Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Amira tace lah mommy Daman kina gida

Walid kuwa Kau dakai yayi yai kamar bega mahaifiyarsa,ba yahade Rai yarige hannun sadiya

Amira tace mommy Kinga ummi ta samo Mana mommy me sanmu tana da kirki har Sallah tasamu mukayi da asuba kamar yanda ummi take samu muyi in munje gidanta har karatu ta koya Mana har mun iya karatun da takoya mana

Wani tsawa malika ta dakawa Amira tace wacece mommy naku Wai wannan tanuna sadiya da yatsa tsawa ta dakawa sadiya ke wacece anan gidan da har Zaki rabani da yarana har tana cewa ke mommy suce wayakawoki gidannan yaushema wai kikazo wayakawoki an nemi izinina da zakizo,min gida daga zuwanki har kin rabani da yarana kiga Walid kauda Kai yake Dan yaganni bayama San ganina ko mgn yaki yai min me kika cewa yarana daga zuwanki akaina munafuka

hannu tasa ta cakumo sadiya tadaga hannu zata mareta runtse Ido sadiya tayi tana jiran saukar Marin Malika afuskarta Banda hawaye Babu abinda yake fita a idan sadiya tatsani tashin hankali batasan hayaniya bare har wani yahauta da fada

Malika jitayi anrike Mata hannu tana juyawa taga aliyu ne yarike Mata hannu yahade Rai kamar be taba dariyaba

Yace karki Fara wannan ba irin Yan aikin da kike nemowa da kanki bane ki wulakantasu har kina dukansu wannan me darajace da matsayi Dan zabin iyayenace wannan da kike cewa yaushe tazo gidan baa nemi izinin,kiba ita wacece uwar yaranace ita ke wacece akayanmiya anan gidan har wani matsayi gareki da zaa nemi izininki Dan Zan kawo me kularmin da Yara bake kin banzatar da su bakya,sansuba to Allah yabasu wata uwar me sansu me kaunarsu jiya kawai tashigo gidannan konace tashigo rayuwarsu Amma Kiga yanda yarannan ke farin ciki kiga daga Amira har walid kuka suke Dan kin batawa sabuwar mommy nasu rai ai Ni Walid yabirgeni da yaki kulaki kadanma Kika gani Sema nangaba har kuka se kinyi da idanunki danhaka ko dawasa karki,kara gigin sa hannu da sunan Zaki mareta wlh wlh du ranar da hannunki yadaga ze mareta ko dukanta wlh se na mugun Bata Miki Rai Dan Akan yarinyarnan wlh Zan iya Bata Miki Dan tafiki daraja da komai awajena tinda jinina takeso take kula da su Kuma iyayena sun yarda da ita ta kuma sadaukar da rayuwarta take kularmin da su wannan yarinyar da kike gani amanace awajena ko kuda bazanso yatabataba bare ke Wanda ba Kya kaunar jinin da nahaifa

Aliyu gaban sadiya yaje yakura Mata Ido abinda betaba yiwa maceba in Banda Malika Amma gashi yau yakurawa sadiya Ido Yana kallanta Dan har lokacin idanta arufe yake hawayene kezuba kamar ruwan fanfo daga idanta jiyayi ta bashi tausayi sosai gasu Amira da suke takuka suna cewa tayi shuru sun rinriketa

Cikin sanyin muryar yace kiyi hakuri ummu Walid da Amira Kinga yaranki nakuka saboda kukan da kikeyi Kuma Kinga makaranta zasu tafi Dan Allah kiyi shuru Dan hankalinsu yakwanta namiki alkarin Babu me kuma Bata Miki Rai agidannan ko kuka Babu Wanda ya Isa yasaki kuyi rabuwar farinciki da yaranki kisa musu Albarka kiyi musu addua kinji tinda makaranta zasu

Hannu yasa yagogewa Walid da Amira hawaye yahau ranrashinsu har suka Fara dariya

Walid yace daddy baka gogewa mommy nata hawayanba

Yakama hannun aliyu yasa akusa da fuskar sadiya

Aliyu yace ai itama Zan goge Mata hannu yasa itama yagoge Mata kamar yanda yaiwa su Amira jikin sadiya rawa yafara takuma runtse Ido ga kamshin aliyu da yacika Mata hanci me samutun nutsuwa

Tsalle suka Fara yeee daddy yagogewa mummy itama

Ido sadiya tabude ahankali idanta yasauka Kan malika da tasaki Baki tana kallinsu ga hawaye na tazuba a idan Malika sadiya jitayi gabanta yayi mugun faduwa gawani tsoro da yakamata Dan tagane malika itace matar gidan Kuma Mata wajan aliyu uwa wajan Amira da Walid in Banda rawa Babu abinda jikin sadiya yake Dan tsoran malika yagama shiga ranta

Aliyu dayaga haka hannun su amira yakama da hannunnshi Daya dayan hannun Kuma yakama hannun sadiya wani yarrrr yaji ajikinshi da yakama Mata hannu gawani irin yanayi da yashiga lokaci guda sadiya ma haka taji yarrrr ajikinta gashi namiji betaba rike Mata hannuba du jikinta amace tabi shi se waigen malika take ko zata biyosu tarufeta da duka

yace zomuje mu rakasu sutafi makaranta karsuyi lanti kinga direban dayake kaisu yadawo da su

Nan suka,tafi sukabar malika Baki sake tana shararar hawaye takasa mgn Dan aliyu yabata mamaki yadaure Mata Kai har tsoro yabata yanda yahade Rai yarufe ido yaballaleta da fada gaban Yar aiki yakunyatata

aliyu Yana sane yaiwa Malika Haka Daman haushinta yakeji gakuma mahaifiyarsa tazo gidan jiya Malika Taki fitowa ta gaisheta Kuma tana gidan ta,kuma San ummi tazo danhaka yaguma Mata wannan wulakanci yayi hakane yaga ko zatayi hankali ta dena yawan gantalin takeyi da abinda take Masa ta nutsu ta,kama yaranta ta,kula da su shima yasamu kulawa awajanta kamar yanda yake bukata azuciyarshi addua yake Allah yasa ta,fara kishin sadiya ta nutsu ta zauna takula da iyalanta tadena du wani abinda takeyi

Suna fita harabar gidan yasaki hannun sadiya Dan karfin Hali kawai yakeyi Dan shiyasan irin yanayin da yake ciki azuciyarsa yadangana haka rashin sabone Dan be taba rike hannun wata maceba inba malikaba tinda yagirma yauma Dan yagumawa malika bakin ciki yayi

Su yaran aliyu basuma zaci sadiyaYar ya aiki bace sunzata Yar uwar alyuce Dan sun ganta tsaftsaf da ita gata nutsantsiya ba irin Yan aikin da suka Saba ganin malika na kawowa bane

Daman ita malika nusaiba ce me samo Mata Yan aiki Dan haka suke Babu tarbiya Daman nusaiba da biyu take nemowa malika Yan aiki Dan tacinma manufarta take Nemo Mata take siyesu kan suzo gidan su Fara aiki Dan du Wanda zata samowa malika tafara aiki agidanta seta siyesu har magani Tasha Basu su badawa aliyu ahanya ko a abin Sha har malika Tasha bayarwa Yan aiki Susa Mata ko su bada Mata ahanya ko abin shanta

Sadiya nagefe har aliyu yasa su Amira mota suka tafi makaranta se dagawa sadiya hannu suke itama tana daga musu

Aliyu yakalleta yace Kinga mekaisu makaranta kullin in kinzo rakosu

Cikin ladabi tace to yallabai

Gaba yayi zuwa cikin gida itama tabi bayanshi har yashigo yaga malika na tsaye inda suka barta Bata kula da shigowarsaba da sauri yakoma Dan bega sadiya ta shigoba ashe ta tsaya ta kasa karasowa ciki Dan ganin malika da tayi atsaye tsoranta takeji Dan yakuma gumawa malika wani bakin cikin yaku Kama hannun sadiya

Yace yakikaki shigowa ciki zoki shige bangaranku kije ki karya kema ki huta Kan yaranki su dawo

Tagaban malika suka Kuma shigewa hannun sadiya na cikin hannunsa se hakuri yake Bata Dan malika tadada kulewa

Aikuwa burinshi yacika Dan ko bangaran su walid Basu kaiba malika ta saki wani mahaukacin ihu tace nashiga uku Ni malika yau me nake gani haka agidana kodai aliyu yahaukacene agabana yafifita wata akaina lanlai na yarda ummi bakyasona kin tsaneni kin rabani da aliyu nashiga uku aurema mahaifansa suka Masa ban saniba agabana alyu yake rike hannun mace wlh bazan yardaba

Dagudu tafice tana kuka zuwa gidan nusaiba dan taje tagaya Mata abinda yake faruwa

 

 

 

 

 

 

 

Godiya ta musamman ga

Shafa Umar jinjina tamusamnan
Da kairat isiyaku jinjina tamusamnan
Da zuwaira da Nana eshah da Fatima Muhammad jinjina tamusamnan da maman munar maman yaseer ban manta dakeba godiya nake kunayi inajin Dadi ngd da kwarin gwiwar da kuke bani kunayi inajin Dadi Allah yabar kauna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button