Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Haka suka shige gaba,dayansu bayan sun gaisa zuwa dakin da su Amira suke suna shiga ummi ta,karasa wajan su Amira ganin halin da suke ciki kawai tafashe da kuka tana Kiran wlh bazata yandaba dakyar abbah da aliyu suka rarrasheta har suka samu Tai shuru Dan su daddy sunma kasa mgn shima hawayene ke ta zubowa a idanunsa Yana Allah wadai da halin yarsa abbahne me karfin Hali acikinsu shine me Basu hakuri Yanadada karfafamusu gwiwa suyi hakuri zasu warke

Mommy nagefe se harara take zafga musu Babu halin mgn ahankali tahau mgn yanda baza,sujiba tace munafukai ahaka Zaku Kare masu San kansu Ni Kun manta da tawa Yar gatacan akulle da tsohon ciki yau ko gobe kunanan Kuna ta jikokinku Allah yasa sumutu kowama yahuta Naga karshan so shima aliyun munafuki ko ajikinshi be da mu da Malika na kulleba se tayaransa yake da yar aiki har wani rike Mata hannu yake daga ganima shi da yarinyar sun Dade da sanin juna Allahne yasan me suke aikatawa shi da ita suna cin amanar malika abayan idanta

Daddy yajuyo yaga bakinta na motsi suka hada Ido yazafga Mata harara yai Mata mgn da Ido tadawo cikinsu Kuma ta,nutsu dasauri takaraso cikinsu tana duba su Amira

Tace aliyu gayamin number dakin da Sadiya take naje Naga halin da take ciki itama Yar Amana

Yace muje na kaiki ummi

Shiga sukayi dakin har lokacin sadiya na bacci ummi ta tsorata ganin yanda sadiya itama ta koma

tace aliyu Allah yakawo maka karshan wahalarnan kandararnan yanzu Dan Allah kakalli yanda Yar mutane takoma lokaci Daya tahau kuka kaima kaga yanda kakoma du kayi zuruzuru karame saboda tashin hankali wlh nagaji Dole ayita takare wannan Karan lokaci yayi da Ni da mahaifinku mufito da abinda muka shirya waje kowa yaji dolene mu aiwatar da abinda muka tsara aliyu takira sunanshi da karfi yadago Kai Yana kallanta kayarda mune iyayanka mu muka haifeka baka da wasu Wanda yafimu

Yace eh ummi nayarda Mana kune iyayena bani da wayanda suka fiku bani da kamarku

Tace malika zabin kace kaima kasani

Yace eh ummi

Tace to wannan Karan munaso Kai Mana biyaiya azamanmu na mahaifanka muma mun,maka zabin ranmu ka jiramu Ni da abbanku zakaga kome nake nufi aliyu zakayi alfari da mu zakayi farinciki Kai dai kayi mgn biyaiya yanzu banaso Kai mgn ko ka tsananta tinani ko bincike Kan mgnta kajira zakaga me nake nufi kadai Mana alkawari bazaka bijire manaba Kai bayaro,bane kasan me kake to inaso Kai Mana biyaiya azamanmu na iyayanka

Shuru aliyu yayi can yace ummi Ni aliyu danku namuku alkawari zanmuku biyaiya har karshan rayuwata Kuma kowana hukunci kuka aiwatar Akaina zanyi biyaiya sau da kafa azamana na Dan cikinku

Ummi tace Allah yaimaka Albarka

Yace Amin ummi

Tinani yatafi shifa begane me ummi take nufiba kanshi yadada daurewa kawai yabar mgnar yace ai koma menene Ni dansune bazasuyi min abinda ze cuceniba Allah yasa naji alheri

 

 

 

Nikuwa nace ameeeen aliyu

 

 

 

 

 

 

 

 

Godiya ta musamman ga masuyimin comments kunayi Ina Jin Dadi masoyana comments dinku shine karfin gwiwata Ina sane da ku masoyana

 

 

 

FREE BOOK
Bana siyar wa bane duk Wanda ya siyar ban yafe ba

 

 

 

 

 

 

 

 

New writer’s

Hakan take

*Husba’ahfama* ????????????

*Yar* *kwaliya* ???? ????????

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????????
????????????

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????

????????????????
????????????
????????????

 

 

???????? *HALEEMATUS* *SADEEYA* ????????

 

Written by *HUSBA’AHFAMA*

 

IG **officiall_husba’ahfama*
Facebook *Real* *husba’ahfama*

Follow me on Wattpad @ *Real* *husba’ahfama*

 

 

*Bismillahir* *Rahamanir* *Rahim*

 

 

 

 

Shafa Umar
Khairat isiyaku

Inayinku????inaji daku kunayi inajin Dadi godiya???? ta musamman da jinjinar ????????ban girma agareku???? Allah yanar kauna

 

 

 

 

 

23-24

 

 

 

 

 

Ummi da aliyu suna cikin mgn sadiya ta farka da salati tana kuka tana cewa umma kizo ki tafi da Ni zasu kasheni zasu lalatamin rayuwa waiyo Amira da Walid zasu kashesu tadiro daga Kan gado zata fita waje da gudu kafin ummi ta karasa wajanta aliyu har yakarasa da gudu yarikota tana fusgewa tana cewa Dan Allah kuyi hakuri karku cutar da mu wlh Zan bar gidan

sunan Allah aliyu yake Kira danshi tadada rudashima gaba,Daya addua yafara Mata Yana tofa Mata yaga tafara nutsuwa sunanta yakoma Kira sadiya nine muna tare da ke Ni da ummi Kinga ummi gabanki kin ganni Babu me tabaki su Amira nanan lfy Suma ne manki suke tin dazu suka tashi Ido tabude takura Masa Ido taga aliyune yariketa hawayene yafara zuba a idanta takalli ummi taga tana kusa da ita tarike Mata hannu alhamdulillah tahau fada afili takalli aliyu

tace inah su Walid Basu kashesuba ko wlh nakasa karbarsu sunfi karfina sawa sukayi aka rikeni nakasa zuwa na karbesu har rokwansu nayi Ni su dakeni su barsu wlh sukaki yarda Dan Allah kayi hakuri nakasa Kare amanar da kuka bani

Murmushi yafara Yana girgiza Mata Kai yace Baki da lefi ninema me lefi da naki kareku da wuri har haka tafaru Dan Allah kiyi hakuri haka bazata Kara faruwaba

Bakin gado yakaita tahau ta zauna

ummi tace sannu sadiya kinji Allah yabaki lfy Dan Allah kiyi hakuri Kinga har kin cire Karin ruwan da ake Miki se ankira an gyara Miki yanzu Bari nahada Miki ruwan wanka kiyi kafijin dadin jikinki se kici abinci

Kai sadiya ta girgiza tace aah ummi gidanmu Zan tafi wlh tsoro nakeji kasheni zasuyi in banbar gidanba har handi wasu suka kusa ketamin ta fashe da wani irin kuka me cinrai

Ido aliyu yarintse besan sanda yadanki wata kwalbar magani da ke gabanshiba da karfi ya danketa seda ta tarwatse ahannunsa tafashe hannunsa yahau zubar jini idansa yakada yai jajir jikinshi yahau rawa ran yanmaza yabaci ko zafinma bayaji

Dagudu ummi Tai kansa tana salati bude kofar akayi aka shigo Ashe su abbahne da daddy

abbah yace subahanallahi meyake faruwa aliyu Kai aliyu Kama hannunsa yayi yazaunar da shi Kan kujera yakalli ummi me aka dada Masa kinsan yadade beyi hakaba kinsan se ransa yayi mugun baci yake haka addua yahau tofa Masa Yana Kiran sunanshi jikinshi har yanzu rawa yake kayi hakuri kaji aliyu

Ummi tace Ni Kar wani ciwan yakamashi kayi hakuri Dan Albarkar kaji kirari tahau yimai kamar wani sarki aliyun ummi da abbah kaga damo sarkin hakuri aliyu Zaki aliyu gadanga kaga haidara Jan Zaki kaga samaza gudu Dan dole kaga Dan gidan ummi me farin jini daga Allah aliyu ikwan Allah aliyu bawan Allah alyu Dan Albarkar Kai jarimine komai yai farko Yana da karshe insha Allahu Kuma karshanma yazo se dai labari kaga Dan halak Dan ummi da abbah kaga Dan gatan umminsa da abbansa

Murmushi yafara yabude Ido Yana kallan ummi yaga hawayene itama yake fita a idanta rungume kansa tayi ajikinta tana shafa kansa jiyayi zuciyarsa tayi sanyi wata nutsuwa na shigarsa nunfashi yahau mayarwa ruwan hawaye yahau zuba a idansa har yanzu jinine yake zuba ahannunsa

Abbah yace alhamdulillah Bari Akira likita yaduba hannun nashi Ashe sadiya tatashi sannu kinji Allah ya baku lfy fita yayi Kiran Dr

Kai sadiya ta sunkuyar tana mamaki me akayiwa aliyu yake irin wannan abin haka har da Jin ciwo

Ummi hamdalah tahauyi azuciyarta tana farinciki azuciya tahau mgn lanlai aliyu yadamu da sadiya yanaji da ita tinda har tafadi wannan kalmar ta ankusa keta Mata handi tasashi yin haka lanlai sadiya tazama wani bangare na jikinshi Dan in kaga aliyu yayi irin abinda yayi yanzu to lanlai bacinran yakai bacinrai Kuma abin na da mahimmanci awajansa lanlai hadin da zamuyi bazamusha wuyaba Kuma baza asamu matsalaba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button