GURBIN IDONOVELSUncategorized

GURBIN IDO CHAPTER 2

Da sauri maimunatu ta karbi kayan hannunsa tana tayashi saukewa hade dayi masa sannu da zuwa,inna na daga tsaye tana zabga mata harara amma bata kulaa da lamarinta,don ba zata iya ganinsa da kayan bata karba masa ba

“Yaya mutum zai kwana da yunwa……ki debar mata cikin nawa mana” tuni ta cika dama tayi fam da yadda yake nuna kulawarsa akan maimunatun,uwa uba kuma ya buda ledar hannunsa ya bata bread cikin tsarabar da yayo

“Wallahi ba zata ci ba….koda abincinka ne kuwa”

“Ka barshi bappa,zanci wannan” maimunatu ta katsesu da sauri,saboda tasan muddin jayayyar taci gaba to la shakka a kanta abun zai qare,inna zata yi mata hukunci ne wanda ba zataji dadinsa ba,sannan babu abinda zai sanya innar ta sauya rantsuwarta,saboda ba wai tsoro ko shakkar bappan take ba,duk da tasanshi farin sani,yana sakar mata ne,saboda kasancewar maimunatu daga tsatsonta ta fito,shi yasa yake dage mata qafa,baya zaqewa cikin al’amarinsu da yawa

“Shikenan,balejam(mu kwana lpy)”

“jam” ta amsa tana juyawa da dan hanzarinta tabar wajen zuwa nasu dakin.

“Kiji tsoron Allah fulera,kiji tsoron randa Allah zai kamaki da haqqin marainiya” daga haka ya dauka ledarsa ya rab’eta ya wuce ciki,ta bishi da harara,sannan ta sauke idanunta tabi hanyar maimunatun ta wuce da hararar itama har zuwa qofar dakin nasu,sannan taja qwafa tana sakin labulen

“Tsoronka da zanji,rashin godiyar Allah ne yasa baka ganin qoqarina ai,banda ni ma waye zai riqeta?” Taci gaba da mita abinta,saidai ko daga kai bappa jauro baiyi ba bare ya kalleta,idan da sabo ya riga ya saba da halayyarta.

Saman shimfidarta ta koma ta zauna sannan ta bude ledar biredin,a hankali ta dinga yaga tana turawa,cikin ranta tana godewa Allah da ya turo bappa jauro,da haka zata kwana da tsohuwar yunwarta.

Yadda biredin ya fara mata go slow a wuya ya sanyaya bisa dole ta miqe cikin raunin da jikinta ya fara yi ta lalubi wani tsohon kofi nata ta tsiyaya ruwa a jallonsu dake dakin,ta sake komawa ta zauna,tana ci tana korawa da ruwan,kafin sannan tuni bacci yayi gaba da gaje,wadda maimunatu bata da tabbacin tayi sallar magariba bare isha’i.

Jahilci ya sanya gaje da wata ire irensu sam basu baiwa ibadarsu muhimmanci,duk da cewa akwai makarantar islamiyya guda daya tal,wadda anan ake koyarwa da kowa da kowa cikin rugar tasu,maza da mata yara da manya,cikin hobbansa da malaman ahlussunnah sukayi suka kawo musu malami bafulatani irinsu yake zaune dasu.yana koyar dasu,saidai ba kowa bane ya fahimci alfanun hakan ba bare har yace zaije,da yawa wani kallo sukewa makarantar,dai daikunsu ke zuwa.

Tana da.matuqar buri da kuma sha’awar kasancewarta daliba a makarantar,saidai inama taga lokacin da zai zama rara(saura) a gareta tsahon wuni guda,wanda bata bautar komai,da gar zatayi.amfani dashi ta ziyarci makarantar da sunan daukan karatu,kullum aiki take,babu dare ba rana,ba asabar babu lahadi,kamar yadda babu alhamis babu kuma juma’a,koda makara tar bokonsu dake da dan karen nisa,koda yuashe maimunatu mafarkin zuwanta take,bare wannan dake kurkusa dasu,gaje nada dama mai yawa da zata iya zuwa makarantar,saidai sam ita ba wannan bane a gabanta ba,bata taba ma kwatanta zuwa din ba.

Dai dai lokacin da gari ya sake daukan shuru bayan daukewar mamakon ruwan saman…..dai dai lokacin da wata iska me sanyi ke kadawa,a wannan lokacin zazzabi ya fara saukar mata,yana murqushe duk wata gaba dake da sauram qwari a jikinta,takurewa tayi sosai waje guda,tana jin yadda zazzabin ke ratsawa ta qashi da tsokar jikinta,a hankali yana saukar mata da sanyi da wani irin radadi,saita cure waje daya,numfashinta na fita da qyar tana kokawa dashi.

Duk da cewa wannan din ba baqon yanayi bane tare da ita,amma shi ciwo ba’a taba sabo dashi,ta jima cikin wannan yanayin tana kokawa da numfashinta,tana hangen kanta tsakanin rayuwa da mutuwa kafin ubangiji cikin tausayinsa rahamarsa da kuma jin qansa ta fara samun sassauci,numfashinta ya fara komawa dai dai,saidai qirjinta dake riqe da kuma ciwon dake ratsawa cikin jikinta yana sandarta a hankali,har wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita.


“Maimunatu!…..maimunatu…..” Can tsakiyar baccinta….sannan cikin tsakiyar kwanyarta taji ana ambatar sunanta,shurin da aka kaima gefan cikinta shi ya qarasa tabbatar mata da cewa ba cikin duniyar mafarki take ba,abinda ya sanyata zumbur ta miqe daga kwanciyarta,sai kuma ta sanya hannayenta guda biyu ta dafe kanta tana furta

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” saboda wani nauyi da taji kan nata yayi mata,baya ga dan karen ciwon da yake mata

“Ke yafi kamata a jawa innalillahi,akalluɗo(muguwa)” inna dake tsaye bisa kanta ta fada cikin fushi,bata ko motsa ba bare tace wani abu,kanta na qas tana jin yadda zuciyarta ke suya,jikinta ke tsami da kuma ciwo saboda ciwon dake jikinta

“Ananata haala maimunatu?(bakyajin magana maimunatu ko)da kika zo kika kwanta kina barshi,waye zai miki tatsar nonon,waye zai fita da dabbobin?,ko uwarki ce zatazo tayimin?” Idanunta ta runtse,tana jin xafi cikin zuciyarta fiye da kowanne irin zafi,koda wasa bata qaunar inna ta dinga sanyo mahaifiyarta cikin kowanne irin sha’ani ko laifi da zata aikata mata,ta kuma tabbatar ci gaba da shurunta xai bawa innar dama taci gaba da zagin nata ne,don haka cikin murya mai cike da rauni tace

“Minyauɗo inna(bani da lafiya inna)” idanu innar ta qanqance tana dubanta

“Wannan keta shafa,yahudillo durgul,wurtawa(zo ki tafi kiwo,fito)” ta fada a tsawace kamar zata finciko maimunatun.

     Bata da sauran zabin da ya wuce ta miqe din kamar yadda inna fa buqata,duk kuwa da yadda takejin jikinta,ta dafa a hankali ta miqe tsaye,a sanda innar ke mata wani kallo

“Nikam kin zamemin alaqaqai masifa” saita juya ta fita zuwa waje tana zazzaga masifarta,idan lokacin ka shigo gidan zaka tsammaci wani mummunan abu maimuntun ta aikatawa innar.

      Kayanta data saqale.jiya ta miqa hannu cikin juriya ta cirosu,hawaye me dumi ya subuce mata,ta zame zanin jikinta,ta fara shirya kanta a cikinsu,babu batun wanka bare akai ga abinci,dama bata lafiyarta take ba

“Wurtawa fa maimaunatu” ta tsinkayo muryar innar tana fada cikin salo na azalzala

“Mihosh shawai filkul(dan kwali zan dauko)” maimunatun ta fada tana duqawa a hankali ta dauki dan yalolon dan kwalinta ta dora kan sassalkan gashinta dake cure waje daya cikin kitson doka(bijaɗe a fulatance),sannan ta matsa zuwa bakin kofa tana laluben wuffajen ta(asalin rufaffen takalmin da fulani ke amfani dashi wajen kiwo.

Ba zata iya duqawa ta sakasu yadda ta saba ba,dole sai datakai qasa ta zauna dirshan sannan ta samu damar sanyasu ga qafafuwanta,ta miqe tana riqe da sandarta tana takowa zuwa tsakar gidan nasu iska na kadata.

Kamar kullum babu kowa a tsakar gidan,daga inna dake can rumfar da suke girki,sai gaje dake zaune tana cin tuwo,tuwon da take da tabbacin da safen akayishi,amma bata da darajar da za’a bata ta sanyawa cikinta,ko don darajar bautar da zata fita yi musu.

Ganin tuwon ya tuna mata da guntun biredinta na jiya,ta sanya hannu ta dafe qaramar jakar da take daureta a qugunta taji tudunsa tabbacin yana nan,sanna ya fara takawa zuwa ma’adanar dabbobin,muggan kalaman inna sunayi mata rakiya,har zuwa sanda ta kammala kunce na kuncewa,ta kuma fara kadasu suka dauki hanya.

❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????

ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA

Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button