Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

.bacci sadiya take da akasa Mata ruwa Dan Haka yafito daga wajanta yasa yaransa su rakashi dakin da aka kwantar da su Amira Suma yasamu har da Karin ruwa ake musu bacci Suma suke tayi tausayi yaran suka bashi sosai dayaga yanda jikinsu yakunbura abinka da farar fata jiyayi hawaye nazuba a idanshi Wai uwa mahaifiyace taiwa ya’yan cikinta irin wannan dukan

Ahankali yafara mgn malika na tsaneki bana sanki kamar yanda bakya sanmu Ni da yarana Nima Sena Miki abinda Bazaki taba mantawa da Shiba har kikoma ga Allah kamar yanda Nima kika min iya bakinciki kin taramin azuciyata bazan taba mantawa da keba arayuwataba

waya yaciro yakira
Mahaifin malika yagaya Masa abinda ke faruwa gaba,Daya har Taran da tayi na yanduniya agidansa da dukan wulakancin da sukaiwa su Amira da sadiya har kullesun da yasa akayi se da yagaya Masa Amma begaya Masa yasaki malikaba Dan Yana ganin girmansa baze iya gaya,masa yasaki yarsa ta wayaba se komai yalafa ze Gaya Masa da bakinsa yakuma cemasa yanzu haka suna asibiti ankwantar da su Amira sannan yakashe Kiran sukai sallama

Mahaifin malika nagama waya da aliyu yahau tari mekarfi Yana dafe gefen girjinshi Yana cewa malika kin cuceni kin zubarmin da mutunci da kima a idan duniya

dagudu manyan ya’yansa da suke gida sukayo kansa suka rinrikeshi suna tambayarsa meyake faruwa yayi hakuri Kar ciwansa yatashi maganinsa suka dauko Masa suka bashi yasha se da yadawo haiyacinsa tukunna suka hau Masa tambayar me malika tayi Nan yagaya musu abinda yake faruwa

Budar bakin mahaifiyar malika cewa tayi yanzu alhaji Akan abinda Malika tayiwa aliyu shine kake nema ciwanka yatashi Kai Wai aliyu mallakeka yayi kake nuna,Masa so fiye da Yar da kahaifa acikinka Kai kullin aliyune me gaskiya malika Bata da gaskiya yarinyar,nanfa aliyu cin zalinta yake cutarta yake Amma Kai idanka yarufe shi kakeso yanzu Dan Allah inda yanasan malika zesa akulleta da tsohon ciki yau ko gobe yarinyar tashiga watan haihuwarta,fa Amma Dan rashin imani yasa aka kulleta wlh bazan yardaba se nadau mataki ai kome malika Tai Masa bedace yakulletaba ai ko darajar yaran da tahaifa Masa yaduba da tsohon cikin da take da shi ai Daman nasan wlh basan malika yakeba jikinta yakeso nifa kome malika taiwa aliyu ta yimin dedai Kuma wlh sedai in Banga aliyuba se na cimasa mutunci in uwarsa akaiwa haka ko kanwarsa mijinta yai Mata zeji Dadi wlh se nayi sharia da aliyu senaga meyake takama dashi

Daddy yai murmushi yace hm yaro besan wutaba se yataka to koni Nan aliyu yafini gata akasarnan da matsayi gatan da yake da shi koni bani da shi bare ke Karan kada Miya danma yaran beme girmankai bane bayanuna shi wanine malika tayiwa kanta tabar adalin miji Dan asali me tsoran Allah Bazata ganeba se Nan gaba zatayi da nasani Kuma hakkin aliyu se yakamata Dan Allah baya bacci kome kayi yana gani bare mijinta ta kuntatawa ta wulakantashi a idan duniya wlh to kisani wlh da wasa kikasa Baki Akan mgnarnan ko Kika samu aliyu ko iyayansa Kika cimusu mutunci ko kikeji inda aka kulle malika wlh daga ranar narabu dake har abada abakin auranki kemadin angaya Miki dadin Zama nakeji da ke darajar yaranmu kikeci Amma tinda bakisan hakaba kijira sakamakwanki wlh wlh aure zan Kara Babu fashi nagaji da halayarki da ta yarki malika angaya Miki du irincin mutuncin da kikewa aliyu da yaransa ban sani bene to nasan komai Ido nazuba miki Naga iya gudun ruwanki tinda da ga ke har yartaki Baku da hankili Ni da kune ko mgn kika karayi anan se nabaki mamaki karna karajin bakinki

Shuru tayi takasa mgn se Ido da take ta zarewa mgnar daddy tabata tsoro batakawo haka daga gareshiba ita yanzu abinda yafi tada Mata hankali mgnar auran da daddy zekara da mgnar kulle malika ga dokar da yakafa Mata batasan lokacin da tafara kukaba tatashi dagudu tabar wajan

Yaiyun malika babakin mgn see Ido Dan ko hakuri sun,kasa bawa mahaifin nasu Dan sun San Yana hakuri da mahaifiyarsu kallansu daddy yayi

Yace kutashi muje asibiti muga halin da su Amira suke ciki Amma kusani bazani inda malika takeba ko Kuma bance kujeba du Wanda yaje wajanta ba da izininaba ban yafeba

Jikin,sune yai sanyi Dan yau ran mahaifin nasu yabaci sosai Dan betaba daukan zafi irin yauba akan malika da mahaifiyarsu

Tashi sukayi zuwa asibiti wajan su Amira

Aliyu Kiran mahaifinsa yai awaya da ummi Suma yagaya,musu du abinda yake faruwa salati abbah yahauyi

ummi kuwa kuka tafashe da shi tace nashiga uku Ni Aisha yanzu sadiya akayiwa irin wannan wulakancin mezancewa iyayanta Allah sarki su Walid bakuyi dacan uwa tagariba malika halinki beyiba wlh na tsaneki tinda bakyasan jinina senasa aliyu yasakeki nagaji Bazaki kashe,min Dana inaji inagani me Mana biyaiya yanzu kiyaiyar da kikewa su Amira har yakai haka daba a idona Kika haifi Amira da Walidba wlh da nace bake Kika haifesuba nawata Kika dauko se Kuma yaran suka dauko kamannin mahaifinsu gaba,Daya alhaji tashi muje muga halin da Yar mutane take ciki da jikokinmu

Shi dai abbah yakasa mgn Dan irin mutanan,nanne wayanda in ransu yabaci basa mgn Amma matakin da ze dauka baya kyau Dan yagama Yanke hukunci wannan Karan zartar da shi kawai zeyi shima abin ya isheshi Suma asibitin suka tafi suga halin da su walid suke ciki

Aliyu komawa dakin da aka kwantar da sadiya yayi yasata agaba Yana kallo se bacci take daga kaga yanda take baccin kasan tanajin jikinta tausayi ta bashi hannunta yakama Yafara mgn shi kadai kiyi hakuri ummu Walid Ni da yarana ne muka jawo Miki tamu kandararce ta shafeki kiyi hakuri karkiji tsoran Zama damu

Bude kofa akayi aka shigo Ashe mahaifin malikane da Yan uwanta har da uwar malika se da daddy yasata Dole ta biyosu badan tasoba Ido yabude Mata yakuma nuna Mata ba mutunci yanuna Mata shifa neman Kai yake da ita intaki sakinta zeyi Dole ta biyoshi yakumace Mata inyaji bakinta yafadi kalmar da be daceba abakin auranta hakuri yakeso tabawa aliyu da iyayansa da yarinyar da akaiwa duka Dole tayarda da sharadinsa badan tasoba

Aliyu yatafi tinani rike da hannun sadiya ahannunsa yakura Mata ido kamar ita yake kallo bema San su daddy sun shigoba se jiyayi andafashi ana Kiran sunansa dogo Kai yayi yaga daddyne da Yan uwan malika da sauri yadurkusa Yana gai da daddy da mommy Yana musu sannu da zuwa suka amsa masa dasauri daddy yadagoshi yahau gaisawa da Yan uwan malika cikin mutunci su du kunyarsa sukeji saboda abinda Yar uwarsu Tai Masa hakuri suka,hau bashi har da daddy da mommy

yace bakomai yashige tambayarsa sukayi yamasu jiki yace da sauki sukace Ina su Amira yace suna Daya dakin sukace arakasu suje suma su gansu kafin sadiya tatashi daga bacci

fitowa sukayi zuwa dakin da su Amira suke suka,hadu da su ummi da abbah sun karaso kunyace takama daddy Yan uwan malika Suma Kai suka dinga sunkuyarwa kasa gaba,Daya akunyace suke Banda mommy ko akanta Dan ita gani take yarta tayi dedai in itacema se tayi abinda yafi haka Dan ita asibitinma da tazo jinta take kamar tana Kan Kaya Dan itama ta tsani ummi da abbah haushinsu takeji gashi Kuma sun hadu gakuma aliyu agabanta jitake kamar taje ta shakeshi Amma Babu Hali daddy yahanata se wani cike cike take kana ganinta kasan ranta abace yake

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button