Lu’u Lu’u 10

*10*

 

Ko da ta saka wayar sai bata ga tayi alamar ta d’auka ba, ta jima zaune tana son ta ga wayar ta nuna mata tana d’aukar cajin, Deeyam da suke zaune kan gado suna jiran 12:00 ta yi ne tace mata “Dan Allah ki rabu da wayar nan ki zo, mu ji me kike shiryawa?”

Cike da damuwa tace “Wayar nan ce ta k’i d’auka fa.”

Sabrine ce tace “Ki kunnata mana ta yiwu ta d’auka.”

Jinjina kai tayi ta danna wayar dan kunnawa, Deeyam ce tace “E lallai, irin wannan damuwa haka, da alama fa akwai k’amshin wani abu tsakaninki da malam Umad.”

Ganin wayar ta kama kuma lallai ta fara d’aukar cajin yasa ta mik’ewa ta nufosu tana tab’e baki tace “Kinji wani banzan tunani kuma, malamin na wa?”

Tsaki tayi ta zauna tana fad’in “Ba zan iya had’a hanya da mai saka uniform ba, dama dai shi d’in joker ne ko kuma mai aikin gidan zoo, zai fi armashi.”

Bushewa sukayi da dariya sai Deeyam da tace “Ke kuma ki rasa wanda kike son yin rayuwa da shi sai wanda bai kai komai ba.”

Sabrine ce tace “Ba ma wannan ba, me yasa take son auren irin mutumin nan?”

Zuba mata ido sukayi, numfashi ta sauke sannan ta kalkesu dukansu tana murmushi tace “Saboda ina so na rayuwa kusa da dabbobi, ina son ganinsu a kewaye da ni.”

Gyara zama tayi tace “Ba wannan ba, yanzu me kuka shirya min ne na ga kuna ta b’oyo d’azu har da korata a d’akin nan.”

Da sauri dukansu suka ce “Ba komai.”

Da kallon tuhuma ta bisu tace “Kun tabbata?”

“E.” Suka fad’a a tare, tab’e baki tayi ta mik’e ta nufi gadonta ta kwanta tana fad’in “Da 12:00 tayi ku tasheni.”

“Ba ma sai kin fad’a ba.” Cewar Deeyam, dan suna son bata mamaki kamar yanda ita ma take basu idan irin wannan ranar ta zo musu, Ayam k’awa ce da kowa zai yi fatan samu, zata tsaya maka idan buk’atar hakan ta tashi, idan kana da kad’aicin yan uwa ita ta kan maye maka wannan gurbin, idan kuma maraici kake fama da shi zata mantar da kai shi, duk abinda take da tana baka ba tare d tunanin yawanshi ko darajarshi ba, haka kuma zata iya tare maka duk bala’in dake neman tunkaroka iya k’arfinta, kamar dai yanda tayi a kan Sabrine tsakaninta da Zafreen.

*12:57* ta d’an fara juya kan ta tana motsawa kamar zata farka, sam mafarkin da take yi bata jin dad’inshi, yatsina fuska take yi duk da a cikin bacci take, a can k’asan mak’oshi cikin bacci take fad’in “Ku daina, ku daina azabtar da ita, ku daina.”

12:00 a daidai kunnenta suka taru su uku suka d’aga murya wajen fad’in “Barka da zagayowar ranar haihuwa.”

A mugun zabure ta tashi zaune da k’arfi tana zazzaro ido a tsorace, Deeyam ce tace “Ke mu ne fa.”

Kallonta tayi kamar bak’uwar hallita a hankali ta fara saisaita nutsuwarta, shafa kan ta tayi ta sauke ajiyar zuciya tace “Oh, thanks.”

Wani k’aton cake suka aje mata gabanta suka fara tafawa suna mata wak’ar murnar k’ara shekara, bushe wutar tayi sannan ta yanka cake d’in, a bkin Deeyam ta fara sakawa sannan ta saka a bakin Sabrine da d’ai k’awar ta su, dukansu ma yankawa sukayi suka saka mata a baki sannan suka dangwala suka shafa mata a fuska, daga haka suka haukace inda suka dinga d’ibar cake din suna shafawa junansu suna ta dariya suna tsalle akan gadon cikin nishad’i, dan iya daren garesu kawai da zasu iya yin wannan farin cikin, idan ba haka ba babu lokaci zuwa wayewar garin.

Wata babbar kwalba Deeyam ta d’auko ta lemu mai tsadar gaske sai ka ce barasa, saida ta girgizashi sannan ta bud’e duk ya pallatsar musu a jiki, kowa kofin tangaran ya mik’a ta zuba mi shi, suna tsaka da sha suka ji vibration na waya, a tare suka juya hakan yasa Sabrine cewa “Tun d’azu fa ake kiran wayar nan.”

Deeyam yace tace “Watak’ila kiran ujila ne, ko wani abu mai mahimmanci.”

Lek’a wayar Ayam tayi ta ga lambar an rubuta sunan *Ffrind* (aboki) da yaren Gallois, d’auke kanta tayi tace “Ku manta kawai, abokinsa ne.”

Mantawar sukayi kamar yanda ta ce, saidai tuni aka sake kiran hakan ya katse musu shagalinsu, Deeyam ce tace “Ayam me zai hana ki kashe wayar nan, idan ba haka fa ba zamu huta ba.”

D’an k’aramin tsaki tayi tace “Haba, malam ka kira sau d’aya ka ji ba’a d’aga ba kayi na biyu har da na uku, me zai hana ka shafawa mutane lafiya?”

Sabrine ce tayi saurin fad’in “A’a fa Deeyam, ni ina ga da d’agawa mukayi ko kuma dai ta je ta kai masa wayar, ki tuna fa akwai ujila a rayuwa, muka sani matarshi ce ko kuma mahaifiya ko mahaifi.”

Cike da gatse Ayam tace “Ke ki je mana tunda ke ce matarsa d’in.”

Murmushi tayi tace “Babu inda zan je in fad’a miki, ke zaki je tunda ke ya bawa wayarsa.”

Deeyam ma cewa tayi “Gaskiya ne, ki je ki kai masa to.”

Tsaki tayi ta kalli jikinta sai kuma ta kallesu, sauka tayi daga kan gadon ta d’auki wayar ta nufi hanyar fita, Deeyam ce tace “Akwai sanyi fa a waje, ki saka rigar sanyi mana.”

“An k’i.”Ta fad’a kai tsaye tana ficewa a d’akin, da kallo suka bi d’an k’ugunta da baya juyawa saidai dake tana da k’ira ba zaka gane komai ba.

Likitar dake daf da k’ofar shigowa ma’ana sai ka bi ta kan ta zaka wuce tana ganin Ayam ta murje idonta daga baccin dake son d’aukarta daga zaune, ba alamar girmamawa tace “Ke ina zaki je yanzu a daren nan?”

Kallonta Ayam tayi tace “Zan je gurin yallab’ai ne.”

“Me zaki je yi?” Ta fad’a a gatsalce, gyara tsayuwa tayi tace “Dama kina zaune a nan ne dan tambayar abinda zai shigar da kowa nan?”

Mik’ewa tayi tsaye cikin hassala tace “Ke bana son shashanci banza, ya zama dole na san me zai shigar da ke ciki, idan ba haka ba kuma ki koma.”

Matsowa tayi ta tsaya gabanta cikin gadara ta rumgume hannayenta, zuba mata ido tayi kamar zata had’iyeta tace “Kika ce saidai na koma?”

Haka kawai tsigar jikinta ta tashi ta ji ta kasa jurar kallonta, samun kan ta tayi da rusuna kan ta tace “Kinyi sa’a yau bana jin bala’i, da…”

Kasa k’arasawa tayi sai kawai ta kalli k’irjin Ayam tace “Shiga kawai.”

Sama da k’asa Ayam ta galla mata harara ta wuce, tana shiga zaune ta sameshi yana kurb’an coffee a farin kofin tangaran.

Bud’a k’ofar da tayi ce ta ja hankalinshi zuwa kan ta, yanda ya so yi mata kallo d’aya sai abun ya ci tura ya kuma gagara, bai d’auke idonshi daga kan samb’ala samb’alan cinyoyinta ba wanda suke a cikin fari kuma gajeran wando iya cinyoyinta, haka ma rigarta fara ce mai siraran hannaye, kan ta kuma yanzu babu komai a kai face launin gashinta mai kalar maroon da d’an ratsin yellow yellow.

Gabanshi ta tsaya cike da shak’iyanci sakamakon lura da kallon da yake mata tace “Wato na maka kyau ko? Saboda ka ganni a hakane? Ai dama ni d’in kyakyawa ce.”

Cikin jin kunya da takaicin kan shi ya duk’ar da kai yana fad’in “Me ya kawoki kuma? Ko dai kin gagara bacci ne a dalili na?”

Yatsina fuska tayi tace “Tabb’! Akan me ni kuwa zaka dameni?”

Ziiii! D’in da wayarsa dake hannunta tayi yasa ta mik’o masa tace “Uhum ka gani, wannan abokin na ka ne ya addabi mutane, a gakiya mutumin nan da ina da wani iko a hannu na dana sa an d’aure min shi, haba mutum sai takurar tsiya.”

Duk tana maganar shi kuma yana kallon bakinta ne, saida ta dasa aya ya karb’i wayar ya duba sunan, kallonta yayi yace” Nagode to zaki iya tafiya, amma ki sani zan tuna miki wata rana.”

Da mamaki tace” Me zaka tuna min?”

Girgiza kai yayi alamar ba komai, sannan ya lumshe mata ido ya bud’e alamar tafi, baki ta bud’e da matsanancin mamaki tace” Kai! Ni zaka kora da ido? Na rantse babu inda zan je sai ka min magana da baki, kaji ka kamar wani sarkin gaba d’aya k’asar Texanda.”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button