Halimatus sadeeya

Sadiya jitai tsoro yakamata gabanta yahau faduwa batasan lokacin da hawaye yahau zuba a idantaba jitayi tsoran gidan da zata Tai aiki yakamata ga tausayin su Amira tanaji ga tsoran halin masu gidan da ummi tagaya Mata
Ummi tace Kar kiyi saurin sarewa Kar kibari tsoro yashiga zuciyarki kisawa zuciyarki Zaki iya Kuma temako zakije yi agidan kizama jaruma kinji
Cikin rawar murya tace to ummi Allah yashige Mana gaba Allah yabani ikwan kula da su Amira
Ummi tace ameeen haka nake,san ji ga abinci,Nan kuci ke da yaranki se ki huta sosai kafin dare yayi na rakaku
Dare nayi wajan karfe takwas na dare ummi tashirya tasa sadiya tashirya su Walid tadauko jakar kayanta sukazo wajan abbah zasuyi Masa sallama abbah tinda sadiya tashigo Ido kawai yakura Mata da sauri ta karaso gabansa ta durkusa har kasa cikin ladabi ta durkusa ta gaisheshi yaji dadin yanda ta gaidashi tambayoyi yadinga yi Mata har Akan karatunta tana bashi amsa yanda take bashi amsa yagane sadiya na da tarbiya jiyayi yagamsu da ita nasiha yai Mata Suma su Walid yajamusu kunne sunawa sadiya biyaiya Banda rashinji da rashin kunya sannan sukai Masa sallama har mota yarakosu Yana samusu Albarka
Ummi tace du yanda mukayi da su Zan gaya,maka in nadawo
Yace to
Sannan suka shiga mota suka tafi gidan aliyu motar su na karasowa gidan megadi yabude musu get suka shiga sadiya kallo takeyi tana mamakin Ashe gidan su ummi ba komai ta ganiba Akan gidan da aka kawota yanzu azuciyarta tace lanlai masu kudi suna shaaninsu ko mutuwa basa tinani zasuyi irin wannan gida haka aljannar duniya wayannan jamian tsaran kamar zasuci Babu du gidan suke gadi jitayi tsoran gidan yadada kamata dabadan Dan uwanta aminu ne yakawosu da tace gidan yankankai aka kawota zaa sayar se zancan zuci take
seda ummi tace sadiya fito munzo
Fitowa sadiya tayi ummi taciro waya ajaka takira number aliyu tace gamu mun karaso
Baa dadeba yafito Yana tafiya cikin izza jallabiyace ruwan kasa ajikinshi tamasa kyau se kace balarabe ga gashin kansa Daman akwance yake Yana da sansi se kamshin turare yake tashi ajikinsa tinkan yakaraso tiraransa yai musu sallama har yakaraso wajansu sadiya Bata kalleshiba se da taji muryarshi yanawa ummi sannu da zuwa su walid sun rungumeshi suna murnar ganinshi kallansa tayi taji gabanta yafadi gakwarjini da yaimata azuciyarta tace tubarkallah Dole kayi jan aji da daga Kai tinda Allah yabaka kyau se kace balarabe ko larabane Daman
Muryar ummi taji na cewa ga mommy su Amira nakawo muku
Yace mukarasa ciki ummi se muyi mgnar
Harcikin falansa suka shiga kowa yazauna sadiya kasa tanema kusa da kafar ummi ta zauna
Aliyu durkusawa yayi yagai da ummi ta amsa masa
Tace to ga yarinyar da mukayi Zan samo tana kula da su Amira sunanta sadiya Daman nagaya maka sadiya ga alhaji aliyu mahaifin su walid shine me Nan gidan
Sadiya Baki narawa ta gaisheshi kamar ance Dole yaamsa Mata gaisuwarta saudaya yadago Kai yakalleta yaji gabansa yawani irin faduwa yai maza yagau da Kai
Murmushi ummi tayi azuciyarta tace mehali baya fasawa alyu Zaki Malika ta canjamin Kai komai lokacine
Aliyu yace ummi nawa kukayi da ita zaana Bata
Tace ai Kai muke jira muji nawa kayanke
Shuru yayi can yace Zan Fara da biyanta dubu hamsin kafin inga yanda nata aikin yake in Naga tana aiki tsakaninta da Allah Zan Kara Mata albashi ummi kece sheda wlh wlh in ta cutar da su Amira wlh Sena hukuntata se munyi sharia da ita Dan nagaji da abinda Yan aiki sukewa yarana kece sheda ga amanar su Amira na bata Kuma nasan Kun Bata in taci ko abayan idone ita da Allah ranar da na kamata Kuma tana yimusu wani mugun abin wlh bazan yafe mataba se na hukuntata yakalli sadiya kima bude kunnanki Dan kiji da kyau Naga se wani sunsun,kuyar da Kai kikeyi du kanku halinku Daya dahaka kuke zuwa kamar na kirki daga baya kucuci mutane Dan haka kuka ficemin aka
Ummi tace ikwan Allah du me yakawo haka aliyu angaya maka duka suka taru suka Zama daya Ina ita matar taka ko batasan da zuwan,muba
Kame kame yakama yace tafita aiki
Dan tinkan suzo yaje kofar dakinta yafada Mata Taki mgn yatura Mata SMS Akan yau su Amira zasu dawo ummi ce zata kawosu har da me kula da su Amira tafito su taresu Taki bashi amsa yakirata awaya Babu adadi Taki dauka se hakura yayi yakyaleta abin yabata,Masa Rai ko da su ummi sukazo se da yaje kofarta yafada Mata Amma Taki mgn Taki fitowa Dan haka yahauwa ummi kame kame Kuma tagane bagaskiya yagaya mataba
Murmushi ummi tayi tace hm aliyu kenan ban sanka da karyaba kana Kare matarka,ko muje kanuna Mata dakin su Amira Dan na yanke hukunci tare da su zasuna kwana se Walid yadada wayo se
Araba Masa nashi dakin
Yace Amma ummi ai
Tace bana,san Jin komai kaidai kabi shawarar da na yanke inah da dalilin yin hakan
Gaba aliyu yayi cikin tsare gida suna binshi abaya har dakin su Amira yakaisu yanuwa ummi ko inah itadai sadiya du tsoran aliyu yakamata tin bayanin Jan kunnan da yai mata Akan yaransa Ido suka hada yagallah Mata wata uwar harara da sauri sadiya ta dauke idanta ta sunkuyar da kai du abinda ke faruwa a idan ummi Tai kamar Bata ganiba
Tsaki yajah yace ummi in kin gama da su inah falo
Tace to se nafito
Ummi tace sadiya ga gidan yaranki gakuma dakin kwananku ke da su Allah yatayaki riko ki kwantar da hankalinki du abinda akai Miki in be mikiba ki,kira numberta da na baki ki fadamin Dan Allah karki boyemin komai kinji muje yakarasa nuna Miki du abinda yadace
Du inda yadace aliyu yanuna Mata har inda kicin yake ummi nabiye da su se da aka Gama nuna,mata komai tukunna ummi Tai sallama da sadiya
Ummi Jan hannun aliyu tayi zuwa falansa tace wlh aliyu na sanka da tsanar Abu Naga yanda kakewa sadiya to kada naji kada nagani ga amanar Yar mutane Nan ahannunka in kacutar da ita ko kabari wani yacutar da ita Kai da Allah kasan akarkashinka take Kuma Amana iyayanta suka bamu wannan ba irin Yan aikin da kasani bane wannan da gatanta da darajarta temakwankuma tazoyi Dan haka ka kula da Yar mutane Kuma kajawa Yar mulkin matarka kunne karta kuskura taiwa Yar mutane wani Abu wannan ba irin sauran Yan aikin da take wulakantawa bace Babu ita Babu sadiya in bahakaba wlh Zan iya cimata mutunci Akan sadiya kaima in kacutar da ita wlh Sena Bata maka
Ido aliyu yazaro yace ummi wannan wace irin yargwal Kika kawo Mana wannan dokoki haka Ni ummi kallone banaso tafiya kallo tinda kukazo take kallona Kuma Ni yarinyar ladabinta haushi yake bani se wani sunkuyar dakai take nifa seyai shuru
Ummi tace yaushe ta kalleka Kai da wana idan kasan tana kallanka bayan tinda mukazo Kaine kake zafga,Mata harara kazata bana ganine du kasawa Yar mutane tsoranka azuciyarta da kasan labarinta yanda kake da tausayi da haka bazata faruba da Kaine nadayan temaka Mata
Shidai aliyu Jin ummi yake yace ummi nadau amanar da Kika bani akanta Allah yabani ikwan rikewa Zan kula da ita sosai Kuma insha Allahu bazan Bari acutar da itaba
Ummi tace yauwa haka na kesan ji Allah yaimaka Albarka
Har mota yarakata sukayi sallama tatafi
Bayan fitarsu daga gidan ummi tahau murmushi afili tace Malika Malika hmm Dani kike zancan muzuba Ni da ke
Yau kwanan sadiya Daya gidan aliyu tayiwa Yara wanka tayi musu abin karyawa tayi musu Shirin makaranta tahada musu du abinda yadace tafito rakasu suka hadu da malika tafito zata aiki kallan kallo suka tsaya yiwa juna sadiya da malika