Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Kunyace ta kamata hannu tasa duka biyun tarufe fuskarta tana murmushi Kai yagirgiza yace yarinta manya Daman nazo nai muku sallama tafiya zanyi Zan Dan kwana biyu ban dawoba ga Kayan abinci da na anfanin yau da kullin nasa anzuba muku ke da yaranki Banda yawo Dan Allah kuringa kula Banda fita harabar waje ba hijabi ko Dan kwali Kinga da ban shigoba yanzu haka Zaki fita waje Babu dankwali kanki bare hijabi Kuma maza sunfi yawa agidannan karna Kuma ganin haka yafaru kowana wasa zakuyi iyakacinku iya bangaranku karnaga kunfita waje da sunan wasa kecefa Kika koyawa Amira yawo da hijabi ko yaushe inajin Dadi shine yau Kika Bari tacere Miki dankwali Kuma Kika,bita waje Zaki karba karnaga konaji kina sakarwa maaikatan gidannan maza fuska baruwaki da kowa in zaku wajan ummi koyaushe ban hanakuba in kungaji da Zama kuje amma Banda yawan da bashi da anfani ummi tamin mgnar zuwanki isilamiya ke da su Walid nagama komai zaku Fara zuwa ke da yaranki direbane Zena kaiku kullin gobe zaku Fara zuwa

Waya yabata meshegen tsada gashi kina anfani da ita nasa Miki numberta da ta kasar da zani nasa Miki kudi aciki zanna kiranki koyaushe In na sauka lfy Zan kiraki in da matsala kina kirana kina fadamin ga wannan kudin ki ajje hanninki ko zaku nemi wani abin Kan nadawo Dan Allah kikula da kanku ke da yaranki baruwanku da kowa se Allah yadawo da ni tashi yayi zetafi

Cikin ladabi tace adawo lfy Allah yasaukeka lfy mungode Allah yakara Budi

Dadi yaji har cikin zuciyarshi ahankali yace abinda malika ba iyaba kenan Daman Mata na godiya in anmusu kyauta Kai Nima Dan ba mijinta bane Danhaka ta godemin har tamin adawo lfy in mijintane bazatai masaba du halinsu daya Mata kenan hannun su Amira yakama suka fice zuwa wajan motarsa suyi Masa rakiyi har sunyi nisa yajuyo yace zo in nashige ki tafi da yaranki

Ahankali jiki amace tabiyo bayansu har wajan mota kafin yashiga se da yai addua sosai kafin yashiga cikin motar yazauna direba yajah yaransa suka biyo bayan motarsu megadi yabude musu suka fice da gudu se hannu su Amira suke daga Masa shima Yana daga musu har suka Dena ganin juna

Sadiya da su Amira na komawa ciki ta barsu afalo suna wasa ita daki ta shige taiwa kudin da yabata wajan ajiya ta ajje ta jona wayar da yabata acaji tayi mamakin tsada da girman wayar da yabata

afili tace wannan waya ai tafi karfina kodai besaniba yabani Kai be kula da wayar da yabaniba Sena nunawa ummi Kan na fara anfani da ita yanzuma Zan Kira nagaya Mata

Daman akunne wayar take murmushi tahauyi ita Daya tashaki kamshin aliyu da yake tashi ajikinta tarufe ido Kan gado tafada ta kwanta tayi rigingine se murmushi take tayi tana shakar kamshin tana rufe Ido du jinta take wani iri

Tace tubarkallah gaskiya mutuminnan Allah yabashi kyau Kuma bashi da girman Kai bashi da mugunta Allah yabashi baiwar kyau Amma matarsa take banzatar da shi Ni tinda nazo gidannan kaina yadada kullewa ban taba ganin kalar rayuwar aure irin ta gidannan ba bubu tsari alamarin matarsa Bata kula da shi tausayi yake bani wlh narasa meyasa bawan Allah gashi daga ganinsa zeyi hakuri Allah sarki me temako koyana inah yanzu ko Allah zesa na ganshi wataran Ido da Ido meyasa har aka sallameni a asibiti bantaba ganinkaba ko Kai kasanni gashi kusan kullin se ka fadomin azuciya kullin addua nake maka ta alheri Allah yasa wataran mu hadu dakai aikuwa da naji Dadi

Tashi tayi Dan ta dora musu abincin rana

Aliyu amota Ido yarufe yajingina da kujera afili yace aliyu me yakaika kana zamanka lfy kajawa kanka Wai yarinyarnan mutunce kuwa

Dan shiyasan me yakeji ajikinsa tinda jikin sadiya yataba nasa jikin daurewa kawai yake gashi saubiyu kenan haka nafaruwa tsakaninsu indai jikinshi da nata yagogi da na juna se yaji canji ajikinshi se yashiga wani Hali ciwan mararsama tashi yau yake nema yayi yadanganta haka Akan rashin kulawa da malika takeyi Masa Dole yashiga wannan halin hakkinshi,ma babashi takeba

Ahankali yace malika kin cuceni kinsani wani Hali nakai lokacin da hakurina yakusa karewa akanki yanzu da bani da tsoran Allah da kinja na fada ahalaka na dauko zunubi na kwaso Mana cuta Allah nagode maka da kabani tsoranka azuciya Allah kadada tsareni Allah karka ban ikwan da Zan Saba maka gashi Allah yazubamin kyankami wace matama nake da lokacinta bare nace Zan aura tsoransuma nake konace na tsanesu haka Zan ta hakuri nai ta azimi har Allah yakawomin mafita a alamurana

Tinanin sadiya yake ko Ido yarufe sadiya yake gani ga kamshinta Yana jinsa ajikinsa har yashiga jirgi bedana tinanin sadiya ba

Itama sadiya anata bangaran hakane ganin abinda yafaru tsakaninsu da aliyu take gani in tarufe Ido gashi abin yahade Mata biyu ga me temakwanta yau se tinoshi take tanaso tasan ko waye shi haka tayini cikin tinani

Aliyu yasauka lfy bayan yahuta yakira sadiya awaya suna Shirin kwanciya bacci kiransa yashigo se karar waya sukaji duba sunan sadiya tayi taga sunan da yanuna ajikin wayar ansa abban Walid tana gani tagane me Kira cikin faduwar gaba ta dauka da sallama bakinta shuru yayi na wani lokaci har ta dauka baya jinta tadada gaisheshi numfashi yaja da kwrfi kafin yaamsa Mata

Tace kasauka lfy ya hsnya

Yace lfyklau alhamdulillah yakuke ke da yaranki nazata ma kunyi bacci kodaya ke da yaranki kunajin Dadi Kuna jin dadin wasa badai wata matsalako

Kunyar aliyu takeji sosai gashi in tatuna faduwar da ta kusayi tafada jikinsa kunyace take dada rufeta murmushi tayi cikin sanyi murya tace lfyklau muke shirinma kwanciya mukeyi

Yace to alhamdulillah yaran naki nakusa bani aransu mu gaisa

Walid tafara mikawa wayar suka gaisa da aliyu Walid yace daddy in zaka dawo kasaya Mana Kayan wasa masu kyau Ni da Amira da mommy iri daya zaka siyo Mana

Dariya aliyu yahauyi yace Walid kuna jin dadin wasa ku da mamanku yanzu har dakwan Kayan wasa Zan muku Zan sayo muku kaji kumin addua Allah yadawo da Ni lfy Zan sayo muku mekyau

Murna Walid yahauyi Yana dariya yabawa Amira wayar su gaisa itama gai da shi tayi ya tambayeta yasuke tace lfyklau daddy Ni Kayan kwalliya zaka siya Mana Ni da mommy zamuna kwalliya Ni da ita

Aliyu yace Zan siya muku wazakuyiwa kwalliya Inna saying muku

Tace agida zamunayi Ni da mommy inzamu unguwama muyi Ni da ita

Yace banda dai unguwa agida kawai zakunayin kwalliya in zaku unguwa karkuyi Zan saya muku kinji ko dayake bawa maman naku

Dariya Amira tahauyi tana cewa daddy mungode

Tamikawa sadiya wayar takara akunne shuru tayi tana jiran taji me zece

Yace kinbiyewa yaranki Kin koma karamar yarinyako yanzu Dan rigima har Kayan wasa danki yasa nasiyo muku ke da su du kunzama yarako

Kunyace ta kamata tahau dariya kasa kasa shima dariya yakeyi yau Haka kawai yajishi cikin nishadi yaji yanasan janta da hira dadin janda da Hira yakeji

Tace ai bama wasan Yara

Yace ko Amma Kuna wasan kasa in bakwa wasan kasa har Yar goyo kunayi da rarrafe da guje gujeko

Shuru tayi tahau tinanin a Ina yasan suna wannan wasan Nan kuwa batasan ta CC,TV yake ganin abinda sukeyiba

Yace Amira tace nasiyo muku Kayan kwalliya Zan sayo Amma banyarda in zaku fita unguwa kuyi kwalliyar haukan da Mata sukeyi sufita da ita unguwaba agida kadai na yarda ke da Amira kuyi kwalliya in zaku fita ko Yana fuskarku se Kun goge kafin kufita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button