Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Kuka nana tafara tana salati tace nashiga uku Ni Nana yau Naga abinda yafi karfina Anya kuwa malika kina da imani kekuwa musulmace Anya kuwa ke jinin daddyce wana irin zuciyar kafircine da ke malika Yar da Kika haifa acikinki zakiwa haka ko jinin haihuwa be Gama daukewa daga jikinkiba radadin zafin haihuwa be Gama warkewa ajikinkiba ki tuna har Ranki Kika kusa rasawa wajan hihuwar yarinyarnan bakaramin jini Kika zubarba ai in sone wannan jinjirar ita yadace kifi kaunarta fiye da kowa da komai arayuwarki Amma Dan ke dabbace itace Kika tsana bakya,santa shi Kenan na barki bazan Kara fada Miki gaskiyaba wlh da Baki taba haihuwaba da nace balefinki bane bakisan darajar ya’yaba to karewama kece Kika haifi yarinyar da kanki Ni nazare hannuna daga lamarinki kwanama awajanki darajar wannan baiwar Allah da batasan komaiba aduniya Zan kwana Dan nakula da ita Dan innayi zuciya yanzu natafi gida Zaki iya kasheta tinda ba kaunarta kikeba kin fada da bakinki Ni inasan yarinyar Zan roki aliyu yabarmin ita na raineta Allah yaraya,min ita Zan Bata kulawar da du wata uwa tagari take bawa danta tadada rungume yarinyar ajikinta tafashe da kuka Taki kandarar kenan kenan baiwar Allah kinshigo duniya se hakuri kinzo kin samu duniya da rikici kalakala Ni inasanki Ina kaunarki Allah yarayaki

daya gadan da bakowa akai tahau ita da yarinyar ta rungumeta suka kwanta suka juyawa Malika baya kuka nana take tayi tanajin tausayin yarinyar tasan mommy in tazo bayan malika zatabi Kuma malika tafijin mgnar mommy akan daddy

Malika ko akanta du mgnar da Nana tayi Mata beshiga kunnantaba bare tayi nadama illah shedan da yake dada zugata yake Kara Mata wutar tsanar yarinyar da aliyu azuciyarta baccine me Dadi yadauketa

Nana ita da jinjira azaune suka kwana yarinyar se kuka take tanajin yunwa se dai ruwan zamzam da take ta Bata in Tai kuka tana Bata se Tai shuru har garin Allah yawaye haka suka kwana Ido biyu se da Dr yashigo dubasu malika tatashi daga bacci hankalinta kwance

Abbah da wuri yashigo asibiti dakin da su sadiya suke yafara zuwa aminu na biye da shi abaya da kulolin abinci ahannunsa suna shiga aminu yagai da ummi yaiwa su sadiya yajiki

Yace abbah Bari naje nakaiwa masu jego nasu abincin Awana daki suke

Abbah yafada Masa yafita yaje Kai musu

Bayan sun Gama gaisawa da abbah yaimusu yajiki se ga aliyu yashigo cikin shirinshi yasha manyan Kaya se daukan Ido suke tinkan yakarasa shigowa sukasan shine yazo saboda kamshin da suka faraji Yana tashi danshi maabocin kamshine har kasa yadurkusa yagai da iyayansa su Amira suka gaisheshi yai musu yajiki

yakalli sadiya yace yanzu me yake da munki

Tace bakomai yallabai na warke

Yace alhamdulillah me kukeso ke da yaranki nasa akawo muku yanzu

Tace bakomai ummi da abbah kome mukeso sunyi Mana

Yace yangatan abbah da ummi karfa kuyi,min kwace Dan Naga Kuna Shirin kwacemin fadata

Murmushi sadiya tayi
Tarufe fuska tace ai yanzu mu yangatansune

Murmushi yayi

Abbah yace to tinda kazo kashige muje muga mejego kaga abinda ta Haifa Daman Kai nazauna jira tin dazu mahaifin malika yazo yashigo yaduba su Amira Yana waje Yana jirana ban saniba ko Kun hadu shima Nina hadashi da Allah yatsaya hajiya tashi har da ke zamuje

Tace to alhaji muje

Aliyu yace zanje Dan darajar jinina da tahaifa Ni yarinyar zanje gani ba wannan matarba

Abbah yace hakanma yayi muje

Sadiya ita tinda suka Fara mgn Bata gane me suke nufiba Dan ummi batai Mata zancan malikaba Bata Gaya,Mata ta haihuba har su Walid Bata Gaya,musuba

Ficewa sukayi zuwa dakin da Malika take har da daddy suka shiga atare nana na ganinsu ta durkusa ta gaishesu suka amsa ta mikawa aliyu yarinyar yakarba yai Mata addua yakurawa yarinyar Ido jiyayi hawaye na niyar zubo Masa tausayin yarinyar yakeji yamikawa daddy ita ya karba

Yace tubarkallah Masha Allah amaryata to yanzu wata zaba acikin Ni da abban su aliyu

Dariya sukasa abbah yace Ni na barmaka tawa matar ta isheni

Se lokacin malika Tai mgn tace daddy ina kwana

Yace Ni kadai Kika gani nashigo bakiga sauranba

Alama abbah yai Masa yayi shiru Kar yai Mata mgn

Kwafa daddy yayi

Kai malika takawar tana mgn ciki ciki ana haka mommy tashigo Babu sallama Babu Wanda taiwa mgn Suma Basu Wanda yakulata se huci take

Mommy tace to wance ake ciki nazo tafiya da yata zanje gida na kula da ita Dan munyi mgn da Dr yace yau zaa sallameta

Daddy yace ai bakece kike da iko da itaba mijintane yake iko da ita Dan haka gidan mijinta zata shige

Malika tace wah waini malika aini da aliyu har abada munrabu rabuwa ta har abada Dana koma gidan aliyu gara namutu se dai akai gawata Babu aure tsakaninmu da shi yasakeni agaban mutane ya wulakantani yaimin saki Daya Daman ku nake jira kuzo ayi komai agabanku Dan kuzama sheda so nake aliyu yakarasa cikashe,min saki biyun da yarage tsakanin Ni dashi Dan nasan nabarshi har abada Kuma yarshi wlh wlh bazan riketaba kakarta ummi tatafi da ita ko shayar da ita bazanyiba Ni ko kalar yarinyar ban ganiba Dan bana naSan ganinta kwatakwata ummi tashayar da ita aliyu ga mahaifanka agabanka ka cikamin saki uku na abbah kusa Baki murabu da shi ta ruwan sanyi

Mommy tace kin min dedai Yar halak ku muke saurara

Wani mahaukacin Mari daddy yadauke mommy da shi yajuya yadauke malika da wani Marin yace ke rukaiya in ita Bata da hankali kema Baki da shine ke da zakiyi kokari muhadu mu gyara tsakaninsu shine Zaki hau zigata

Abbah yace kayi hakuri alhaji mubi komai ahankali ke malika kiyi hakuri saki dayanma yaisa Allah yadedaita tsakaninku Nan gaba

Malika tace wlh Ni bazan yardaba gara nasan mun Gama rabuwa aliyu in Kai Dan halakne ka haifu cikin Fatima gatanan agabanka da idiris gashinan shima agabanka ka,karasa min saki ukuna

Mommy tace Kai muke saurara ko zaa kashemu se ka karasa sakin

Ummi tace Wai a Ina ake haka yamata saki Daya Kan ta haihu ta haihu Dan hauka Kuma ace a cika sauran saki biyun da yarage Awana hadisin ake haka

Daddy yace dakata hajiya Fatima kinsan shi jahili du inda yake se yanuna shi jahiline yakalli aliyu yadaka Masa tsawa Kai aliyu kadaiji me sukace in dai Kai Dan halak dinne Kuma Kai kahaifu kakuma San darajar iyayanka kana Kuma jin mgnar manyanka inaso ka haramta auran Malika agareka har abada Dan Allah karkaji kunyata Kai min wannan alfarmar nine Nan nabaka isini

Idan aliyu yakada yai jawur jijiyoyin kansa du sun tashi yakalli Malika yace Ni aliyu idiras dan Fatima Dan idiris na haramta auranki akaina har abada nakuma karasa Miki saki biyun da kikeso yazama saki uku yanda kanwata uwa Daya uba Daya taharamta agareni Haka kema Kika haramta agareni har abada nayi wannan alkawarin tsakanina da ubangiji kuzama sheda su Abbah

Sunan Allah abbah da ummi kawai suke Kira

Malika Buda tasaki tasa shewa tace alhamdulillah Allah yarabani da Kaya zanje nayi rayuwar yanci Ni da haihuwa Kuma se kallo na gamata har abada

Mommy tace alhamdulillah yata kin huta ga yarka aliyu se akara gaba yata bazata rikeba bare har ta shayarma da ita

Karbar yarinyar aliyu yayi yamikiwa ummi ita ta karba yabude kofa yafice daddy da abbah sukabi bayansa Yana fitowa yayanke jiki yafadi ko numfashi bayayi da gudu su abbah da yaransa sukayi kansa da gudu suna Kiran sunansa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button