GURBIN IDO

GURBIN IDO 66-70

10:10 PM] Safiyyatulkiram: 66

Johannesburg
kemfton park,69 oleander avenue

( Eagle rock executive guest house)

Tun daga parking lot na guest house din maimunatu tasan wajen na dabanne,jabir da ja’afar suna gaba su kuma suna biye dasu,a hankali fatiman ke mata hira

“Zan samu na huta sosai gaskiya,wajen yamin kyua fiye da yadda sweetheart ya gayamin,anty moon,qilan fa ba zaki sake ganina ba sai ranar da zamu tafi” ta fada tana ‘yar dariya,murmushi maimunatun ta sakar mata ba tare da tace mata komai ba,don ita nata lissafin daban yake,batasan ya zaman zai kaya na kwanakin da zasuyi ita da miskilallen mutum irin ja’afar ba,sai kuma ta sake sakin murmushi da kwanyarta ta tuna mata da fuskarsa,ya yake iya rayuwa haka kuma yake jin dadinta?,kullum fuska a dinke?,zata iya rantsuwa bata taba ganin dariyarsa ba sai miskilin murmushin nan nasa,shima sanadiyyar zuwan amna ne.

         A main entrance su jabir din suka tsaya,da alama sallama suke don yana karbar muqullin private entrance da kowanne apartment ke dashi,waiwayowa jabir yayi ya dagawa fatimansa hannu,sai ta dubi maimunatu

“Anty moon,Allah ya qaddara saduwarmu” murmushin ta bita itama dashi tana amsa mata,sannan ta taka zuwa gaba a hankali inda ja’afar din ke tsaye,ya fara gaba shima a hankali tabi bayansa.

“Bismillah” ya sake cewa bayan ya bude dakin,yadan dakata kadan yana karanto addu’o’in shiga sabin muhallin da ba naka ba,sannan ya sake yin bismillah ya shiga tabi bayansa.

Dakin ya tsaya yana qarewa kallo,na meye jabir zai kama musu daki irin haka,maganan gaskiya ya fara gajiya da kwanciya saman sofa,sauqin abun ma large bed ne dai dai kwanciyan mutum biyu,sai bed sofa.

Knocking akayi,sai ya bude,ma’aikatan gidan ne janye da luggage dinsa,ya karba ya maida qofan ya rufe,ya jawota tsakiyan dakin ya aje a gefe guda.

Fidda abubuwansa masu amfani ya fitar daga cikin jakar,sannan ya rage kayan jikinsa ya shige toilet.

Tana zaune daga kan bed sofa din tana qarewa dakin kallo,kadan kadan sanyin garin yana dan busata,da alama ba’a jima da dauke ruwa a garin ba,don ya dauki sanyi sosai,qofar toilet din taji an taba,ya fito daure da tattausar hoodie bathrobe,sai tayi qas da kanta,batason tayi wani motsi bare yace tayi ba dai dai ba zaiyi punishing dinta da kalar abinda ba zata iya dauka ba,tana jinsa ya gama shirinsa tsaf,qamshin turarensa ya gauraye dakin,qafafunsa ya zurawa wasu boots da suka dace da shigarsa sannan ya miqe yana dan dubanta kafin ya kauda kai

“Kiyi waya reception idan akwai abinda kike da buqata,za’a kawo dinner”

“A dawo lafiya” ta fada a tausashe,sai ya lumshe idanu yana jin yadda muryar ta sauka masa a kunnuwansa,ya juya a hankali ya fice a dakin.

Yana fita din sai taji kamar an zare mata qaya,batajin zata iya wanka a yanzu,don a haka ma sanyin ya dameta,sunci abinci cikin jirgi don haka bata jin yunwa,sai kawai ta gyara kwanciyarta ta fidda wayarta,tana kunnawa taga free wi-fi na guest house din,babu passcode,don haka tayi connecting hankalinta kwance.

Duk yadda taso sakewa dole ta dauko electric duvet ta yafawa jikinta saboda yadda sanyin ke qaruwa,bata jima sosai ba bacci yayi awon gaba da ita saboda gajiyan zaman jirgi.

Bata farka ba sai bayan sallar magariba sosai a can,ta fahimci hakan ta agogon dake dakin da kuma agogon wayarta data maidashi na can saboda gudun kubcewar sallah,tana miqewa ta fahimci akwai room heater,sai ta kunnata,cikin lokaci qalilan sanyin ya ragu,gidan shuru duka ba dadi. Tana niyyar shiga toilet don ta watsa ruwa ko zataji qwarin jikinta akayi knocking aka kawo abinci.

Ajjiyeshi tayi tayi sallah,sannan ta ware wanda zata iya ci,tana ci tana duba lokaci,duk sai ta fara jin wani iri babu dadi,ina ya tafi?,ya kuma dade har haka bai dawo ba?.tun tana dubawa har ta haqura,ta kammala tayi sallar isha’i,ta cire kayan jikinta ta shiga toilet ta hada ruwa me zafi tayi wanka.

Duka jakan kayanta ta zauna ta hautsina,sai ta dafe kanta,da alama musayar jaka tayi,ta dauki wadda tace a tafi mata da ita ta bada wadda tayi niyyar tahowa nan din da ita,sai ta koma ta zauna kamar zatayi kuka tana bin kayan da idanu.

Duk ciki bata ga wata suturar arziqi da zata sanya ba,daga night gown din har sauran kayan sawa dake ciki,ta dan jima zaune tana tunanin mafita,babu…..itace amsar,don haka ta maida hannunta tana sake daga kayan ko za’a dace.

Da qyar ta tsamo wata a ciki,wadda a ganinta tafi kowacce tsarki,Two pieces ce in da top,wine color,ta cikin siririn hannu gareta kamar na vest silk and satin,iyakarta saman gwiwa,ta saman kuwa zallar net ne,long sleeve ce ita,ta kuma sauko har qauri,gaba daya zare daya ne ya riqe ta saman wanda dashi ta daure gaban rigar.

Gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta,iya kyau rigar tayi mata kyau fiye da kima,ita kanta taga hakan,saidai gaba daya babu sirri,kusan abinda ta rufe matan kadanne,sai tasa hannayenta tana jan top din zuwa qirjinta sosai,ko zata sake dan rufe mata wani abu,don gaba daya tudunsu ya fito sosai ta sama.

Dan qaramin tsaki taja ganin babu abinda zasu iya sake rufe mata,sai kawai ta yanke ta kammala duk abinda zatayi tayi hanzarin kwanciya kafin ya dawo,wannan yasa ta rage wutar dakin,tabar qwai daya,sai ta koma bandaki ta dauko hair drayer din data ganina ciki,saboda gashinta yadan jiqe sanda take wanka,batason kuma kwanciya da jiqaqqen kai.

Cikin gajiya jigata da kuma zazzabin da ya saukar masa ya turo qofar dakin a hankali,qarar hair drayer din ya hanata jin shigowarsa,uba uba kuma gaba daya ta sauke sumar tata zuwa gaban fuskarta,bata iya ganin komai sai gashin nata da yayi mata rumfa.

Cikin wata kasala fiye da wadda ya shigo da ita ya maida qofar ya rufe,idanuwansa a kanta,cikin wine color sleeping dress din da tayi masifar haskata,farin bayanta da fararen damtsenta ya fito ta cikin lace top din,hawan kalar jikin fatarta sai ya zama kamar wani ado na musamman,dumin dakin ya gauraye da qamshin hair mist dinta dake dai daita masa tunani a duk sanda ya shaqeshi,maimakon yaci gaba da shigowa sai ya kasa,gaba daya ya goye hannayensa a qirji,bayan ya taimakawa kansa wajen tsaiwa ta hanyar jingina da bangon dakin,yayin da idanuwansa suka ci gaba da sauka zuwa kowanne sashe na jikinta,daga bisani idanuwansa suka tuqe ga qugunta wanda yake daya daga cikin abubuwan dake daukan masa hankali.

Gaba daya ta kwashe gashin ta maidashi baya,tana hadeshi cikin dan mitsitsin robber band,tana cire drayer dinne taga kaman da mutum a dakin,a matuqar razane ya saki drayer din,ta kuma juya da sauri da niyyar neman mafaka ba tare daga gama tantance waye a tsaye ba.

Duk yadda yakejin kasala da mutuwar jiki taku uku ya kamota,da gaske ta tsorata sosai, saboda har yanzun dakin bashi da wadataccen haske,cikin wani irin coolness ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki,ya kuma matseta gam,sannan ya dora habarsa a tsakiyar kan nata,tattausan qanshin turaren gashin yana shigar masa hanci,gami da aike da wani saqo mai nauyi a qwaqwalwa gangar jiki da zuciyarsa,ya kuma tadda mood din da yake ciki ya fara motsa abun.

“Relax……relax,it’s me,ja’afar ne” ya fada da wata karyayyiyar murya,kaman ba muryar captain ja’afar ba,mai yawan zafi da karsashi.

Ajiyar zuciya ta saki tana jin wata nutsuwa na saukar mata,ta sauke ajiyar zuciya tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa,dumin dake jikinsa yana ratsa sassalkar rigar jikinta zuwa fatarta,duk da batasan temperature na jikinsa ba,amma zuciyarta ta bata zazzabi yake,dukkaninsu sukayi shuru kowanne bugun zuciyarsa na daduwa.

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button