Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Mota yashiga dansa yajashi suka tafi gida yabar aliyu da ababah awajan

Abbah yakalli aliyu yace shiga mota mutafi aliyu

Aliyu yace Dan Allah abbah kayi hakuri bazan,jeba in da abinda na tsana shine nakuma ganin wannan matar ko sunanta banaso Akira agabana Zan Kira kawu ko zuwa gobene zaa saketa tinda kasa Baki ammafa se munyi sharia da ita

Abbah yace aliyu kadubi darajar mahaifin malika da yaran da kuka Haifa tare da Kuma tsohon cikin da ke jikinta karaga Mata ai ko alahira wani nacin albarkacin wani ko Kun rabu Baku rabuba su Walid sun hadaku Babu yanda zakayi karkaga Dan ran mahaifinta yabaci yayi fishi da ita kaga kamar be damu da yarsaba yanasan yarsa halinta yatsana Kuma kasan Yana da kawaici Akan yarsa baya taba goyan bayanta to kaduba darajarsa kaje kasako malika mu kawota asibiti

Aliyu badan yasoba haka yashiga mota suka tafi da abbah har police station yai mgn yanaso asaki malika zasu kaita asibiti aduba lfyarta sukace to Bari aje afito da ita yansanda Mata guda biyune suka fito da ita se cije cije take daga gani kasan tanajin jiki ga cikin yadawo kasan maranta da Kar take tafiya har mota suka sata abbah se sannu yake Mata aliyu ko kallo Bata isheshiba kau dakai gefe yayi Babu yanda abbah be da Shiba yashiga baya yakula da malika aliyu yaki yashige gaban mota yahade Rai ko juyowa yakiyi yaga halin da take ciki yaki abbahne yazauna abaya tare da ita direba yaja suka tafi suna isa asibiti tinkafin mota tagama tsayawa yabude yafece yashiga motarsa direbansa yaja yaransa nabiye da su abaya suka fice daga asibitin

Kai abbah yagirgiza yace lanlai ran yanmaza yabaci indai aliyu yai irin zuciyarnan Babu me iya shawo kansa tin Yana yaro kome zaai,Masa baze saukoba baya fishi se ankaishi makura malika kinkai aliyu bango Allah yakyauta

Abbah Dr yakira awaya yace ga Mara lfy mace yakawo tana mota yaturo Masa Nurses Mata su shiga da ita Babu Bata lokaci sukazo suka shiga da ita Dr naganin halin da take ciki yace ashige da ita dakin haihuwa adubata suna dubata sukace haihuwace da baa kawota da wuriba komai ze iya faruwa

Abbah Kiran daddy yayi awaya yace yadubi girman Allah yazo yaga halin da yarsa malika take ciki gasu a asibiti in bazezoba yaturo mahaifiyarta da Yan uwanta suzo su ganta zataji Dadi

Shuru daddy yayi yace alhaji idiris wlh kana matsamin Akan yarinyarnan nidai wlh adai yau bazan zoba se dai na turo Mata Yar uwarta mace guda Daya Ni da mahaifiyarta se gobe da safe zamuzo shima Dan zamu duba su Amira shiyasa zamuzo kafinma abbah yakuma mgn yakashe waya

Abbah yace Allah yakyauta Kiran aliyu abbah yayi awaya yace ran dangidan ummi yadade atemaka abawa wani Kayan da malika da yaro zeyi anfani da shi in tahaihu tinda kayanta har yanzu na gidanka itama tace aduba dakinta tahada komai daukowa kawai zaayi katuro akawo Mana bacewa nai kakawo da kankaba umarni nabaka kasa akawo kafin aliyu yayi mgn abbah yakashe wayar

Dan yasan in bahaka yai masaba baze turo da kayanba Kuma inyace yakawo da kanshi ko yacemai to bazuwa zeyiba

Abbah dakin da aka kwantar da su Amira yakoma yasamu ummi na Hira da su sadiya yai sallama yashiga suka amsa yace alhamdulillah jiki yayi kyau sannunku Allah yakara sauki

ummi tace ameeeen

Yace ummin Yara ko nace ummin sadiya inasan ganinki Ina jiranki awaje

dariya tayi tatashi tabi bayansa zuwa waje ganinshi tayi yana jiranta akofa tace alhaji lfy kuwa

Yace to lfyar kenan yagaya Mata halin da malika take ciki da yanda suka je suka karbota da yanda sukayi da daddy da aliyu

Ummi tace hm malika kin Gama cutar kanki yau kece kike nakuda kina dakin haihuwa aliyu nagarin Amma bezo ya tsaya awajan,kiba yaron dashi ake shiga dakin haihuwa Yana tsaye Kan matarsa har se tahaihu yaro mesan Yara da matarsa kinsa Masa tsanarki azuciyarsa aliyu ne yau yake gida be damu da alin da kike cikiba lanlai kinkai aliyu bango Allah yakyauta Bari naje Naga halin da take ciki Kwanan asibiti yakamani Dole ga su sadiya ga Kuma malika

Inda malika take ita da abbah sukaje lokacin babban yayar malika har takaraso gaisawa su kayi

ummi tace nana yake ciki yanzu kin shiga kin ganta

Tace sun hanani shiga sunce najira haihuwar tazo insha Allahu yanzu zata haihu

Ummi tace to Allah yasa muji Alheri

Wajan awaya Daya wata Nurse tafito daga dakin haihuwar da sauri su ummi sukai wajanta suna tambayarta yajikin malika tahaihune

Tace alhamdulillah komai yayi dedai Allah yasauketa lfy tasamu baby girl ammafa mejegwan Tasha wuya dan tazubar da jini Dr yace tana bukatar hutu abarta ta huta Kar adameta

Hamdalah suka,hauyi se lokacin kowa hankalinshi yakwanta karkuso kuga murna wajan abbah

Anfito da mejego zuwa wani dakin su ummi dukansu suka shiga ganin baby malika na ganinsu tajuya baya tarufe Ido

Yayar tatace ta dauki yarinyar tabawa su ummi abbah yakarbeta yai Mata huduba yamikawa ummi takarba tana ganin yarinyar tana murmushi kamar malika tadauko yarinyar ummi ta karasa inda malika take

tace sannu malika Allah yabaki lfy yaraya abinda Kika haifa yanzu me yake da munki

Wani dogwan tsaki malika taja Taki mgn

Nana yayar malika tace meye haka kefa iskacinki yawane da shi ummi kikewa tsaki Dan Baki da mutunci ba uwar mijinki bace ko Baki santaba ai ta haifeki ke du wanan halin da kike ciki be isheki isharaba har yanzu mugun halinki yasa ko mijinki bezo yaga halin da kike cikiba gasu daddy Babu Wanda yazo ga daddy yayi fishi da ke Amma ko akanki banza Wanda batasan ciwan kantaba wlh kin Riga da kinyi nisa malika bakyajin kira takalli ummi Dan Allah ummi kiyi hakuri Dan Allah badan itaba

Ummi Tai murmushi tace bakomai nana kinsan Bata Gama warwarewaba mubarta ta huta kema kidena Mata wannan fadan ya Isa haka Ni Zan tafi Allah yaraya se zuwa safiya in Allah yakaimu Zan shigo Tamika Mata yarinyar tace taja musu kofar

Nana zata dada mgn

Abbah yadaga Mata hannu yace ya Isa karki Kara mgn kirabu da ita Nima gida Zan tafi tinda Allah yasauketa lfy Kuma Naga abinda ta Haifa se Kuma gobe da safe in Allah yakaimu zan shigo

Kafinma tayi mgn har yafice Dan yaji haushin yanda malika taiwa ummi

du kunya ta kama nana tace kedai malika kinyi asara wlh mutanan da suka tsaya Kai da fata du da kece me lefi suka fito da ke daga wajan yansanda da yanzu awajansu Zaki haihu suka karboki suka ceci rayuwarki Amma Dan Baki da mutinci Kika yimusu Haka harshi abbah da yake Miki yajiki Allah yaraya Baki amsa masaba Dan wulakinci Wai me kikeji da shine me Kika dauki duniya wlh Nima in Kika batamin Rai zantafi na barki kitashi kiga kalar abinda Kika haifa kibata tasha tin dazu take neman abinci

Malika tace wlh wlh anty bazan ko taba,taba bare har na shayar da ita su walid ma ban shayar da suba bare ita da ta,jamin matsala da dama tinda nasamu cikinta farinciki yaimin kaura arayuwata wlh ko kalarta banaso nagani ubanta yaja Mata du wani Wanda yake da alaka da aliyu wlh wlh na tsaneshi ko ganinshi banasan nayi Ni da Zaki temaka ki fadawa wannan munafukar tsohuwar uwar tasa da munafikin tsohon ubansa karsu Kara zuwa inda nake bana San ganinsu wlh na tsanesu ai komai aliyu yai min da saninsu sune suke sashi yai min sun tsaneni basa kaunata Dan haka Nima bana kaunarsu ke in Zaki shayar da ita gaki gata kibata Tasha gobe kije kibasu jikarsu har gida kikai musu ita karma susha wahalar zuwa Nan wlh bazan raini jinin aliyuba ubanta yajawa jinjirar ko wannan munafukar tsohuwar tashayar da ita ta raineta har tagirma na bar Mata ko shi aliyu yadauka yabawa karuwar Yar aikinsa tashayar da ita Amma bani malika wlh

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button