Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Dansandan da yai harbi sama shigowarsune yataho dagudu yace yallabai karkayi kisankai karkadau doka ahannunka akwai hukuma kasaketa tanafa daciki ba ita kadai bace yihakuri kasaketa yallabai aji tausayin cikin da ke jikinta Bata kyautaba Dan Allah kayi,hakuri hukuma zata hukuntasu du kansu karka dau doka da hannunka

Dakyar yasamu yakwaci malika ta jigata ahannun aliyu tafita haiyacinta

Dagudu yaran aliyu sukazo suka dauki su Walid suka sasu amota sukace yallabai mu munyi gaba zamu kaisu asibiti

Kai kawai yadaga musu Yama kasa mgn

Kallan Malika yayi cikin tsana yace malika Ni aliyu idiris kije na sakeki saki daya bani bake har duniya tanade

Yakalli dansandan itama kutafi da ita ku kullemin ita se munyi sharia da ita Akan wulakantamin ya’ya da tayi da uwar ya’yana da taramin gardawa agida

 

Mutuwar tsaye tayi gabata gama warwarewa daga shakar da Tasha awajanshiba gakuma saki da yadankara Mata suman tsaye tayi Dan ko amafarki batayi tinanin akwai ranar da aliyu ze iya sakintaba gani take baze iya rabuwa da itaba saboda San da yake Mata

Nusaiba wani irin farin cikine yarufe zuciyarta murna tahauyi afuskama farincikin da take ciki yanuna yau burinta yacika taraba malika da aliyu yau aliyu da malika sun rabu jitayi Tama Gama Zama matar aliyu Tama Gama shiga gidansa kallan kyan gidan da kawatuwar da yayi da irin kudin da aka kashewa gidan wajan ginashi take tana tinanin irin iskancin da zata tatawa mutane in tashigo gidan zatayi yanda takeso tana cikin tinani taji anrufeta da duka ta ko Ina bude Ido tayi taga waye da wannan karfin halin yarufeta da duka azamanta na wacce aliyu ze aura yame gurbin malika da ita Dan jitakeyi Tama Gama Zama hajiya meji da kanta itama in ta auri aliyu zata Tara kudi da gwala,gwalai kamar yanda taga malika tatara bude Ido tayi sosai cikin azabar dukan da take Sha taga kowaye taga aliyune yake dukanta haka Babu tausayi Babu komai har da kafa yake naushinta lokaci daya kamanninta yacanja Dakar yansandan da ke wajan suka karbi nusaiba du tafita haiyacinta abinka da sauran bilicin hular da tasama tagashi tadade da cirewa gefe daya se kwaryar kanta ake gani da yadada Kara Mata Muni ainahin gashin kantama Babu kannata kamar namaza yake gashi irin matan,nanne masu katan Kai da goshi bakaramin kunyatata aliyu yayiba awajannan ga mutanan,ta awajan kafinma suzo bakaramin karya tazuba musuba har labari tabasu suna soyaiya da aliyu ze auretane gidan mijin da zata aurane Dan Haka tinda suka shigo take nuna gadara da isa tana wani daga Kai Amma dayake malika mahaukaciyace du bata gane me nusaiba da kawayanta suke nufiba se wani hura hanci nusaba takeyi se kodata kawayen nata sukeyi da sukaga gidan Amma aliyu ya,kunyatata agabansu abin yayi mugun taba Mata zuciya inda tadada daura damarar shiga gidan aliyu dan ta nuna Masa kuskuransa takumaci kudinsa

Aliyu yace du wayannan gardawan kutafi dasu kurufesu wlh se munyi sharia da su sun gayamin dalilinsu na shigomin gida cikin iyalina ku in akashiga naku gidan cikin iyalinku akayi wannan shedanancin zakuji dadi
Yanuna alhaji bushasha Kai Kuma Kaine tsohun banzako kasamu yarinya karama zaka lalata ka kunya bakaji in anyiwa yar da kahaifa zakaji Dadi ko akayiwa matarka

Rufeshi sukayi da masifa alhazawan wlh baka isaba me kakeji da shi kudiko muma munaji da su muje kotun muzuba mu da Kai Kai Kama isa ka kiramana yansanda su tafi da mu su rufemu wlh mu munfi karfin wulkanci muje can din

Murmushi aliyu yayi Babu Wanda yakula acikinsu yace Suma matan baze hakuraba se anrufesu

Haka yansandan suka hada Kan mutanan wajan gaba daya suka tafi da su masu mota se ahadashi da dansanda daya sutafi dedai da Malika aliyu be raga mataba bare yaji tausayin cikin jikinta haka aka tisata agaba aka tafi da ita da su nusaiba da zugar kawayansu da haka har aka kwashesu

nusaiba jiyi ta,dada tsanar Malika sosai ta,kuma dau damarar Kara zigata ta nesanta da aliyu yanda ita zata samu tashiga jikin aliyu taruwan sanyi har ta aureshi se sadiya da ta tsaye,mata arai Dan yau ta,dada tambatarwa kanta aliyu yadamu da sadiya Kuma ze iyayin komai akanta Dan tayi mamakin ganin bacin,ransa sosai akan antaba sadiya Nan ta,dada sawa aranta se ta dada shiryawa sosai akan Sadiya Dan yanzu ita damuwarta yanda zata Kori sadiya daga gidan aliyu Kuma yanzu murnarta Allah yasa su Amira su mutu kowa yahuta Dan taga aliyu namusu so bana wasaba Dan Haka tataya malika dukansu ta yanke shawara in su Amira Basu mutuba ita se tayi ajalinsu Dan tana ganin in tashiga gidan aliyu yarannan zasu takura Mata Kuma Bata kaunar ganin jinin malika akusa da ita Daman can ita ta tsani yaran Dan har ziga malika take Akan yaran Dan har da sa hannanta wajan ziga malika tsanar haihuwa da yaranta

Aliyu dagudu yai Kan sadiya da take layi yace yihakuri kema asibiti Zan kaiki dagata yayi ze Kama hannunta yaga tazube Masa ajiki Ashe Suma tayi girgizata yahauyi yana Kiran sunanta sadiya sadiya yaji shuru shikenan sun kashewa su walid uwa

Daukarta yayi kamar wata jinjira yai mota da ita dagudu aka bude Masa har ze shiga yatina jikinta Babu hijabi Babu dankwali yacewa direban karka shiga kajirani Ina zuwa yai cikin gida bangaran su walid dagudu dakin kwanansu yashiga yabude drower kayansu yaci saa na sadiya yabude yadauko doguwar Riga da hijabi yafito da gudu Dan komai cikin sauri yakeyinshi motar yashiga se da yaga yasaka Mata dogwan hijabin tukunna yabawa direba umarnin shigowa yajasu suwa asibiti se masifa yakewa direban Akan yai sauri Kar su walid su rasata suna isa asibitin aka karbeta aka Bata gado akahau dubata har ruwa akasa Mata

Likitan yace karka damu yallabai kasan tana da hawan jini tintini Duda beyi karfi sosai ajikintaba yanzunma bacin Raine yasa tashiga wannan halin da Hadi da dukan da aka Mata Wai suwayema sukai Mata wannan dukan haka Kuma ai munja kunne cewa Kar ana Bata Mata Rai yaakayi haka tafaru

danshi Dr gani yake sadiya Yar uwar aliyuce Dan yaga ai kwanakima shine yakawota har suka Bata gado Kuma shine yakula da ita be San aliyu bema gane sadiyaba

Shi aliyu kansane yakulle be gane me Dr yake nufiba da bayanin,saba shi yashiga damuwar sadiya na da hawan jini yaushe hawan jini yakamata besaniba tana yarinya karama Ashe Malika ta,dade tana kuntata Mata da bayanan Amma sadiya Bata,taba Gaya masaba jiyayi yadada tsanar malika gaba,Daya har yanzu in yarufe Ido yaga Taran mutanan da suka taru agidansa da Kuma halin da yadawo yaga sadiya aciki yake gani ransa dada kuna yake Yana baci

tun jiya hankalinshi yayo gida yanaji gabansa na faduwa yau Kuma da yatashi tin da asuba yaji gaba Daya gida yakesan dawowa faduwar gabansa yadada karuwa yaji su Amira yake San gani Ashe halin da suke ciki kenan abinda zezo yagani kenan Dan Haka yabiyo jirgi yadawo gida Yana isowa masu gadin gidansa suka kirashi awaya suka fada Masa abinda ke baruwa agidansa da abinda akewa sadiya Dan Haka tin ahanya yakira yansanda awaya tare suka karaso Dan Haka suka shiga gidan atare saboda kwamashinan yansanda na Kano kanin ummine uwa Daya uba Daya Dan Haka daga yakirashi yagaya Masa anmasa Abu yanasan aturo Masa yansanda zaaka turo Masa babu Bata lokaci kosu nawa yake bukata zaaturo Masa Suma Kuma yansandan sunaso suji ance aliyu na nemansu murna suke sunsan samu yazo Dan kudi yake sakar musu sosai saboda bashi da rowa Dan Haka yakewa alhazawan,Nan dariya gakuma shugaban alkalai na Kano shikuma kanin abbane uwa daya uba Daya aliyu dangatane gaba da baya du Wanda yatabashi se yaji ajikinshi ko befadaba adangi wuyartane suji zasudau mataki bare wanannan shine yakira yafada da kansa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button