Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 45

Mamuhgee 45_*
Tana Isa bangarenta ta zube Palo tareda fasa ihun dataketa riqewa tun daga can,

Wayyo Allah na shiga uku Ina neman lalacewa Ni Na’ima,
Duk Wanda ya Shiga tsakanina da Turaki Allah ya bayyanarmun dashi na shiga tsakaninsa da nasa farin cikin da kwanciyar hankali….

Kururuwar ihun datake saki tana tsinewa duk macen data taba ko kallon Turaki harda uwarsa data haifesa tsine Mata takeyi tana rusa ihu zuciyarta da kirjinta Kamar zasu babbake da wutar dakeci aciki…

Siddika lafewa tayi a kicin taqi fitowa Dan ko ruwan zafi zata iya konata dasu idan tana wannan masifar tata komai fasawa take tana haukarta Dan Haka tunda tasan halinta ta daina tsayawa idan al’amarin yazo
Dan Haka ko yanzu tana jinta tana dure duren masifarta cikin tashin hankali Amma ta lafe taqi fitowa.

Duk da tana Mai aikin Ms Na’iman Kuma take yarinya akan Ms Na’ima tanada tabbacin wataran Ms Na’iman idan Bata kashe wani ba akan masifar kishi, zata kashe kanta to,
Idan Kuma duk hakan Bai faruba to zata haukace.

Ganin abin na Ms Na’ima ba qarewa zaiyiba ta fidda wayarta takira Haj Zinat ta fada Mata abin dayake faruwa ta kashe wayarta tana ajewa gefe ta nufi fridge tana cewa”

Yau ranar Jin dadina tunda batada kwanciyar hankalin yimun fada Bara na girka abinda nakeso naci abuna hankali kwance.

***Haj Zinat cikin quluwa da lamarin Na’ima da haukarta ta dauki wayarta tafara Kiran Na’iman Amma Bata dagawa,
Tsoki ta saki tareda jefar da wayar Kan gadonta tana cewa”

Na’ima haukarki tafara yawa wlh muna buqatan komawa ganin likitan qwaqwalwanki tun kafin Turaki yagama gano kinada matsalar hankali,
Yanzu da Daren Nan bazan iya zuwa gidanki ba sbd dare yayi Kuma Turakin na gari ba’a Shiga gidan idan karfe bakwai ta wuce matuqar ba Yan gidaba,
Indama baya garine sun Saba take dokar sbd securities na ragewa idan bayanan,
Amma yanzu Yana gari ubanwa zai Bari tashiga gidan da wannan lokacin¿

Allah yasa dai haukarki ta tsaya iya bangarenki kafin nasamu safiya tayi nazo karta budemun aiki Turaki ya gano batada cikakkiyar lafiyar qwaqwalwa mun shiga uku Dan kuwa take zai gano duk wani abun da Na’iman keyi kusan itace take dorata akai.

Ms Na’ima kuwa tun tanada karfin iya tashin hankalin ita kadai har qarfinta yaqare ta zube kwance qasan dakinta tana Jin kamar ta cinnawa gidan wuta kowa ya mutu har ita…

***Washe gari tun qarfe 6 na safe ta kwadawa zinat Kira batareda ta damu da lokacinba,

Dayake itama da ita ta kwana cikin ranta ba wani baccin arziki tayiba Dan Haka Kai tsaye ta daga Kiran tana cewa”

Thank God nasamu kin dawo hayyacinki,
Na’ima Ina fatan bakiyi abunda zai Bata Mana komaiba da janyo Mana matsala?

Bata amsa tambayar Zinat din ba tafara koro Mata bayanin abinda ya faru jiyan ta qara da cewa”

Zinat wlh saina tafi tunda ya nuna bayason zuwan nawa na tabbatarda yasan idan naje zansan sirrin dayake boyewa shida Waccar tsohuwar.,
Wlh Zinat idan ban illata ko waceceba qwaqwalwata bazata dawo daidaiba….

Can you imagine Ni Turaki yake cewa idan naje karna Isa ko kofar gidansa……

Wait wait”” Haj Zinat tafada tana tashi zaune daga kwancen datake cikin wani tunanin daya shigeta tana kasa yarda da hakan tace”

Idan yace ko gidansa karki Isa kenan ba tafiyar takice matsalarba zuwa gidan nasane¿

Idan hakan ne kuwa to wlh kila bayan barowarki akwai wata a gidan kokuma Laylah Dake gidan tasan wani abun bayason ki koma ta sanar Miki…

Shiru Na’ima tayi sbd yanzu Bata Gane komai Bayan taganta a jirgin komawa, idan ta Isa koma menene ayi sauran tunanin acan…

Kira Laylah ki tambayeta komai gameda gidan kiji idan wani Abu yafaru Bayan barowarki sbd itama bazata yadda acucekiba.

Cikin yanayi na kosawa tace”

Zinat me Laylan zata iya fadamin ko bincikamun wadda sanyin jikinta kawai ya Isa yasa na isa qasar Bata Gama sanin me gidanma yake cikiba bare wajensa,
Zinat Naga Kamar kin daina Gabe baqin cikina dakike maganar tsayawa ayi magana da Laylah….

Cikin gundura Haj Zinat ta katseta da cewa”

Na’ima meyasa kanki yafi na kowa tashewa ne Ana ce Miki ga abinda Zakiyi kina cewa aa,
Idan Kika tafi kin manta abinda yace ne?
Gidansa yace karkije,
Idan Kika tafi a yanda yakeda wata a zuciyarsa yanzu wlh Kika take dokarsa igiyarki daya data rage sakinta zaiyi kila Kinga shikenan kowama saiya huta,
Mama Baraka da bakya kaunar komawa gurinta saiki Koma can Dole Dan ayanda kasuwanci yake rawar Nan yanzu anata samun asara tako Ina wlh bazaki wafta kudi acikiba ki siya gida ko kamawaba,.

Dan Haka idan Zaki nutsu ki nutsu mubi komai a daki daki
A hannu zamu Kama komai kafin mu lalata koman kuma.,

Yanzu kiyi hkr ki aje maganar tafiyar a gefe kizo Nan muyi magana a tsanake idan yasan wata baisan wata ba ai.

Ba Haka Na’ima tasoba Amma Kuma tasan yanda Zinat ke cewa ayin koyaushe itace Hanya Mai bullewarsu Dan Haka Dole tabar maganar tafiyar saidai Bata fasa fitaba tunda uwar safiyar ta fice daga gidan cikin motarta Mercedes Benz C-class da Bata cika hawaba ta fice gidan cikin wani Irin speed dayasa har securities din gidan Gane madam din na cikin bacin Rai.

Turaki dake zaune cikin sofa a dakinsa tun bayan Gama sallar asubarsa Yasan dama ba zataji maganarsa ba sbd idonta yagama rufewa da taje din…

Wayarsa Dake gefensa yakai hannu ya dauka a hankali tareda saka Kiran Numbern A Abdoul Dake qasan ta Laylah daya Gama waya da ita ya Danna kiransa cikin nutsuwa.

Cikin bacci A Abdoul yaji wayarsa na ringing ya Dan mirgina tareda Kai hannu inda wayar take ya daga yana duba Mai kiransa wannan lokacin..

Ganin sunan TURAKI akai yasashi sake Ajiyar zuciya Dan dama yasan bayan Turaki Babu Wanda zai Masa wannan Kiran yanzu
Dan Haka ya tashi zaune Yana wartsakewa daga bacci cikin girmamawa ya daga wayar Yana cewa”

Good morning TURAKI.

A gajarce ya amsa cikin nutsuwa ba hayaniya tareda cewa Kai tsaye”

Ayiwa Zainab komai na Shirin tafiya duk ko yayane inason ta baro Atlanta ta sauka Lagos zuwa jibi.

Yes Turaki Inshallah angama.

Kashe wayar yayi tareda maidata gefe ya ajiye Yana maida kansa ya jinginar jikin kujeran dayake zaune tareda rufe fararen idanuwansa dasuka kasa samun komai face ganin Laylah ta iso garesa cikin koshin lafiya Dan baisan iya abinda zai iya faruwa idan Na’ima ta Isa qasar ta taba lafiyarta Dana cikin jikinta.

Ms Na’ima ma data Isa gidan Haj Zinat kasa Shan Koda ruwa tayi sai data Kira Laylah Dake fama da kanta ta ringa jeho Mata tambayoyin dasuka sakata shiga fargaba da shakka saidai duka amsoshin data bawa momyn basu gamsar da itaba Dan Haka ta kashe wayarta tana cewa”

Dama nasan ba wani amfani ne da Laylan ba kikace sai ankirata gashinan na batawa kaina lokaci da Rai abanza.

Da qyar da dabara Haj Zinat tasaka Ms Na’ima Shan tea kafin ta banka Mata maganin qwaqwalwan datake akai aikuwa tana shansa ba jimawa baccin Dole ya dauketa ta zube a gadon Haj Zinat Dake cikin lafiyayyar bedroom dinta tana baccinda ba shiri.

Bata farka ba sai yamma wanda daman Haka maganin yake wani irin mugun bacci yake sanyata harsai qwaqwalwanta ya dawo Yana Dan aiki daidai,
Hakama da mutuwar jiki zatai kusan wuni biyu sbd bazata samu qarfin wani tashin hankalin ba shiyasa batason maganin idan tanajin masifarta Amma so da yawa Zinat ke yaudararta tabata gashi yanzu Bata iya wani dogon tashin hankali sai bayan kwana biyu kuma Dan Haka ta tattara Fahad babban Dan Haj Zinat din ya dawo da ita gida.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button