GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

GIDAN DADI COMPLETE NOVEL

Oum Aphnan✍️

Free page
007

Tun daga parking lot nake ƙwalla mata kira har cikin gida ,da ƙarfi na hankaɗa ƙofar na shiga tana kwance ta ƙanƙame pillow tana shan love ,a tsorace ta miƙe zaune tana maida gashin kanta daya wargaje saboda kwanciya
“Nadiya why are you banging the door like that,are you mad “
Dafe kaina nayi na koma na jingina a jikin ƙofa ina lalubo video ɗin da na ma ya Hisham “Come and see ,come nowww?!” Ƙur ta mun da ido bata da niyyar miƙewa
“Come on ! Kizo ki gani mana”
“Hello!” Ta ɗan kira attention ɗina ɗagowa nayi na kalleta “Who is your senior sister,who age who?” Turo baki nayi ,da har nayi zuciya zan tafi ganin interest ɗina ne yasa na dawo nabita kan gadon na miƙa mata “watch your naked evil” a tsorace ta karɓa Saidai wani ƙara ta fashe dashi da sauri na rufe mata baki da hannuna “Malamansu momy is around ,she may definitely need to dig the true ,to shawara ya rage naki me kike gani zaki fasa auransa ne ko zaki auri mayaudari ɗan iska mai rungume mata a titi”

Kwantawa tayi akan pillow wasu kyawawan hawaye suna layi a kuncinta “Dole zan fasa auren Hisham ,Nagode ƙanwata”
Rungumeta nayi “Da kyau” na bata amsa na wuce bathroom Ina bouncing kamar wacce tayi abun arziƙi


32hours Later

Muna zaune a ɗakinmu Ni ina game a laptop ɗina Anty Nusaiba tana chating a wayarta fuskarta a murtuke ,Hisham ya kira wayarta yafi sau ba Adadi taƙi ɗagawa,a hankali momy ta Turo ƙofar ɗakin ,da sallamata saidai ba wanda ya amsa ta
Kewayowa gefen bed ɗin tayi daidai an sake kiran wayarta ,direct Anty Nusaiba ta nufa ta miƙa ma wayar “Amshi Hisham yace yina kiran wayarki bako ɗagawa”
Da muryarta adashe kamar wacce tayi kuka tace “ok mom kije zan kira shi da wayana”
“Oh no pick up” a hankali ta ɗauki wayar ,batayi magana ba na ɗan lokaci Saida yace salamu Alaikum ,kafin tace “hello”
Ta bangaren Hisham ya zarce da cewa “Sweetheart how are you I’ve been wondering what happen to my blossom…” Da sauri ta katsesa da
“Oh sorry I will call you later” kafin yayi wani magana ta datse kiran ta mika ma momyn wayan

Karɓa tayi tana jujjuyawa tana saka abubuwa a ranta “me ke damunki?” A takaice ta amsa da ba komai
“Ok me ya hanaki magana da Hisham”
“Haba momy ki ƙyaleta mana may be she is not in the mood tayi magana ne” na karɓe maganar da sauri ina wani tattare gira

“Yi mun shiru dake nake magana ehen,ko kece mouthpiece ɗin ta”
Danna wayar nayi na nuna mata wayana “to kalli nan” wani shock tayi amma da sauri tayi maintaining kanta
“Oh really? Nusaiba zo muje” ta faɗa tana kamo hannunta
“Momy go where now,kuyi maganar anan mana “
Kallona tayi ta bankaɗa mun harara “kece big informant banso kiji,na gaji da rabata da masoyanta da kikeyi wannan bazaki yi nasara ba…” Shiru tayi saboda Dady da ya Turo ƙofar
“Ohoo haɗe mun kai zakuyi? So kuke ku nuna mun nine kaɗai namiji a gidan ,zan ƙaro wata ,gaskiya zan ƙaro mai tayani hira”
Dukda momy tasan wasa yike bai hanata tankawa ba “Come on,daga naxo ganin lafiyarsu …kawai ma dai muje” ta tasa ƙeyarsa suka fice ,Ni kam dariya na saki abuna rai fes ,itakuwa Anty Nusaiba taɓe fuska tayi ta juya ta kwanta ,ta rarumo wayarta ,a hankali na miƙe tsaye ,ina nanata mata “karki yarda ki ɗauki wayarsa kinji ,You guys should break up!”


Muna zaune a dinning muna lunch mu ukune ,still Kiran wayar Anty Nusaiba ya damemu ,duk dauriyar momy saida ta magantu
“Haba pick nah” na saka fork Ina ƙaƙarin gutsuran kaza kenan nayi saurin cewa “momy its ya Hisham fa,Anty karki ɗauka”
Muzurai momy ta mun kana ta sanyaya muryarta “Nusaiba ɗauki wayar mana” a zafafe na cusa naman a bakina na soma magana yagau yagau “Yawwa ɗauka ki ci masa You locked the relationship with him ,ya aiko a amsan masa kayan baikonsa….”
Harara momy ta kwasa mun
“Nadiya Inaso inga young man ɗin da zai zo auranki” caɓe baki nayi na magantu ciki ² “Aiko ba rana bare wata”
“Me kika ce?” Da ƙarfi nai magana ina ɗan bubbuga kai “Ahhh bance komai ba ” kallon banza tayi mun “ohooo bakomai ?” Gyada mata kai nayi “gwara ya zama bakoman “ta faɗa ranta a ɗan ɓace ,saboda taji zafin mugun alkaba’in da nikewa kaina “momy sorry it joke”
“Gwara ya zama ba’an Nadiya “
Daidai nan ya sake Kiran wayar
“Oya ɗauka in ga gari”
Dakan dinning table ɗin nayi a zafafe nace “yawwa ɗauka ki faɗa masa bazaki iya ba kuma, wedding is cancelled ,baki yi kawai period”
“Kinajina bazan ce maki lallae ki auresa dole ba ,kawai abunda nikeso shine ki ɗauki wayarsa ki faɗa masa me ya faru let him confess,in kinason sa then you move,in baki sonsa daga nan mu manya sai mu shigo maganar”
“Momy idan har yina sonta bazai je yina rungumar wata akan titi ba ,harda cewa wai bashida masoyiya”
“Aushhh,Nadiya jeki ɗauko mun wayata a bedroom” zaro Ido nayi “momyyyyy” na ja sunanta kamar zan kuka “Nadiya you heard me, so , go”,ta fada cikin tsawa²
tashi nayi na tura kujeran baya na fara stepping zuwa ɗakinta da sauri saboda in dawo kafin ya kira
“Ok my love me kika yanke a ranki uhum”
“Momy zan ɗauka wayarsa kamar yanda kikace saidai abunda nikeso ki gane shine ,bazan faɗa masa maganar nan ba ,saboda koda na gaya masa dole kare kansa zaiyi ya kuma cemun sorry ,to idan hakan ne why not in yafe masan kafin ya zama jacks da musayan yamu tunda dole za’a dawo one circle ne?”

“Kenan You truely forgive him,or…?”
“Gaskiya momy banda option din da ya wuce hakan ne shiyasa “
“Ina sonki da hakurin ki ,unlike your sister …” A hankali ta ɗauki wayar ta mika ma Nusaiban “ok talk to him kamar ko yaushe don’t let evil to break this good…”
“Momy banga wayanki ba” na fadi da karfi tun kafin in ƙaraso ,dasauri na dawo na zauna
“Ok go and check my car”
Kwaɓa² nayi kamar zanyi kuka
“Ah ah momy taya zaki bar wayarki a cikin mota”
“Nadiya wuce na ce” diddirke ƙafa na shigayi haka dole na fita ,har na kulle ƙofa na buɗe na leƙo da kaina
“Kar ki ɗauki wayar nan fa Anty” tsaki sukaja suka cigaba da shirya maganarsu irin na masu hankali
Yina kira ina shigowa ,a hankali Nusaiba ta dauki wayar zata shafa screen ɗin na ƙwalla ihu ,wanda ya tsorata su duka
“Anty no zakiyi kuskure ,uhm uhm I’m warning You”
Dafe kai momy tayi “Nadiya what again? Ina wayar nawa yake “
“Momy mukullin motan nazo amsa” ɗauka tayi ta miƙa mun
Kawai saiga ƙwalla a kuncina “mumuuu na gaji ƙafana zafi,wallahi aikena kuke kuna mun wayo kuma na gane”
“Oh haka ne? To tunda har tunaninki ya baki haka ai MashaAllah ko banza mun samu cigaba ,wuce ki bani waje ” ,sannan ta juyo ta kalli Nusaiba a karo na barkatai “Nusaiba bari in baki wani hint da baki sani ba ,99.9% na maza Are cheat ,let’s say budurwansa ne ,so what is your business tunda ke ya zaɓa out of those girls ya zaɓeki a matsayin abokiyar rayuwarsa dukda kyawunsa,dukiyarsa and his prestige ,let’s this be enough to you durling ,kiyi haƙuri plz Ni mamanki na baki hakuri don Allah”
“No mah I will…ki bar bani haƙuri I will” da sauri ta ɗauki wayar “hello”
“Babe what’s wrong ?”
“Sorry wayata na jefa lungu sai yanzu naga Ni” sassanyar ajiyar numfashi yayi
“Oh har kin tayar mun da hankali kwana da wuni,naji ba daɗi gani ,ina jirgi on my way to China da kin ganni a gidanku saidai i don wanna miss the flight babe ,anya kin damu dani kuwa,anya kina kewana”
“I’m missing you love ,kawai dai ina tare da mama yanzu will talk later?” Shikennan nima za mu tashi zamuyi chat ok?”
“Yes safe trip durling”
“Ok thanks” ya kashe wayar a hankali ya kwanta a bayan seat din jirgin ,yina manne da wayar a ƙirjinsa a hankali wani sanyi ke shigarsa ,nan danan yaji wasai an ɗauke masa damuwarsa ,sanarwar kowa ya saka belt ɗin jirgin a shirya jirgi zata tashi shi ya dawo dashi tunaninsa ,da sauri ya miƙe a inda yike saboda yina wajen en regular passengers ne ,shikuma late yazo airport ɗin bai booking ba don haka na en vips ya biya wanda yafi tsada ,yafi secure kuma .
A nutse ya ɗauki jakar bayansa ya goya ya shige can ,tsayawa yayi yina kallon nature d’in wajen,Govenor ne da mukararrabansa ,sai wani calm guy cikin track suit da tuntumemen cambas ,ji yayi yafi masa sauki ya zauna kusada saurayi kamarshi,ba cikin wanda zasu damesa da hayaniyar siyasa ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button