Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Yau ummi tasa aminu yadau mota Dan yaje yadauko sadiya daga gidansu se da yafara biyawa gidansu yadauko mahaifiyarsa Yaya tukunna suka tafi tare lokacin sadiya tagama shiryawa Yan uwanta na zagaye da ita du basuso tafiyartaba malam ma be fita ko inaba Yana jira yaga tafiyar yarsa

sallamar Yaya sukaji yau Dan gullama su tala sunga malam nagida har da amsa sallamar Yaya da gaisheta takuwa amsa musu da faraarta tashiga dakin umma sukai Mata sannu da zuwa yaran suka gaisheta

Tace to sadiya da fatan kin,Gama shiryawa se tafiya damota mukazo daukanki sauri aminu yake zaa aikeshi wani wajan tashi mutafi Kar yagaji da jiranmu hawaye sadiya tafara kannanta naganin haka Suma suka Fara kuka malam ne yai musu tsawa

Yace mutuwa akayi ko ance muku Bzaata dawo bane zaku Tara Mana mutane kuyi Mana shuru kema sadiya da girmanki kina kuka gashi kinsa Yan uwanki kuka Kuma ga waya zamuna jin lfyar juna karku tayarwa da ummanku hankali

Shuru sukayi dukansu suka fito rakata su habi da yaransu na tsakar gida suna hadahadar dafa abincin sayarwa se gani sukayi sadiya da jakar Kaya Yara sun fito da ita ga malam da umma da yaran dakinta gaba Daya anfito rakata haba Nan suka zuba musu Ido

lamice takasa hakuri tace malam waye zeyi tafiya agidan namu

Yace sadiya ce

Tofa inah zata inji tala

Yace wannan Kuma be shafekuba tinda baasa da kuba

Habi tace kuma dai meye naku na tambaya tinda baasa da ku gashi kunja ana niyar Gaya muku baka kuzuba Ido in Tai wari maji

Umma tace insha Allahu se dai kuji alheri aniyar me Aniya

Suka fice suka barsu da cizan Dan yatsa Dan bakin munafurci Suma su habi biyosu kofar gida sukayi Dan suga Yaya zaai tafiyar mota sukaga anbude me Rai da lfy hadandiya sadiya da Yaya sun shiga aminu yaja sun tafi su umma se daga musu hannu suke

Tala dagudu takoma dakinta tahau tikar rawa tana Waka tace Kai,kai ashedai malam gobe da nisa ya iya aiki sadiya ta tafi saura Khadija Allah yarabamu da Kaya agida saura kaska Kai malam gobe da nisa kabiyani ai nazata be iya aikiba Ashe ya iya Daman yamana alkawarin sadiya zatabar gidannan gaba Daya sedai be San inda zataba Allah yaraka Taki gona Allah yasa antafi har abada akare atiti

Lami Kama hannun habi tayi suka shige dakin tala

Tala na ganinsu tamiko musu hannu suka hadu suka tafa

Lami tace ashedai bamuyi asarar kudinmuba be tafi abanzaba dafa har na Fara zafgawa malam gobe da nisa Allah ya,isa Ashe ya iyah aiki burinmu yafara cika kiga rashin kunya inaga alhajin da yai Mata cikine yaturo da mota takoma gidansa da Zama Kuma kiga mahaukata dukansu har malam din sunfito rakata se murna suke

Habi tace karuwanci me lasisi kenan shi ake Gaya muku kekuwa anrufe musu Baki da uban kudi ba Dole suje rakataba kiga itama munafukar yayarta har da ita azuwa raka sadiya munafukai du bakinsu Daya itama an rufe Mata Baki da kudi

Lami tace hakane Kuma habi mgnarki gaskiya ce Dan wannan dankareriyar motar kaf dangin su Khadija babu me arzikinta wlh aidai anyi abanza tinda ba gidan miji zaa kaitaba karuwanci zata tafi

Nace hmm su lame kenan ????

Sadiya Ido taware tana kallan kalar Dankareran gidan da me gadi yabuwa motarsu suka shiga Yar kauye ta koma kallan ko inah take na gidan Ashe da sauran kallo se da suka shiga ciki da sallama dauke abakinsu lokacin ummi tafito daga kicin

Tace sannunku da zuwa sannunku da zuwa ga yata ankawomin maman su Walid da Amira ta iso ku karaso ga wajan zama

Dariya Yaya tafara Dan taji dadin yanda ummi tanuna farin cikin ganin sadiya

 

 

 

Nagaji fa yau nayi kokari na muku da yawa

 

 

 

 

 

 

 

 

New writer’s

Hakan take

*Husba’ahfama* ????????????

*Yar* *kwaliya* ???? ????????

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????????
????????????

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????

????????????????
????????????
????????????

 

 

???????? *HALEEMATUS* *SADEEYA* ????????

 

Written by *HUSBA’AHFAMA*

 

IG **officiall_husba’ahfama*
Facebook *Real* *husba’ahfama*

Follow me on Wattpad @ *Real* *husba’ahfama*

 

 

*Bismillahir* *Rahamanir* *Rahim*

 

 

*Wannan* *shifin* *nakune* *masuyi* *min* comments???????? Ina godiya sosai Allah yabar kauna????

 

 

15-16

 

 

Yaya tace ga yarki,Nan mun kawo Miki

Ummi tace aikuwa wlh naji
dadi ga yaranta can tin jiya da na gayamusu sunyi sabuwar mommy me kirki shinefa suke ta murna sun dameni da tambayar yaushe zata zo

Gaisawa sukayi yaya tace hajiya ga sadiya Allah yabaku zaman lfy

Ummi tace Allah yabamu ikwan rike juna da amana

Yaya tace to sadiya ga hajiya kakar su Amira itace ta haifi mahaifin baban su amira

Itadai sadiya kanta asunkuye tin gaisuwar da sukay da Ummi bata kuma mgnba

Ummice tai wa sadiya bayanin yanda akin da zatafara yake tace anjima ni da kaina zan rakaki tare da su amira gidan alyu shima na kuma bashi amanar ki Dan inaso na hadu da malika Dan itama nai mata bayani da kaina Kuma shima zamu karasa mgnar kudin da zena biyanki du wata

Yaya godiya taiwa ummi tace to zata tafi se Nan da kwana uku ko biyu zatazo arakata gidan da sadiya zatai aiki tinda yanzu se dare zasu tafi ita tana sauri bazata Kai dareba anan sallama tayi da ummi da sadiya tatafi har wajan harabar gidan ummi tarakota da abin arziki sannan tatafi

ummi taji zuciyarta ta kwanta da sadiya sosai tana shiga ciki tatar da sadiya azaune a inda ta barta tace ah su Walid Basu fitoba aikuwa Basu San da zuwankiba zomuje na rakaki dakin da suke kwana

Kama hannun sadiya tayi suka shiga dakin da su walid suke

ummi tace Amira Walid ga mamanku na kawo muku tin dazu tazo bakuzo Kun gantaba

Tsalle suka Fara Walid yace anty sannu da zuwa

Amira tace Ni mommy zanna cemata mommy sannu da zuwa

Amsawa sadiya tayi tana ta musu Fara,a daga ganin yaran taji kaunarsu tashiga ranta lokaci Daya

Ummi tace sadiya Bari nasa akawo Miki abanci kici ficewa ummi tayi tabar sadiya da yaran

Walid da Amira kallan sadiya kawai sukeyi suna ta murmushi

sadiya tashi tayi taje inda suke takama hannunsu tace Ni Bari nazo wajan yarana tinda se kallona suke sunki suzo kusa da Ni nifa mommy ce awajanku kunji

Walid yace Bazaki na dukanmuba kina hanamu abinci ummi tace kina da kirki har wasa zamunayi tare da ke Kuma Zaki na koya Mana karatu kullin

Amira tace aike Bazaki na korarmuba in munzo wajanki,ko Kuma Bazaki na tafiya unguwa kullin ki barmuba tare da ke zamu na Zama kullin agida ko mommy

Dariya sadiya tayi tace eh Babu inda zanna zuwa muna tare Kuma bazan dinga korarkuba

Baki suka hada sukace kema kina sanmu,ko muma muna sanki sosai ita Daya mommy Bata sanmu in munje wajanta korarmu take Kuma Bata Zama agida kullin unguwa take zuwa Kuma in tadawo munje Mata oyoyo korarmu take ko ta dakemu in su asabe sun hanamu abinci in munje zamu Gaya Mata fada take Mana tahau zaginmu to koromu ke bazakina mana hakaba,ko

Sadiya jitayi yaran nashirin sata kuka ga wani mugun tausayinsu da yakamata rungumesu tayi alkawari tayi azuciyarta zata rikesu Amana ta kula da su tsakaninta da Allah

Du mgnar da suke du ummi najinsu lokacin zata shigo dakin itama hawaye take karasa shigowa dakin tayi tazauna kusa da sadiya takama hannunta

Tace sadiya kinji halin da su walid ke ciki nasan Kuma mahaifiyar aminu da shi kansa aminu sun Baki labari gashi kuma kinji da kunnanki awajan yaran wannan kadan kikaji sema kinje gidan Zaki dada ganin komai lokacin Zaki dada gane yaran na neman temako sosai halin da gidan aliyu keciki du wani Wanda ke cikin gidannan Babu Wanda be saniba tin Ina boyewa Dan Kar kowa yaji har takai yaran da kansu du Wanda suka zauna dashi agidannan suna Hira se sun bashi labarin halin da suke ciki yaran abin tausayine Basu rasa uwaba Basu rasa ubaba Amma Allah yajarabcesu da wata irin uwa se kinje gidan kinfara rayuwa aciki Zaki gane me nake nufi Dan Allah sadiya ga amanar su Amira kikula da su kamar yaran da suke jininki karsuyi kukan rashin uwa Allah yabasu uba nagari Amma uwa se ahankali Dan Allah kiyi hakuri da halin kowa nagidan daga malika har aliyu Dan du,kansu suna da kalar nasu murdandan halin shi aliyu aimai uziri macace tamai da shi haka Malika Kuma da Hali zakisha kalubale tawajan Zama da malika du da ba mazauniya bace agidan Amma Dan Allah ki daure kijure ki temaka kiyi hakuri da kowa nagidan insha Allahu zakici ribar hakurin da zakiyi agidan Nan gaba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button