Halimatus sadeeya

Direban yace ai wannan ba komai bane daga cikin temakwan yallabai ai kome yayi baa mamaki Dan shi wannan abinda yai muku ba komai bane awajanshi yanzu kafin Nan kafin kwana uku yamanta ma da abinda yai muku ko haduwa kukayi da shi se Kun Tina Masa ku su waye Kan yatinoku
Malam yace ikwan Allah kaga na Allah Allah yabiyashi
Dukansu suka amsa da ameeeen
Har kofar gida yakaisu yatsai da motar lokacin su habi sun fito leke kofar gida Yara na dambe suna musu mgn su Bari sukaga mota har mota tana daukan Ido ta tsaya akofar gidansu idan Yan unguwa se yakoma Kan motar ana jiran aga su waye zasu fito daga motar Suma su tala Baki suka saki suna jira suga me fitowa sukaga umma tafara fitowa se sadiya se malam salati su lami suka hau yi suna zare Ido da hanci har suna buge kawuna wajan zuro Kai su kallah sosai Yara akabawa tilin Kayan da suka dawo da shi du siyaiyar aliyu ne da yai musu agabansu Yara suke ta shigewa da shi suna kaiwa da kin umma sallama sukayi da direban suna tamasa godiya da sauri malam yataho yakama hannun sadiya umma ma takama Daya hannun sukasa sadiya atsakiya suna shiga cikin gida sunzo gaf da su habi
malam yadaka musu tsawa yace Wai ku Wana irin jahilcine yake damunku da auranku da yaranku kuke leke acikin unguwa wakukaga Yana haka du cikin unguwarnan ko kunga Yar uwarku Khadija nayi dahallah ku shige ciki ku bamu waje kunga mutane ba sannu da zuwa ba komai Kun saki Baki da hanci Kuna kallansu kurufe bakin Dan Allah Kar kuda yashiga Ni malam musu na kwasowa kaina
Umma tace baban sadiya mu shiga da ita ciki karta gaji kasan likita yace Kar tana wahala
Da rawar jiki malam yace to to mushige mu kaita sannu kinji sadiya na barki atsaye inawa marasa tinaninnan mgn
Cikin dakin umma suka nufa da sadiya inda su habi nabinsu abaya har cikin gida ba bakin mgn seda sukaga sun shige Babu alamar malam yayi zamanshi se Hira suke da yaran umma suna dariya
Abin yadada Bata musu Rai sosai tala talailayo wata uwar ashar ta Danna tace akwai Bala,I agidannanfa wlh wlh wlh da sake muzuba Ni da ku malam kaga abin duniya idanka yarufe anje anmallakeka andawo har da motar Wanda yai Mata cikin shegen ma aka dawo da ku aciki kenan malam yasan da cikin shegen da sadiya tayi Dan anrufe Masa Baki da kudi da Kuma layu da rubutu shine yakasa mgn kenan suna ma tare da alhajin da yai cikin kenan wato shine me motar nan ai Baku birgeniba tinda ba auranta zeyiba sedai akare ahaka har abada wlh Dole ma gobe na fita komai yawargaje se mun sake saban Shiri Wai matarnan da yaranta shedanune ko Yaya muyi tamusu aiki suna wargaza Mana kuga kudin da muka hada muka saci hanya shekaran jiya mukaje kauyen dakasoye wajan malam gobe da nisa yace Mana gidannan se yafi karfinsu in sun dawo malam ze musu korar Kare sadiya zata shiga duniya bazata dawoba se da yaran shegun da tahaifa har guda uku Khadija zata hadiyi zuciya ta mutu Yan uwan sadiya duka zasu lalace Amma bamuga alamar komai ba Wai me yeke faruwane har fa akwaryar tsafi malam gobe da nisa Yasa muka leka fuskokinsu dukansu mun gansu cikin wahala da kuncin rayuwa waiyo Ni tala wlh bazan hakuraba se burina yacika akan Khadija da yaranta wlh se yaran Khadija da ita kanta Khadija sun zama abin gudu aduniya se kowa yagujesu muzuba Ni daku shege kafasa
Lami tace ke wannan,ne yadameki tala kiga irin cin mutuncin da malam yai Mana agaban Yan unguwa da munafukar matarsa da sadiya me ladabin munafurci kiga jiyama irin cin mutuncin da yataramu yai Mana gaban yaranmu Akan bamu tambayi inda matarsa taje,ba saboda shi an asirceshi an rufe Masa Baki Ni tausayi ma yake bani bawan Allah du ta zagayeshi da asiri se mun tashi tsaye in ba hakaba muma mallakemu zatayi muzama bayinta ko ta koremu agidan tazama daga ita se yaranta se tsohuwar guzumar yarta sadiya wlh Nima se nayi abinda malam ze wulakanta Khadija agaban mutane da Yan unguwa se nasa malam yayi watsi da kayanta atiti in dai Ni nacika lami yanzu muka Fara wasan Ni da ke Khadija zamuga malamin waye yafi zafin aiki tsakanin Ni dake
Nikuwa nace hm lami allanta yafi naki malamin
Habi tace wannan Karan mun banbanta da juna ko wancanmu abinda ke ranta daban abinda yabata Mata Rai da ban Ni karairayar da Khadija take Masa tinda tafito acikin shegiyar motar Nan me kyaun tsiya ita da yarta ko bakuga yanda suke wani iyayiba se kace motar ubansu Ni bakin cikina motar da ko tabawa ban taba yiba bare insamu arzikin shiga Wai yau Khadija ce da yarta suka fito acikinta lanlai yau karuwanci yaiwa Khadija da malam Rana sun shiga motar da tinda sukazo duniya Basu taba shigaba Wai da zasu shiga ciki lokacin malam yagaMa mana tijara har dawani cewa baban sadiya wlh yanda kika san na shaketa haka na dinga ji har tagama fadar abinda zata fada Masa shikuma mijin tace jikinshi nabari yarike hannun sadiya suka shige daki Wai yarinya tayi abin kunya akaita azubar da cikin da tayi adinga lanlabata kamar kwai kuji har da cewa likita yace tana hutawa Ni har gobe mamaki nake du ranar da malam yake dakin Khadija har wani rawar Kai yake bini bini kaga yagudo daga wajan sanaarsa yazo wajanta sulume adaki kome suke susuka sani basa tsoran Yara su dawo daga makaranta suga me sukeyi dare nayi ana sallar Isha,I ze shige dakinta yaki fitowa yazauna da yaranta da ita suyi ta Hira suna shewa can dare yaran nayin bacci kamar munafukai zasu shige dakin malam Basu zakaga sun fitoba se gari yawaye yayi haske ko sallar asuba wataran baya zuwa kome take Sha yake wannan rawar kafar ohoh akin banza antsufa baasan an tsufaba Ni Dan bakin ciki narasa me sukeyi in sun shige har labe nake musu Amma bakajin komai munafukan daga ita har malam din ko irin wankan tsarkin Nan da muke fitowa muyi da safe Ido naganin Ido Banda ita tinda Nazo gidannan ban taba ganin tayiba anyama kuwa tana wankan tsarki Kuma Babu wacca yakewa haka acikimun se ita wlh Nima Sena tashi tsaye du ranar girkinta senayi abinda gaban malam ze Dena aiki har yagama kwana dakinta yafito sedai su kalli juna shi da ita ko na danah Mata kwado na shafe Mata gaba kowa yahuta Naga kofar da zaashiga ai rawar Kan aciki
shewa sukayi su,duka suka tafa
Malam ne yafito yai gyaran murya yakallesu yagirgiza Kai yai ficewarsa wajan Sana,arsa
Baki suka hada atare mun,shiga uku ko malam yajimu irin wannan kallan tsana haka da yai Mana
Bana turawa ta pc Dan Allah Kar Wanda ta biyoni tace natura Mata ta tambaya agrp zatasamu insha Allahhu
New writer’s
Hakan Take
*Husba’ahfama* ????????????
*’Yar kwalliya* ????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????????
????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????????????
????????????
????????????
???????? *HALEEMATUS SADEEYA*????????
Written by *HUSBA’AHFAMA*
IG *officiall_husba’ahfama*
Facebook *Real Husba’ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba’ahfama*
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
Wannan shafin nakune na sadaukar muku da shi gaba Daya kuyi yanda kukeso da shi ga du wani members na
HALEEMATUS SADEEYA GROUP
Da Yan
DAHWEESU NOVEL GROUP
Nagode sosai????????????
Kuna karamin kwarin gwiwa Kuma inajin Dadi Allah yasaka da alheri Allah yabar zumunci