Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Tace to da baka siyaba Ni bance tagaya maka ka
siyoba

Yace nasani nasan halin yarana duka karki da mu farincikinsu nakeso kome yake faruwa in da matsala ku kirani ko ku Kira ummi kufada Mata

Ranar da aliyu yayi sati Daya da tafiya sadiya da su Walid sukeje gidan ummi tayi farin cikin ganinsu yanda taga jikokinta sun canja har kiba sunyi cikin murna ta,taresu tarungume sadiya taringa shimata Albarka sunci saa abbah nagida shima yayi farincikin ganinsu yai tasawa sadiya Albarka Yana Mata godiya kowa yaga su Amira yasan sun,samu tarbiya yanzu bakamar da ba abinda su Amira Basu saniba da suga su ummi su gai da su yau se gashi har kasa suka durkusa suka gai da su ummi hawayene yacika idan ummi tarungume su Amira tanawa Allah godiya
Se da suka kwana biyu gidan ummi sannan suka koma har kitso akayiwa sadiya

ummi da taga gashin sadiya mamaki ta dingayi tana tubarkallah
tace hm aliyu kakusa shiga hannu

Amira Daman sadiya ce me Mata kitso Walid ma har aski anmasa haka suka taho gida suna kewar su ummi basuso suka baro gidanba saboda makaranta suka dawo

Yau satin aliyu biyu da tafiya tinda yatafi malika batasan yayi tafiyaba tinda ba shiga harkar juna sukeba Kuma Bata Zama agida se dare wataranma se ta kwana biyu ko Daya take dawowa gida du nusaibace tace tanayin haka in tataso daga aiki tazo gidanta tana kwana wataranma gidan wata kawar zata kwana in taje biki ko suna ko Kuma fatinsu na jaraba ita malika gani take hakan da takeyi aliyu take batawa Rai shikuma yashareta saboda babanta yakirashi har gida yace karya kulata akwai lokacin da yake jira zega me zeyi yaimasa wannan alfarmar Dole aliyu yahakura yazubawa sarautar Allah Ido yakawar da kasansa yai kamar besan abinda takeyiba yanzu bincike malika tayi sosai Akan aliyu Dan haka tagane yayi tafiya baya kasar har Ido tasa ko zataga yadawo yakwana agida bata ganshiba har dakinshi taje taga akulle abinda yabata Mata Rai sosai Kennan

afili tace aliyu Ni kakewa haka Ni kake wulakantawa har takai kayi tafiya bansan da tafiyarba Dan nahaifa maka Yara nazama tsohuwa kake wulakantani Dan Haka banama so asan nice nahaifi su Amira ko Dan nasamu ciki kake wulakantani har da min karya kanunamin kanasan ya’ya Ashe yaudarata kake Dan Haka naso zubar da cikin jikina na tsani wannan cikin kandarar na jikina zakaga matakin da Zan dauka daga nahaihu zakasha mamaki wlh har daddy du se nabaku mamaki badai daddy bayanka yakebiba yafisanka akaina Ni da yahaifa shima aliyu kaja Masa wlh Ina haihuwa Kai da daddy Zan Baku mamaki shawarar mahaifiyata zanbi da tabani Akan cikinnan bazan zauna inaji Ina gani ka cuceniba ko Dan kasamu wannan Yar duniyar Yar aikin kake wulakantani har kake nuna tafini daraja awajanka wayasanma me kuke aikatawa Kai da ita nasan ita tasan yayi tafiya Ni Kuma matarsa ban saniba Dan sakwan da yake barmin in zeyi tafiya be barminba wannan Karan badai Akan yarinyarnan Yar aiki kake min hakaba Dan tana kula da yaranka akanta zandau fansa zakasha mamaki inkaji me mukai Mata muzuba Ni da kai se dai kadawo kaga Bata gidan dariyar mugunta takece da ita kamar wata mahaukaciya tafita da gudu zuwa gidan nusaiba

 

Sun tsai da ranar da zasuyi Taran fatinsu sun kuma shirya irin wulakancin da zasuyiwa sadiya du wayanda yadace su gaiyata maza da Mata sun gaiyata har manyan alhazawa Yan hurdarsu nusaiba da kawayanta du sun gaiyata gogangun yanduniya masuji da kansu suka gaiyata yau asabar yau yakama satin aliyu uku da tafiye yaune Kuma ake Taran fatin su malika ancika gidan aliyu dam da mutane maza da Mata har da samari da yanmata wasuma malika Bata sansuba nusaiba da kawayantane yanduniya ne suka gaiyatosu bakaramin kudi aka kashe awajan shagalin fatinba nera dayar nusaiba Babu acikin shagalin fatin du da kudin malika akayi komai suna hura Mata kai matar mekudi ita Kuma shasha tana fito da kudi kamar batasan ciwansuba irin kudin da nusaiba taga malika takashe awajan shagalin fatin nusaiba takara tsanar Malika takuma ci damarar raba malika da aliyu takuma dada daura damaran auran aliyu takowace hali har makada aka gaiyata ko auran yammata uku ko biyu ake agidan aliyu se dai haka irin wannan Taran gida yakaure da hayaniyar jamaa da ta makada

Sadiya da su Amira basusan meyake faruwaba se jisukayi gida yakaure da kade Kade da hayaniyar mutane lokacin karfe hudu na yamma har wajan shabiyun dare zaakai ana Taran lokacin Kuma makaranta sadiya da su Amira sukeso su tafi sun shirya sadiya taleka ahankali ta kofa Babu Wanda yakula da ita yawan Taran mutanen da tagani yabalain Bata tsoro jikinta rawa yafara tarasa inda zatasa kanta tambayar su walid take me akeyi yau agidan Suma Kuma su walid tambayar da suke Mata kenan jitayi gabanta nafaduwa sosai jikinta yamutu adduar neman tsari tafara azuciyarta se fasa zuwa isilamiyar sukayi saboda Babu hanyar da zasu shige in zasu shige se dai tacikin jamaa Dan haka tacewa su walid suyi hakuri gobe saje

Walid yace mommy daddy yasan da bikinnan to bikin wa akeyi Kuma daddy da ze tafi be Gaya Mana zaayi biki anan gidanba Kai wannan Wanda akace itace mommymu da batasanmu nasan itace take biki se na gayawa daddy kibani waya na kirashi na tambayeshi

Sadiya tace base ka kirashiba tinda kaga haka yasan da bikin

Walid yace Allah banasan matar tinda batasanmu kefa Amira kina santa

Amira tace Nima bana santa yanzu Dane nake santa Naga Bata sanmu shine Nima nadena Santa

Sadiya fada takama musu tace karna karaji mahaifiyarkuce itace ta haifeku ta kawoku duniya itamafa tana sanku aikine yaimata yawa zata kula daku in tagama aikin da takeyi

Kafin su Bata amsa sukaga anbanko kofa anshigo Matane wajansu goma da maza biyu har da malika da nusaiba sadiya kawai se jitayi anwanka,Mata Mari anrufeta da duka

Malika tace Dan ubanki kinsa ya’yana agaba kina musu hudubar tsiyako kina huremusu kunne Kan sudena sonako kina nema ki rabani da yarana ki kwacemin mijiko munafuka Ina aliyu yaje yayi tafiyane ko Yana gari

Kuka sadiya tasa jikinta nafari tace yayi tafiya

Ai kafin tskarasa Bata amsa malika tadada dauketa da Mari

Nusaiba tace tsaya tsaya ai baanan zamu wulakantataba se a idan jamaa yanzu daukanta mukazoyi takarfi da yaji ke wacece da kike Jan aliyu jiki har Kika San yayi tafiya matarsa Bata saniba da Ni kawarta kwace zakiyiwa mutaneko aliyu yafi karfinki ko goge Masa takalmi baki kai matsayinba bare har kibari yarike Miki hannu kinyi kunkuran Barin yata jikinki

Janta sukayi takarfin tsiya suka cinlota waje inda Taran mutanen suke su Amira se kuka suke suna biye da su abaya suna cewa kubar Mana mamanmu malika Dan bacin Rai yanda su Amira suke kuka Dan ana dukan sadiya tarufesu da dukan wulakanci

Tana cewa waceca maman taku nice Nan mamanku Dan ubanku

nusaiba itama zuwa tayi tasa hannu tataya malika dukansu malika takama Amira da duka kamar zata kashe nusaiba Kuma takama walid da duka kamar zata kashe badukan wasa sukai musuba se fitar da numfashi ahankali su Amira sukeyi sadiya nagani Babu halin kwatarsu itama mazan wajan se ruwan lemo suke kwara Mata ajiki du sun mata wanka da ruwan lemo suna banbaka dariya suna haurinta da kafa kamar sunsamu damba Mara galihu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button