GURBIN IDO CHAPTER 3
GURBIN IDO
Huguma
Free page 03
Duk wani taku da takeyi tana yinsa ne da taimakon sandar dake riqe a hannunta,a yau madadin sandar ta zame mata ta saita dabbobin da take jan ragamarsu,sai ta zame mata mataimakiya wajen sanya diga diganta zuwa qasa.
A yau din da baki ta.dinga saitasu tana basu umarni,duk da yadda magana ke mata wuya ainun,duk kalma daya idan xata fitar sai taji kamar kanta zai tsage,sun dan dauki lokaci kafin su isa inda suke qyale dabbobin,kowacce ta ni’imtu ta kums amfana daga rahamar ubangijinmu.
Tana isa kamar koda yaushe,mabanbantan makiyaya dake wajen kowa ya fara qoqarin tattare dabbobinsa don gudun afkawa ko cakuduwa da nata dabbobin,ba yaune farau ba,nan da anjima kadan ma tana iya ganin wajen babu kowa sai ita daya da nata dabbobin,abune data saba da ganinsa,canfi ne da suka riga suka dasawa ransu,wanda batasan ranar da zai goge ba,hakanan babu me cire musu shi sai mahaliccinmu.
A yau dinma bata damu ba kamar kowanne lokaci,bayan ta tabbatar da sun iso inda ya dace,saita fara zame jikinta daga cikinsu,tana wara manya kuma fararen idanunta da kalarsu ta jirkita saboda zafin ciwo dana zazzabi,tana neman inuwar da zata dace da ita.
Babbar bishiyar mangwaro ce,mai yawam sanyi da kuma inuwa,wadda bata da wani tsaho.mai.yawa amma sai yawan ‘ya’ya,daga nan inda bishiyar take basu da nisa da inda zata hangi dabbobinta,hakanan ba nisa da inda zata gangara dasu susha ruwa da zarar lokacin hakan yayi.
A hankali ta zame malafare(hular kaba da suke amfani da ita” ta ajjiye a wajen,duk da hular ba nauyi gareta ba,amma sai takejin kamar ta dora wani dutse saman kanta,ta zare jakar dake qugunta itama ta ajjiyeta,da zata iya kwanciya zatayi,amma tana jin nauyin sallar da batayi ba takai mata ko ina,don haka ta juya zuwa sashen da ruwa ke gudana,ta daura alwala ta dawo ta tada salla saman dankwalin kanta data cire ga yane kanta da mayafin da akoda yaushe bata rabo da yafashi,duk kuwa da cewa baqon abune cikin al’adarsu,zata iya cewa ma kaf fadin rugar ita daya ce cikin matasan yara masu shakaru irin nata dake amfani dashi.
“Maimunatu!…..maimunatu” da sauri ta daga kanta daga durquson da tayi masa,tana ware idanunta cikin matuqar kaduwa da razana,murya mafi muni da razanarwa a wajenta…..muryar da mamallakin muryar abubuwane da tunda take a rayuwarta bata taba jin abinda ta tsana cikin duniyarta sama dasu ba
“Yaushe ya dawo?” Ta jefawa kanta tambayar tana wurga idanunta don tantance daga wanne bangare yake dosota.
Daga can nesa ta hangeshi,tsabar kauri da qarfin muryarne ya sanya ta dinga jinta kusa da ita kamar yana gab da ya cimmata,qasa tayi sosai don kada ya hangota,sannan ta miqe a hankali,ta tattare dankwali hula da jakarta waje daya ga wurga saman bishiyar da take zaune qasanta,karo na farko da tayi ala wadai da rashin iya koyan hawa bishiya irin nata,saita saita mayafinta ta lullube jikinta da kyau,sannan ta zagaya ta bayan bishiyar ta lafe sosai a jikinta,ta yadda zata iya hangoshi,zuciyarta na wani buguwa ɗik ɗik,tana cike da fata da kuma addu’ar rashin samun sa’ar ganinta.
Dube dube da waige waige ya shiga yi,yana kuma sake qwala mata kira iya qarfinsa,fuskarsa a firgice da alama ya zaqu da son ganin nata,bai kuma tsammaci rashin samunta a wajen ba,dube dube yaci gaba dayi,yana sake kiran sunan nata dai,har zuwa sanda ya sare,jikinsa da zuciyarsa kuma suka gaya masa bata a kusa
“Kayyasa” ya fada da kaushin murya,yana kaiwa bishiyar dake kusa dashi karta da wani kakkaifan abu dake hannunsa,da sauri ta zame kadan saboda gudun samuwar ciwo a jikinta,saura kadan kartawar da yayi ta hada da tsintsiyar hannunta,ta dauke numfashinta cak sanda yake sake takowa da baya,sai kuma ya dura wata ashariya,yasa giyaa zuwa gaba ya taka ya fara barin wajen.
Bin bayansa tayi da kallo farincikin boye masan da tayi yana saukar mata,kwata kwata kuma ko sau daya bata taba yiwa buderi kallon mutum mai hankali ba,hasalima tsoro yake bata ainun,buderi kenan,baqin bafulatani na usul,wanda ke ciie da wasu irin baudaddun halaye na wauta jahilci da hauka,irin nau’in haukan da jahilcin ne ke haifar dashi,zuciyarta cike take da mamakin me yasa shi din baya gudunta kamar yadda sauran samarin qauyen ke gaza rabarta bare su furta mata kalmar so?,me yasa shi bai gujeta ba?,ta jima tana yiwa kanta wadan nan tambayoyin.
Sai data tabbatar da cewa ya yiwa wajen nisa sannan ta fito,zuwa sannan zazzabin jikinta yayi wata irin saukar da babu shiri,sai sauran dumi,ciwon kai mai tsanani saboda razana da bayyanar buderi da kuma ciwon jikin da har yanzu tana jinsa shima,ta tako a hankali ta dawo ainihin wajen da ta fara zama da farko,tana tattare jikinta waje daya.
A nutse yake takowa yana kuma sake nazarin rigar tasu,yanayin yadda ko yaushe take bunqasa da tarin dabbobi da albarkar kiwo kusan ya zarce na kowacce ruga dake maqwabtaka dasu,ni’imar dake wajen ta banbamta daya sauran yankuna,hakan shi ya sanya yanayin wajen da rayuwarsu t bambanta data sauran sassa.
Tun daga qasan ruhinsa zuwa saman fuskarsa cike take da wani irin nishadi,tun daga daren jiya da yayi gamo da ita…..har kawo warhaka da yake takowa cikin rugar tasu daga doguwar tafiyar da yayi zuwa cikin ainihin garinsu,tunaninta,siffa da kuma kamanninta basu bace daga idanunsa ba,duk sanda siffarta zata wulqa cikin idanu da tunaninsa sai ya samu kansa da subucewar murmushi,wani lokaci hatta da haqoransa sukan bayyana,nuni da girman nishadin da zuciyar tasa take ciki.
Goye yake da baqar jaka,yana sanye da baqin wandon jeans,sai asalin rigar fulani dake jikinsa mai gajeran hannu,daga ciki kuma t.shirt ya sanya mai dogon hannu saboda hana bayyanuwar dantsen hannunsa,saman kansa ma hular fulanince,sai qafarsa dake sanye da wani rufaffen baqin takalmi na danqo.
Ba qaramin qara masa kyau da haiba kayan sukayi ba,sun kima fidda ainihin salsalarsa na bafullacen usul,duk da kana dubansa zakasan cewa ya dan banbamta da sauran matasan fulani irinsa dake rayuwa cikin rugar,akwai wani banbanci na daban da kuma haske tattare dashi.
Hakanan kawai zuciyarshi ta bashi yabi ta gefan ruwan,yana da tabbacin hakan zai qara masa nishadi,bayi wata wata ba yabi shawarar zuciyarsa,yana tafe yana kallon yadda dabbobin dake baibaye da gefannin kogin keta kaima cikinsu ruwan.
Da kallo yaci gaba da.binsu yana sake takawa izuwa gaba,babban abinda ke sake hanashi sakewa da garin kenan,had’akar ruwan sha a gurbi guda tsakanin dabbobi da kuma al’ummar yankin,daya daga cikin burin da yake dashi idan har Allah ya cika masa burinsa,banbance ruwan shan dabbobi dana mutanensa.
Dauke idanunsa yaso yi,saidai daga gefe guda dab da rafin wani abu ya dauki hankalinsa,ya rage sassarfar da yake a tafiya,ya sake qura mata idanu saboda tabbatar da hasashensa,shin itace koba ita bace,bashi da sauran zabi.bayan ya tabbatar da ita dince illa bin umarnin zuciyarsa dake azalzalarsa yakai gareta,ko zai rabauta da daddadan sautin nan da take magana dashi a koda yaushe.
“Assalamu alaikum” ta tsinkayi sallama daga gefanta,bata tsorata ba duk da bataji takun tafiya ba darajar sallamar da aka gabatar mata,sai ta cira kanta dake boye tsakanin qafafuwanta.