Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Daddy na gefe Yama kasa mgn shi yasan me yakeji azuciyarsa yasa su mommy su koma gida se shi da banban wan malikane yarage Basu tafiba suka tsaya

Abbahne yadawo shi da Dr da wasu Nurses maza guda biyu hannunsu rike da Dan kwanansu na asibiti Dr yace sadiya kin tashi sannu Bari na duba yayanki kafin na dubaki yallabai

Hannun aliyu yakama Yana dubawa ummi tamatsa gefe gaisheta yahauyi ta amsa me yasameka haka yallabai shidai har lokacin beyi mgnba kansa na sunkuye

Ummi tace yankewa yayi da kwalbar magani

Allura Dr yai Masa yasa Nurses din nan da suga shigo tare suyi masa dressing din hannun na shi sannan yaduba sadiya yayi Mata tambayoyi Kan jikinta yarubuta Mata magani yarubuta na aliyu shima yabawa abbah
yace aje akarbo musu su Fara anfani da shi da dandare sannan se da suka Gama gyara hannun aliyu sannan suka fice lokacin ana Kiran sallah Suma su abbah masallaci suka tafi Yana rike da hannun aliyu suka fice

Ruwan wanka ummi tahadawa sadiya tayi tadauro alwala sannan tafito tatada sallah ummi itama alwalar taje tayo tatada sallah bayan sun idar ummi ta hadawa sadiya shayi mekauri tabata Tasha tabata abinci taci duda bataci abincin da yawaba

Sadiya tace ummi Ina su Walid

Tace suna dakin da suke Suma ke suke ta tambaya Bari naje Naga ko har yanzu idansu biyu se na rakaki muje

ummi nafita se ga aliyu yaturo kofa yashigo shikadai babu su daddy yaga sadiya zaune Kan sallaya suna hada Ido da shi Tai saurin sunkuyar da Kai Baki na rawa

Tace yallabai yahannunka

Murmushi yayi beyi mgnba ta daukama baze amsaba can taji

yace dasauki yakikejin naki jikin yanzu

Tace alhamdulillah Dan Allah ka rakani wajan su Amira nagansu hankalina zefi kwanciya

Yace kema kina bukatar hutufa Dr yace Kar adameki abarki ki huta

Raurau Tai zatai kuka har idanta yaciko da kwalla mamaki ta bashi

Yace aah bafa hanaki zuwa zamuyiba zomuje

Shima karfin Hali yake kansa ciwo yake Masa hutu yake bukata haka suka fito suna tafiya shi Yana gaba ita tana baya yaransa na ganinsu suka hau yiwa sadiya yajiki suna take musu baya taamsa musu dasauki suna shiga dakin da su Amira suke sukaga Suma kuka suke zasu wajan sadiya da gudu sadiya ta karasa wajansu kafinma ta karaso sun diro daga Kan gado sun rungume sadiya suna murna se mayar da numfashi suke

ummi jitayi dukansu sun Bata tausayi tace malika kin cucuci kanki kinyi babban kunkure arayuwarki Ina jiye Miki gaba lokacin da zakiso yaranki lokacin sun manta da ke gaba,Daya

Aliyu Kallan su yake Yana murmushi yanajin Dadi azuciyarshi ahankali yace yaro kenan du inda ake kyautata Masa Nan yakeso nayarda da ke har cikin zuciyata ko bananan Zaki rikemin yarana hannun binbiyu Zaki kula da su tsakaninki da Allah na gwadaki ta ko Ina ban kamaki da lefiba

Muryar sadiya da su Amira yaji suna ta dariya

Sadiya tace meyake muku ciwo yanzu

Walid yace Ni jikina du ciwo yake Allah banasan wannan matar da daya matarnan malika da nusaiba yake nufi su ka Mana duka mu da ke muna Basu hakuri su Dena dukanki sukaki wlh in na girma nazama soja dukansu se na harbesu da bindigata

Sadiya bakinshi tarufe tace Babu kyau karka Kara fadar haka kaji Kai me kirki nakeso kazama meyafiya kaji Allah nasan me yafiya in anmasa left

Kafin yai mgn Amira tace wlh Nima bana sansu banasan ganinsu sun kusa kashemu in nagirma nai kudi bazan basuba Nima Allah mommy kibar Walid yaharbe mana,su

Kai sadiya ta girgiza tace ke macece ansan mace da tausayi karki Kara fadar haka kema kinji du kanku kuyi hakuri kunga Nima na hakura Allah ze bamu lada

Shuru kawai suka Mata sukaki cewa komai

 

Nece hm sadiya mgnar Nan tafi karfinki

 

Ummi tace to yanzu tinda kunga juna Kuma ku su Amira ruwan da akasa muku yakare ancire muku muje nai muku wanka kwaji dadin jikinku ke Kuma sadiya ki koma naki dakin da kike Kar Dr yazo bakyanan

Su Amira sukace mu dai binta zamuyi

Sadiya tace ummi

Ta amsa sadiya menene

Tace Ni na warke Dan Allah kuyi hakuri gida Zan tafi yanzu inaso Naga ummana kiyi hakuri ummi bazan koma wannan gidanba Dan Allah karki hanani ki,barni na taba yanzu Zan gane gida

Aliyu jiyayi hankalinsa yatashi bema San lokacin da yaja kujera yazaunaba yazubawa sadiya ido Dan shi Yana hango irin tashin hankalin da yaransa zasu shiga in batanan kewa zata dada musu yawa Daman itace ta dauke musu ta mahaifiyarsu

Muryar ummi yaji na mgn tace sadiya nasan anbata Miki anci zalinki Dan Allah kiyi hakuri karkice Zaki guji yaranki da mu kanmu ai Daman gidan aliyu kin barshi yanzu ke da su Amira

Dasauri aliyu yace ummi Dan Allah

Tace kazuba Mana Ido kaima kafin muzo kanka ai zata koma Amma da wani matsayi me girma zata koma cikin gidanka Naga me tabata Kuma sadiya dan Allah ko iyayanki karki gayawa Kar hankalinsu yatashi suji tsoro Suki yarda damu Dan in har sukaji me yafaru da ke lanlai nasan zasu kwaceki ahannunmu kuma bazasu Kuma yarda da muba Ido aliyu yarintse yafesar da iskar bakinsa aminu Dan uwanki abbah yamasa mgn Kar yafadawa kowa abinda yafaru da ke a Yan uwanku har mahaifiyarshi munce Kar ya fada Mata in sukaji zasu Dena ganinmu da mutunci Kuma shi aminu yasan kudirinmu yakuma yarda Dan Allah kema kirufa Mana asiri Kika tafi yanzu adarannan ai suna ganinki sunsan ba lfy Kuma kin manta suwaye kishiyoyin mahaifiyarkine kema kinsan me ze faru in kintafi gida yanzu a darannan wajan karfe Tara yanzu nadarefa gidanku Zaki Amma ba yauba se kin warke nicema Zan kaiki da kaina ki gansu ki musu kwanaki har da yaranki zaku tafi tare zakuyi kwanakin da zakiyi lokacinne zakiyi komawa gidan aliyu tamusamnan kidada hakuri kinji Kinga yaranki har sun Fara kuka da sukaji kince Zaki tafi Kuma Kinga ko abinci sunki suci da yawa sunce se kinzo zasuci yanzu Bari nai musu wanka se ki sasu suci abinci kema se kije ki kwanta

Numfashi aliyu yajah me karfi yabude Ido ahankali Yana kallan sadiya da ta sunkuyar da Kai tana hawaye

Tace to ummi ke mahaifiyatace bazan Musa mikiba nadena Kuma Babu Wanda Zan fadawa na miki alkawari amma Ni anan Zan kwana tare da su Amira bazan iya kwana adakin canba

Ummi tace to likita aiki yasameku kaji aliyu se kaje kafadawa Dr karyaje can be gantaba

murmushi yayi yace
Uwa da ya’yanta

Murna su Amira suka Kama suna Jin Dadi sadiya zata zauna da su

Su abbahne suka shigo dakin da sallama suka amsa sukace Ashe dukanku Kuna Nan ai munje can dakin da Sadiya take munga ba kowa Kai aliyu wajanka muka dawofa kasa,memu awaje

Suka fita yabisu abaya inda motocinsu suke sukaje abbah yace Kai aliyu munje can police station Babu yanda bamuyi da suba sunki kulamu sunce case din su malika na hannun kawunka tinda shine kwamashinan yansanda Kuma shiyace du Wanda yazo Kar asaurari kowa in ba kaiba Kuma wata daga cikin Mata yansandan tace malika Bata da lfy kamarma nakuda take nakira number kawunka ban sameshiba yanzu azamana na mahaifanka kazo muje kayi mgn afito da malika ita kadai inah neman alfarmarnan in dai Ina da matsayi awajanka azamana na mahaifinka muje afito da ita mu kawota asibiti Kar ta haihu awajan ko Dan da tahaifa in yagirma yaji labarin abinda ubansa yaiwa mahaifiyarsa da cikinshi ta haifeshi awannan waje baze yafe makaba zeji haushinka

Daddy yace alhaji idiris Wai Dan Allah meye naka na damuwa da wannan Mara mutuncin yarinyar ka barta tamutuma awajan karewar haihuwa nifa abinda aliyu yayi yamin dedai ko nine abinda zanyi kenan nifa Kaine kamatsa,min Dan kahadani da Allah da wlh wlh Babu abinda zanje nayi ko da mutuwa tayi Kai aliyu tafi gida kahuta Babu inda zakaje indai Nima mahaifinkane kar kaje kasa afito da ita shige katafi gida kahuta se da safe Nima alhaji idiris kaga tafiyata daganan wlh Babu inda Zan Kuma zuwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button