GURBIN IDO
GURBIN IDO 17
“Babu wanda zai miki allura kinji” ta qarashe maganar tana jan yarinyar cikin jikinta sosai ta rungumeta,sai ta narke itama tana sassauta kukan gami da sakin ajiyar zuciya me qarfi,da alama abinda take buqata dama kenan,tunanin maimunatu yadan cilla wani waje jin yadda yarinyar tayi luf a jikinta tana sauke ajiyar zuciya,kamar tasan fuskar yarinyar a wayoyin al’ummar gidan,kamar tana ganin fuskarta a wajensu.
Tsakiyar tunanin da take aka daga labulen akayi sallama wadda ke cakude da sauti na dariya a tausashe,ta daga kanta a hakali tana amsa sallamar,idanunsu suka sarqe waje guda dame sallamar.