Halimatus sadeeya

Nikuwa nace hm badai Malika ba
Yan gidan su umma kishiyoyinta ko tambayar malam basuyi ba inah umma take harkar gabansu sukeyi da gulmace gulmace antafi zubarwa da sadiya ciki yaran umma kuwa kallo Basu ishesuba bare da su Basu abinci Allah yasa yaran masu wayan sun iya girki dafa abincinsu sukeyi suci malam Shima na kula da yaransa yasan halin matansa Dan haka akai akai yake zuwa yaduba halin da suke ciki har Kiran umma yayi awaya yabawa yaran suka gaisa Dan suji Dadi Dan tin ranar da aka kwantar da sadiya ya koma gida yakarbo musu wayoyinsu yakawo musu
Yau malam gajiya yayi da halin matansa yaga Basu da hankali basusan zuruba Rai abace yatarasu atsakar gida yace habi tala lami asheku rashin hankalin naku da kishin naku har yakai haka ai ko makiyiyarkuce Khadija tinda kukaga batanan ita da sadiya kwatambayi inda take bare kunsan meyake faruwa sadiya Bata da lfy rangaranga aka fita da ita daga cikin gidannan Amma tindaga ranar da kukaga anfita da ita Baku tambayi inah sukeba Dan rashin imani Ni da bana gida aka fita da ita da nadawo baku fadaminba ko yaranta Baku tambayi inah mahaifiyarsu takeba Dan wulakanci da rashin hankali irin naku lanlai nayarda kiyaiyar da kuke yiwa Khadija da sadiya tayi yawa Kuma bakusan Taki ze zame musuba Nan gaba se kunyi danasani da Kuma Jin kunya meyawa Nan Gaba se kunji Kun muzanta agabansu bakusan ikwan Allah Babu abinda be iyaba zakuji mugun kunya Nan gaba
Dukansu hannu suka Dora aka suka hada Baki suka saki wani mahaukacin ihuu Kai kace mutuwa akai musu ga koke koke da suka cika gidan da shi
Tsawa malam yadaka musu yace du Wanda nadada Jin bakinta anan ta namin ihu da kuka agidan iyayanta zata kwana mutane kukeso ku taramin mahaukatan banza kawai kishi haukane ko kunyar yaranku bakwaji kuga yanda suka fito suna kallanku Wai ba se miji Yana da arziki da wadatar komai ba ake kishinsa ba mahaukata kawai Amma ku kishinku na haukane kullin fafutukar abinda Zan kawo muku kuci nake wataranma basamu nake ba haka ake hakura Amma du dahaka kishi kuke Kuma Kan Khadija da kuka zo kuka samu agidan ita tace me da kuka aure Mata miji ita batai kishi da kuba se kune zakuyi kishi da ita ko dayake bakishi kuke da itaba yanzu nagane bakin ciki kuke da ita wahalallu kawai Marasa aikin yi
Lami tace shikenan tamu tasamemu bayan zubar da ciki aka tafiyi Ashe har da asirce Mana miji arabamu da shi yanzu Dan Allah Akan Yar gwaldin matarka ka taramu kake Mana masifa tambayar me zamuyi tinda munsan Komai zubar da ciki aka tafi da bin bokaye adaurewa mutane Baki Dan Kar asiri yatonu Allah yakiyaye mu tambaya wlh can Kai da munafukar matarka da munafukar yarka ku tashafa Bata shafemuba wlh Babu inda zamu in dai anmutune mazo gaisuwa maganin zaman tare Shima Kar ace bakajeba wlh da dai naje duba matarka da yarta se dai mu rabu haka kawai Dan an mallakeka an asirceka anfi karfinka kazama Dan kallo anrufe maka Baki ko mgn baka iyawa kana gani ana aikata saban Allah
Malam besan lokacin da yadauke lami da mariba yace aniyarki ta biki Babu Wanda yataba abin kunya aziriarmu bare munafurci Kuma kome zamuyi da ku Kar wacci ta Kara sako matata da yarana ciki bare sadiya wlh tsaf Zan saki Mata akansu indai irin wannan mugayen kalaman zaku na furtawa akansu Allah yafiki gakinan babbar munafuka du abinda ko wancanku ke aikatawa na sani darajar yarana kukeci Amma kuci gaba karku fasa lokaci nazuwa Daman ba neman ko wance daga cikinku akeba kuje dubasu baaso inkara jin bakin wata acikinku na saki Mata ta koma gidansu wlh nagaji da mugun halinku Wai dukanku kunsan kuwa me yaranku ke ai,katawa awajan tallah da zance in samari sunzo wajansu Ina gudun ranar da alhakin sadiya ze tashi kamaku kunsan da cewa bakin cikinkune yai Mata yawa har ta kwanta asibiti wlh wlh wlh kunji na ramtse in har sadiya ta dawo gidannan kukaci gaba da Bata Mata Rai ku da yaranku wlh ko wancanku seta barmin gida Daman kandarace da raban Yara Yasa na aureku kujawa yaranku kunne tin wuri tinkan ta,dawo bazaku kashemin yariyata me ladabi da hakuri inaji inagani ku watse ku bani waje munafukai
Sumsum kowacce ta koma daki gwiwa asabule Babu bakin mgn Dan yau malam yabasu tsoro Basu taba zatan ze musu hakaba inda lami taci alwashin indai tana Raye se taga bayan Khadija se ta wulakanta sadiya se sadiya ta dauko abin kunyar da zuciyar iyayanta yabuga Dan bakin ciki inda habi tadau alwashin indai tana numfashi sadiya ita da aure har abada se dai taga anayi inda tala tadau nata alwashin Akan umma se tasa umma tabar gidan ita da malam har abada se sun rabu indai boka da malam na aiki aduniya Kuma du yaranta maza da suke aiki se ankorosu daga wajan aiki Kuma se sun kawowa uwarsu shege har cikin gida tinda akanta da yaranta malam yawulakantasu yau agaban yaransu du makota naji da masu zuwa siyan abinci
Banyarda wani ko wata yajuyamin liltafiba ko yacanja min ko yacire sunanaba du Wanda yayi ko tayi Allah ya,Isa tsakanina da ita ban yafeba liltafina bana kudi bane Kar wacce taci kudi ko yaci kudi da gumina du Wanda ko tasiyar min da liltafi ba da izininaba Allah ya,Isa ban yafeba novel Dina na masoyana ne Dan su nakeyi dasu nake alfahari har gobe????
New writer’s
Hakan Take
*Husba’ahfama* ????????????
*’Yar kwalliya* ????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????????
????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????????????
????????????
????????????
???????? *HALEEMATUS SADEEYA*????????
Written by *HUSBA’AHFAMA*
IG *officiall_husba’ahfama*
Facebook *Real Husba’ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba’ahfama*
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
9-10
Ko da malam yabar wajan matansa Rai abace se zancan zuci yake Yana ta Allah wadai da halin matansa wajan sanaarsa yatafi du Wanda yaganshi aranar yasan ransa abace yake
Malika tin safe tinda ta fita Bata dawoba tanacan wajan gantali akwai wata kawarta Yar duniya itace babbar kawarta Kuma itace me zigata Kuma Taki zaman aure kawar Tata yanzu karuwanci take aboye ko malika Bata saniba Amma kusan kawayansu abinda suke Kenna bin maza har da matan auran cikinsu ita wannan kawa Tata sunanta nusaiba ita Kuma nusaiba burinta aduniya taga ta kashewa Malika aure ta koma bin maza kamar yanda takeyi ko kuma tana auran shaawa ko auran kudi in sun samu abinda sukeso su,rabu da namiji burin nusaiba na biyu shine taga ta auri aliyu inhar tasamu aliyu azaman mijin aure to Babu ita ba fitowa tashiga kenan Dan dun duniya Babu namijin da taji ze iya gamsar da ita kamar aliyu ashinfida kullin da shaawar aliyu take kwana Kuma take tashi Kuma ita tana mugun Jin haushi da bakin ciki yanda malika tafisu samu da kwanciyar hankali Kuma mijinta yafi na kowa acikinsu da kudi da kyau da tsari da Kamala da du wani Abu da da namiji akeso atare da shi Dan haka nusaiba ta dau aniyar ziga malika ta ko wana Hali se ta rabata da aliyu ko ita Bata aure,Shiba nusaiba tin lokacin da malika tafara aiki abanki anan tahadu da nusaiba itama wajan take aiki har aka canja Mata wajan aiki Amma Basu rabuba suna tare kawancan nusaiba da malika se yazo dedai yatarar da Hali Abu dayane malika batayi neman maza Amma du wani Hali da malika take da shi nusaiba na dashi Dan haka kawancansu yazo Daya Kuma du duniya malika Bata da abokiyar shawara kamar nusaiba ko Yan uwanta na jini Bata gayawa matsalarta se dai nusaiba ita Kuma nusaiba ba shawarar arziki take bataba se ta tsiya du wasu kawayan malika na yarinta nusaiba tasa malika tarabu da su