron bai wuce 7 years ba ,cikin rashin kula irin na yaro ya bangaji cikinta ya kuwa sheƙa mata ice cream a takalmi ,wayyo Ji kake ɗauuuuuuuu ta yanka ma yaron mari mai tsananin zafi a take yaron ya gigice ,ya fasa ihu ,aiko uwarsa ta juyo da sauri ta rungume ɗan ta tana kallon nadiya dake hura hanci tana masifa ya ɓata mata takalmi

“Haba en mata bakisan yaro ba”

“Yaci kazan ubansa shi yaron ,nima ai yarinyar ce ,kece dai baki bawa ɗanki tarbiyya ba”

“Shikenan keda iyayenki suka baki tarbiyya cigaba da faɗa da ƙaramin yaro …” Da sauri ta katse ta

“Ahhhh karki zageni wallahi Ni pepper ne yanzu zan kwaɓe muyi dambe in kinfi ƙarfina shikenan sai in kuka ina share hawaye”

Nusaiba takai ta dawo ta rasa yanda zatayi haƙuri take ba matar in matar nikuma tana mun faɗa,kawai sai na fashe mata da kuka wai tafison bare a kaina .

Wani Chubby guy ne ya tako a hankali cikin ƙwalisarsa ya matso inda muke so yike ya janyeni ta baya amma ina na aza anty Nusaiba ce ba zato ba sakan masa one blow a baki da sauri ya riƙe bakinsa yina nanata “Ah….ah….ah” ruɗewa Nusaiba ta ƙarayi ,dasauri takai gwuiwonta ƙasa “Man Plz sorry she’s young ” zare hannunsa yayi a saman bakinsa

Ya sa hannu ya ɗago ta ,maye gurbin mamakinsa yayi da wani irin lafiyayyen murmushi mai tsadan gaske “Karki damu ƙuruciya ke damunta jiba da ta nausheni ma ta gudu” waigawa tayi nankuwa taga na ɓace ,can ta hangoni wajen kayan chocolate na maƙale Ina leƙe

Girgiza kai tayi cikin takaici ,shikuwa sai dariya yike yi “kayi haƙuri kaji “

“Ƙanwatace ain’t vex? Muje ki zaɓi abinda zaki siya joooor “

Ɗan murmushine ya ƙwace ma Nusaiba ,lallai guy ɗin is so friendly tasata yayi suka wuce wajen turaruka

Nikuwa taune yatsa nayi “shegiya Anty Nusaiba anga kyakyawar namiji sai rawar kai akeyi ,to baidaice yina sonta ba kuma bari inje masu”

09065990265
Wxp only plz????????
[6/20, 11:26] ????????????: GIDAN DAƊI
(Duniya)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button