Halimatus sadeeya

Farida Baki har kunne tahau murna se washe Baki take tana godiya
Hm Reza se Nan gaba zamuga me kike nufi da farida
Malika se yau da dandare wajan karfe takwas tadawo gida Shima mahaifinta,ne yakirata away yace Mata tana inah tace ai tana gida batasan yasan tin jiya rabanta da gida har aliyu babanta yakira yace Masa Dan Allah yakara hakuri Kan Wanda yakeyi yasan malika Bata kwana agida ba yasa Mata masu samata Ido ako inah in tashiga Ni da kaina akwai matakin da nakeso na dauka akanku lokaci nake jira kakara hakuri
Aliyu yace ba komai daddy Allah yakara girma
Yace ameeeen ko tadawo karkai mata mgn kazuba Mata Ido kafita harkarta kanuna bakasan me takeyiba bakai take wulakanta,waba Ni take wulakanta,wa take nunawa duniya ban Isa da itaba Kuma ita aganinta Kai take batawa Rai batasan Ni take batawaba du acikin yaran da nahaifa halinta yafita da ban batayo halin muba Ni da mahaifiyarta
Sukayi sallama yakashe wayar
Afili aliyu yace Allah kaimin maganin wanan matsalar Allah kakawomin dauki Malika kinyi nisa danma inajin sauki wajan mahaifinki Allah sarki bawan Allah da mahaifiyarki nake kaiwa Kara har zagina zata iyayi Dan San yaranta yarufe Mata Ido Allah sarki daddy shimafa hakuri yake da mahaifiyar Malika Ni wani abinma in munhadu da ita Naga tanayi wlh har kunya nakeji kamar uwatace takeyi Wai sirika tace meyi kuma gashi wasu acikin abokaina sun Santa gashi unguwarsu Daya da idi direba yasha bani labarin abinda matar takeyi gidanma kanshi yasha bani labarin me yake faruwa acikin gidan kamar Yana gidan danma wani lokacin Ina kwabarshi Kar yagayamin ai da wataran se yagayamin abinda zuciyata zata fashe ga idi direba akwai surutu ko kahanashi se yafada du daure fuskar da Kai Masa se yafada Allah yakyauta
Kiran sallr azahar yaji yatashi yatafi masallaci
Mahaifiyar malika irin Yan bokwannan,ne wayanda suka Mai da boko Akida komai nasu boko ita aduniya burinta yaranta suyi karatun boko aganinta sun shige raini awajan kowa tafi bawa boko mahimmanci Akan na musulunci dan ko mahaifin malika yasasu amakantar isilamiya se tasan yanda tayi tahana su zuwa aboye tasa wani malami Yana koya musu karatun boko aboye in sun taso daga makarantar boko ta safe saboda daddy ba mazauni bane itama kanta karatun isilama be Isah akantaba bare tasa yaranta su koya acikin yaranta masu rabone sukabi raayin babansu suka dage suka koyi karatun addini Daman Kuma acikin yaran gidan malika tafita daban irin yarannan,ne masu rawar Kai da rashin ji ga taurin Kai gashi du a abinda zuciyarta taraya Mata shi takeyi Babu Wanda ya Isa yacanja matashi ita Daman Bata damu da karatun addiniba ko ankaita isilamiya kafin uwarta tace sugudo ita zata Fara gudowa Kuma tafijin mgnar mahaifiyarta
sunmafi Shiri da da ita du wani Hali na mommy shi malika takwashe kamar malika kamar mahaifiyarta takwashe gaba Daya Dan haka hajiya rakiya take San Malika sosai sunan ta kenan hajiya rakiya yaranta na kiranta da mommy du wani Abu da malika take aikatawa agidan aliyu mommy tasani Kuma ko ajikinta gani take dedai Malika takeyi batama so daddy yake mgn akai ko yakewa Malika fada Tasha Kiran aliyu ta wankeshi tatass da rashin mutunci Akan yarta Malika har gobe haushin aliyu takeji yatsani yarta Kuma yahada yarta Malika da mahaifita itama kullin burinta taga alyu yasaki Malika tasamu me Santa Daman ita tin ranar da malika takawo aliyu yazo ya gaisheta taga be mataba taga tsarinshi da na yarta bazezo dayaba baze Bari ana sakewaba Bata so auransuba Allah ne yanufa se anyi ko yaran da Malika ta Haifa su walid basansu take ba tadau tsanar da takewa aliyu tadora kansu in sun hadu da yaran in Banda hantararsu da zagin ubansu ba abinda take musu Bata sakar musu fuska Kuma agaban malika takeyi ko ajikinta se daima ta Taya uwarta Dan haka su walid basaso akaisu gidan su Malika ko su hadu da mommy sun fisan su hadu da mahaifin malika Dan bakaramin kauna yake nuna musuba Yana ji dasu sosai Dan haka sukafi San akaisu gidan mahaifan aliyu sun fijin Dadi takowana bangare
Da malika ta tawo gida aliyu yiyayi kamar besan taba ko ta kanta be biba bare ya kalleta ta koma gida da burin Yana kulata Tai Masa tijara shikuma yaki cemata komai ga lefi tamasa tin jiya da taje wajan aiki ba ita tadawo ba seyau da dandare agidan nusiba ta kwana itace tabata shawara tayiwa aliyu Haka Dan tarama kulletan da yai agida yahanata fita shi kuwa ko ajikinshi yariga yasaba da halinta ga Kuma girman mahaifinta da yake gani
Yau ummi takira direban abbah mahaifin aliyu agaban abbah take Masa mgn
Tace aminu Dan Allah wata alfarma nakeso kai min ko nace temako ganin irin hankalinka da rikwan Amanarka gashi Kun Dade da alhaji konace da mu Amma bamu taba ganin kayi wani abin Allah wadaiba gashi mun yarda da Kai har zumunci muke da iyayanka yasa nace Zan rokeka Dan Allah acikin Dan,ginku najini Wanda kayaba da tarbiyar da nutsuwarta kasan zata rike Amana zata rike yaran da zaa Bata raino Amana ta kula da su kamar yaran cikinta mukeso kasamowa aliyu yaransa zatana kula da su Kuma gidan aliyu zata koma da kwana gaba Daya se dai tana zuwa ganin gida munasan Dantijuwa me hankali ko matashiya Wanda tasan ciwan kanta karka Nemo Mana bare ayan uwanka najini muke so Dan haka nace Zan maka maganar agaban alhaji zamuna biyanta kudin aikinta zamu samata kudin da zamu Bata in munga tana rike Mana Yara da kyau zamu Kara Mata albashi in yarinyace zamu dauketa kamar Yar cikinmu in ma babbace zamu kula da ita sosai ba abinda zata rasa in sun gaji da Zama agidan aliyu zaana kawosu Nan gidan suyini ko su kwana
Aminu yace to zanje na fadawa mahaifiyata ko nace mahaifana in ansamu zanzo nagaya Miki Wanda akasamu in kin yarda se naje na taho da ita
Tace to hakanma yayi Allah yasa adace
Yatashi yafita
Abbah yace wlh inajin tausayin aliyu tashi kandarar Kenan banaso inah goyan bayanshi gaban idansa Kar yaga haka yafara musgunawa matarsa duda na shedi aliyu ko karar da takawo rannan nayi mamaki dam nasan ba halin alyu bane Amma matarsa ko kunyata batajiba tagoce ta zubawa mijinta karya ko nace sharri yanzu aganinta mutunci takara a idona kome wlh Dan bakyau mutuwar aure da nabawa aliyu shawara yasaki yarinyarnan tinda ta nuna tagaji da shi agabanmu to ban saniba ko yanasan matarsa Kuma Ina ganin girman mahaifinta Amma wlh ko aliyu yaso ko be soba wlh nakusa daukan mataki akan matsalar gidanshi nagaji yaro yakoma abin tausayi bashi ba yaransaba sun koma marayun karfi da yaji kiga yanda aliyu yakoma abin tausayi kana ganinshi kasan bashi da nutsuwa
Ummi tace haka nakeso gara kadau mataki Nima nagaji su yaran insha Allahu tasu wahalar takusa zuwa karshe in dai ansamu me kula da su ta Allah Nima da shawarar da na yanke Akan alyu in nagama tinani akai Zan sanar da Kai in yayi se mu yanke hukunci kawai Allah yashige Mana gaba Allah yakawo Masa karshan wannan kandarar
Yau sadiya tin tashinta daya bacci tatashi kamar Abu na da munta umma ce takura Mata Ido tana nazari. YarTata tace sadiya
Tace naam umma
Umma tace me yake da munki yau tin tashinki daga bacci nake kula da ke kina tare da damuwa ba an hanaki sa damuwa araiba an hanaki tinani ko bakiji me likita yace Akan jikinkiba