Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Aliyu yadawo gida wajan karfe bakwai na dare agajiye ko da yashiga gidan kafin yashige nasa bangaran se da yaje bangaran malika be gantaba yaduba ko Ina yaga Bata dawoba abin yabashi mamaki afili yace wato me Hali baya fasa halinsa yanzu du nasihar da akayiwa yarinyarnan har dukanta mahaifinta yayi du batajiba Allah yakyauta to Allah kashiryi wannan baiwa taka Bari naga iya gudun ruwamta yaushe zata dawo Daman ba ki rana take awayaba taji yanake Nima nagaji na Dena kiranta in na ki,ratama cewa take Ina da munta Dan haka na Dena Allah yakyauta tahaka takeso adawo Mata da yaranta hannunta kuma abbah yayarda zaa dawo Mata da su yan,kwanaki kadan da su Amira sukayi ahannun ummi har sunyi kiba sunyi kyau sun samu kwanciyar hankali

Bandaki yashiga yawatsa ruwa yafito yashirya har yakwanta ciwan mararsa yatashi da ciwan ciki tin yanayi shi Daya har takai yakira Dr yagamasa halin da yake ciki

Dr yace kome yake yadaure yazo asibiti adubashi sosai abin yafi karfin gida Kuma aiki yayi,masa yawa Babu damar yabaro marasa lfy yataho dubashi

dakyar aliyu yasamu Yana dafa bango yafito falo yakira yaranshi awaya suzo su temaka Masa suna zuwa sukaga halin da uban gidansu ke ciki Babu Bata lokaci suka kaishi asibitin da aka kwantar da sadiya Dan Shima in Yana gari anan yake ganin Dr shi da iyalinsa du anan suke ganin likita saboda yazuba kwararrun likitoci a asibitin Kuma ba karamin kudi yake kashe musuba mutane na yaban asibitin sosai har daga wani asibitin turo mutane ake zuwa asibitin ranga ranga yaransa suka kawo aliyu daki na musamman aka ware akasa aliyu lokaci guda likitoci suka hadu akansa suna dubashi

Sun Dade akansa sosai Karin ruwa suka sa Masa akai Masa allura wani Dr ne yafito Yana tambayar yaran aliyu Ina matarsa

suka ce batanan tayi tafiyi

shuru Dr yayi yagirgiza Kai yace bawani nashi da ku kazo tare

sukace eh ko da matsalane Dr

yace aah yashige yatafi

Wajan karfe goma na dare alyu ya Fara dawowa dedai yace Akira Masa Dr shi gida ze tafi Dr nazuwa aliyu yace Zan tafi gida Dr kome ake ciki gobe kazo gida ka karasa min akwai dalilin da Yasa Zan tafi gida yanzu naji dedai ba abinda yake da muna tafiya zanyi

Dr yace gaskiya yallabai in muka barka katafi gida yanzu komai ze iya faruwa sedai in zakaje wajan madam ne kasauke matsalar da take da munka munyi mamaki kana da aure har da Yara matarka ba saban aure bane Kun Dade tare Amma shaawa ta tarar maka haka Amara Kuma kasan matsalarka kana da karfin bukatar mace akusa da Kai ko da yaushe in wannan matsalar taci Gaba da faruwa se anmaka aiki Kuma kana gaf da Dena haihuwa Gaba daya kakusa rasa Kwan haihuwarka Gaba Daya in matarka bata gamsar da Kai ka Kara aure Allah yahure maka za ka iya rike Mata har hudu gaskiya kadau mataki cikin gaggawa kafin lokaci yakure maka in ba hakaba da matsala babba Nan Gaba in ma madam tayi tafiyane Bata gari ka gaggauta sawa ta dawo da matsala yanzu muna so kayi hakuri ka kwana zuwa gobe ma sallameka

Aliyu Ido yaruntse yahau girgiza Kai azuciyarsa Yana takaicin abinda yake niyar faruwa da shi gashi Allah yadora Masa San Yara jiyayi hawaye na niyar zubo Masa yadaure Dan Kar Dr yagane halin da yake ciki in ma aure zeyi shi wa zema aura yatsani Mata baze Kara aureba gara yakarasa rayuwarsa ahaka tinda yayi beji dadiba bude jajayan idansa yayi Yana kalallan Dr yaja dogwan numfashi yace agaskiya gida Zan tafi yanzu Ina da abin yine naji shawarwarinka na gode gobe kazo gida ka karasa,min abinda yadace

Dr yace to yallabai bazan matsamaba bansan matsalar kaba agidan se goben Zan zo har da sauran magungunan naka yanzu cikin naka da marar sun Dena ciwo ko

Kai aliyu yadaga Masa yasauko daga Kan gadan yabude kofar yafito yaransa na ganinsa suka taho suna tamasa sannu Kai kawai yake daga musu hanyar inda da kin da aka kwantar da sadiya yanufa ze shiga kenan

Sega umma tataho da kula rike ahannunta tace alhaji sannu da zuwa yaaiki

Dakyar yabude Baki yace alhamdulillah yame jiki

Tace taji sauki gobe da safe Dr yace ze sallamemu shigo Mana yau idanta biyu kanwar taka itama nemanka take Tai maka godiya se sabani kuke du sanda zakazo tana bacci babantama haka Baku haduba har yau

Yace ba komai base na shigaba sauri nake tinda na ganki mun gaisa shikenan se direba yazo gobe kaiku gida kigai da baba kar yadamu base yamin godiyaba

Hannu Yasa a aljihu yaciro wasu kudi masu yawa Shima besan adadinsuba yabawa umma cewa tayi bazata karbaba dakyar yasata ta karba tana ta godiya

Tace bawan Allah yasunanka karkace na dameka gashi Kuma balanlai bane nakara ganinka

Yace sunana Ali umma se da safe yajuya yatafi

Tsayawa umma tayi tana kallan hanyar da yabi da mamaki da kudin da yabata rike ahannunta tace Ali ikwan Allah wlh ban sanshiba Allah kaiwa bawannan naka Albarka Allah kabiya Masa bukatarsa na alheri

tabude kofa tashiga tasamu sadiya zaune Kan sallaya ta idar da sallah tace sadiya Kinga yanzu alhaji bawan Allah yazo dubaki

Dasauri sadiya ta zubawa kofar shigowa Ido tace umma Yana inah Allah yayi Zan ganshi yau

Umma tace ai har mun gaisa yatafi yace sauri yake aimiki yajiki nace Masa kinasan Masa godiya yace base kin masaba agaisheki wlh Ni mutumin mamaki yake bani Kinga uban kudin da yabamu Ni tsorone ma yakamani naki karba se da yamatsamin sannan na karba nai tamasa godiya yace bayaso base na masaba Basu hadu da malam ba har yau Shima Wai sunansa Ali da na tambayeshi

Shuru sadiya tayi bahaka tasoba jitayi hawaye naniyar zubo Mata se taji Babu Dadi azuciyarta Dan taso taga Wanda yatemakawa rayuwarta ahankali tace Zan tamaka adduar alheri bawan Allah naso ganinka Allah be nufaba me temako inah San ganinka Ido rufe Allah be nufaba Ina Zan ganka Kuma shikenan Allah yaimaka Albarka bawan Allah me temako

Rai ba dada ta tashi taje ta kwanta zuciyarta ba Dadi du hirar da umma take Mata bajinta take sosaiba har bacci yadauketa

Alyu da yakoma gida masu gadi yatambaya ko malika ta dawo sukace Bata dawoba rabanta da gida tin safe da ta fita bece Komai,ba yashige cikin gida afalo yazauna Yana jiran ikwan Allah yaga yaushe zata dawo sha Daya na dare dedai har shada da rabi shuru Babu ita ba labarinta waya yadauka yakirata yaji wayarta na shiga har sau uku yakira Bata daukaba

can se ta turo Masa sako ta msm tace,,,,,,,, MALAM KARKA DAMENI KAJIKO KOWA YAI HARKAR GABANSA BARUWANKA DANI,,,,,,,,,,, se ta kashe wayar Gaba Daya

Abin yabawa aliyu haushi Kiran duniya wayarta akashe daki yatafi yaje yadauro alwala du da ba Dadi yakejiba yai nafila raka,a biyu Allah yaimasa maganin matsalolinshi yakwanta yai adduar bacci badadewa bacci yakwasheshi

Da safe wajan karfe Tara na safe Dr yasallami su sadiya likita yadada fadawa umma da malam sharadi Akan jikin sadiya sukace duka sun dauka zasu kiyaye Babu abinda ze Kuma faruwa yabasu magungunan da zata dinga Sha Kuma yace bayan sati biyu sudada dawowa agwada lfyarta aga komai yakoma dedai

Suna hada kayansu zasu fito su tafi Sega direba inji aliyu yacika alkawari yace yakaisu har gida umma da sadiya ba bakin mgn se mamaki da suke tayi malam ne yake ta godiya yace wannan bawan Allah shi baya gajiya wlh da yabarshi muna fitowa zamu samu abin Hawa yakaimu har gida

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button