MUTUM DA DUNIYARSA 53 – 54

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[53➖54]_*
…………A matuƙar kasalance ya zauna a bakin gadon idonsa akan ƙirjinta, hakan
data fahimtane yasata yinƙasa da kai da ƙoƙarin gyara ƙaramin gyalen data ɗaura akanta ya rufe mata ƙirji sosai.
Sassanyan murmushi yayi yana lumshe ifanunsa da sauke ajiyar zuciya kafin yakuma buɗewa a kanta yana miƙewa tsaye, hanyar fita ya nufa, saida yaje ƙofar sanan yajuyo yana kallonta “Idan kingama abinda kike, Kisameni a ɗakina”.
Kamar zata fasa ihu tace, ”to”.
Bai kuma cewa komaiba ya fice abinsa.
Shiru jiddah tayi a tsaye, zuciyarta sai saƙawa da kwancewa take, tana mamakin miyasa yace taje can? Tunda tazo gidan bata taɓa shiga ɗakinsaba, kullum shike zuwa ya sameta, taja wasu mintuna kafin ta matsa gaban madubi ta ɗauki turare ta fesa da wasu sirrikan ƙamshi na humra, sannan ta saka hijjab har ƙasa ta fita.
Gidan tsitt babu wata hayaniya gashi babu nepa, rabonsu da wutarma tunda safe, saida aka tada gen ɗin masallaci, kuma suna kammala karatu aka kashe, koda Aliyu ma yashigo gidan har an kashe.
Taja wasu adadin mintuna a bakin ƙofar falon kafin ta tura ta shiga da sallama. Babu kowa a falon, hasalima dunɗum yake da duhu, fitilar wayarta ta haska falon dashi, komai yamata ƙyau gwargwadon iko, kujeru da labuloli duk kalar ruwan siminti, sai baƙi kaɗan, ƙofa ɗaya dake rak a falon ta nufa, ta ɗora hannunta saman handle ɗin, harzata murɗa saikuma ta fasa tayi tsaye tamkar mai fargabar shiga ɗakin jarabawa.
Saida taja kusan mintuna biyu kafin ta murɗa ƙofar ta buɗe, da sallama ta shigo a bakinta kanta a ƙasa.
Aliyu dake zaune a bakin gado laptop a gabansa yana dannawa ya ɗago ido yana kallonta da amsa mata, kafin ya ɗauki kofin shayinsa yakai baki.
“Kosai na taso nayi tarbane Amarya?”.
Kai Jiddah ta girgiza tana cigaba da takowa ciki da faɗin, “A’a nagode”.
Murmushi yayi yacigaba da abinda yakeyi, “Bismillah ki zauna to”.
Takowa tayi zuwa bakin gadon ɗan nesa dashi ta zauna.
Kofin shayin ya miƙa mata. ta girgiza masa kai alamar a’a.
Baice mata komaiba ya cigaba da akinsa, itama saita jawo littafin *KITABUT TAUHID* daya ajiye tana dubawa.
Kusan mintuna huɗu suna a haka kafin ya ɗago yana kallonta, ”Afuwa gimbiya inaɗan rage saƙwannine, kozaki tayani?”.
Murmushi tayi tana riƙe baki, “Wai inani ina wannan saƙwannin? Aina manyane”.
Ɗan murmusawa yay kawai yana cigaba da aikinsa, “Hakadai kikace, amma ai kuma bana wasa baneba Jiddatulkhair. Shin Kin haddace littafin nan ne?”.
Ɗagowa tai taɗan kallesa ta janye idonta “A’a ba dukaba, mun fara babu daɗewa na daina zuwa makarantar”.
Sosai ya kalleta yace, “miyasa?”.
da ƙyar ta iya fisgo maganar tana inda-inda, tunda yataɓa cemata bayason ya tuna ta taɓa aure, ”lo lokacin wancan au..ren ne”.
“Humyim” kawai yace yamaida kansa.
Kasa daurewa tai saida taɗan kallesa saboda yanda ya bata amsar, ganin yacigaba da aikinsa itama saita cigaba da duba littafin.
Minti kusan ashirin yanata aikinsa, kafin ya janye laptop ɗin gefe yana faɗin “Alhamdulilahi, hajiyata basai kicemin na huta hakananba”.
Cikin rufe fuska Jiddah tace, “Haba saikace wani aiki?”.
“Aikine mana tunda nabar Matata ita kaɗai” yay maganar yana Matsowa jikinta.
Jitai duk kasala ta saukar mata, taɗan matse jikinta waje ɗaya tana sinne kanta.
Sumbatar hannunta yay dake riƙe a nasa, “kinyi alwalar barci?”.
“A’a” ta faɗa tana girgiza masa kai.
Batareda yace komaiba ya fara ƙoƙarin cire mata hijjabin, batayi jayayyaba ta barsa ya cire, kayan barcinta wando da riga kalar pink suka bayyana, sihirtaccen ƙamshin da take zubawa ya shaƙa yana lumshe idonsa, kansa ya ɗaura bisa kafaɗarta, gashin gemunsa dake taɓata ya saka tsigar jikinta tashi, hancinsa yakai jikin wuyanta yana shinshina, tuni jikinta yakuma yin sanyi ƙalau.
Ganin yana neman zurmawa tace, “Zanje nayi alwalan to”.
A kasalance ya sauke numfashi kafin ya matsa daga jikinta yana nuna mata hanya alamar taje tayi.
Sum-sum tamkar munafuka ta wuce bayi ɗauro alwalar barci. Bayinma yamata ƙyau, gashi a tsaftace babu wani ƙazanta, kodayake dama batai tunanin samunta daga gareshiba, dan ko farcen malam ka kalla kaɗai ya isa shaida maka shimai matuƙar tsaftane.
Taɗan jima sannan ta fito, yanda ta barshi haka tazo ta iskeshi yana duba littafin data ajiye. Ta gefen ido yake kallonta harta zo ta ɗayan gefen ta kwanta can ƙarshen gadon.
Ruwa takeson zuwa tasha, amma kallon ƙurullar da yake mata duk saita daburce. Shima lura da hakanne ya sakashi ɗauke idonsa daga kanta yana faɗin, “Ko kina buƙatar wani abune?”.
“Uhm zan sha ruwa ne”
jug ɗin Ruwan dake ajiye a dirowar gefen gadon ya tsiyayo ya miƙo mata. Zaune ta tashi ta karɓa tanasha, shikuma ya miƙe yanufi bayi.
Lokacin daya fito Jiddah hartayi addu’ar barci tai luf.
Baice mata komaiba ya shinfiɗa abin sallah domin yin shafa’i da wutiri kamar yanda ya saba. Duk abinda yake Jiddah na kallonsa, amma taƙiyin koda ƙwaƙwƙwaran motsi dazai tabbatar da hakan.
Yaɗan jima yana addu’a kafin ya miƙe yay shirin barci, tunda Jiddah taga zai cire jallabiyar jikinsa saita rumtse idonta, shi baimasan tanayiba, duk zatonsa kotayi barcine mashi.
Harya hawo gadon ya kwanta da kashe fitilar tana jinsa, hannu yasa ya lalubota yana jawota jikinsa, “Haba Kairunnisaa, waya ce miki haka mata da miji ke kwanciya?”.
Shiru tai takasa koda tari, saida taji yana hura mata iska a kunne ne tashiga sauke numfashi da ƙyar, hakanne yasakashi fahimtar idonta biyu dama, sai kawai ya canja zuwa wani salon daban……….????⛹♀
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Baƙi dai duk sunyi ƙaura, hatta dasu balu duk sun tafi, sai umma taji gidan duk babu daɗi, yayinda kewar jiddah ta dawo musu sabuwa fil a zuciya.
Koda Uncle yahya yazo ɗazunma da safe haka yaytajin babu daɗi da baiga jiddah ba. Yazone sun tattauna akan batun sauran kuɗin sadakin Jiddah daya rage a wajensa, shinema har yake sanar mata Abba yaje nemansa ranar, amma sai ya cema yaron yace yaje Adamawa, kuma yana gida babu inda yaje.
Murmushi Umma tayi tana faɗa masa suma dayazo nan bai zaunaba ya fice abinsa.
“To ALLAH ya ƙyauta, insha ALLAH idan ya huce zanje nabashi haƙuri, dan nasan da gaske ba a ƙyauta masaba ɗin, amma bamuda wata mafitane sai wannan ɗin”.
Murmushi kawai Umma tayi, dan tasan ko maƙiyi bazaice yahya baiyiba, mutumin kirkine dayasan haƙƙin ɗan adam da darajar zuminci. a wannan zamanin irinsu ƙalilanne a cikin al’umma.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su Ashir harsun kama hanyar gidan Abba sai yayansu ya dakatar dasu bayan zuciyarsa tamasa wani tunani.
Canja hanya yayi zuwa police station.
Bala yace, “Wai ina kuma zaka kaimune yaya?”.
“Station zamuje Bala, ɗaukar hukunci a hannunmu bai daceba, ai dama da jiƙaƙƙiyar kuɗi a tsakani, kunga daganan saimu wuce kotu”.
A fusace Ashir yace, “Amma yaya kabarmu muɗan sassafashi mana, kaga daga yanzu baya sake munafincin zuga waniba ai”.
“cooldown ƙanina, abinda zamuyi masa yanzu saiyafi duka zafi ai”.
Shiru duk sukayi badan sun soba, a station duk abinda ya dace sun yishi, atake akaje kamo Abba.
Abba yana kasuwa hankalinsa kwance, dan sosai yakejin daɗi ganin a kwana ukunan babu sammacin da Alhaji garba yace za’a kawo masa na kotu, shi kansa Alhaji garban ma baya zuwa kasuwa gaba ɗaya…….
Yana tsaka da wannan tunaninne ƴan sanda suka iso shagon bisa kwatancen dasu Ashir sukai musu.
Sosai gaban Abba ya faɗi, amma saiya fuske yana mazurai, ƴan sanda dai bayani sukai masa na buƙatar ganinsa a ofishinsu. Kamar Abba zai musa saikuma ya fasa ganin idanun mutane yadawo kansa gaba ɗaya.