Halimatus sadeeya

Abbah yace mungode Dr insha Allahu zamu dau mataki Kan matsalar zamu,kula mun Kuma jidadi da baka boye Mana komaiba ka gaya,Mana
Fitowa sukayi daga wajan Dr kowa da abinda da yake tinani azuciyarshi
Daddy yakasa mgn Kai kawai yasunkuyar Yana dafe kirjinshi Dan shi ba yaro bane yasan Dr Yana sane yai mgnar matsalar aliyu agabansa Dan yasan shi mahaifin malikane yafadane Dan inma matsalar daga wajan malikane yaiwa yarinyarshi fada ta,gyara takula da mijinta yasan koshi Dr yasan wacece malika Dan shima Yana haduwa da ita kusan kullin yakuma San irin aikin da takeyi Dan haka yai musu mgnar Dan su gyara matsalar yaransu
Ahankali daddy yace malika kin,gama tonamin asiri kin Gama zubarmin da mutunci abin nakima har da Hana miji hakkinsa in ban muku hukunciba ke da mahaifiyarki bancika Dan halakba rukaiya Allah ya,Isa tsakanina da ke kin batamin tarbiyar yarinya se na,baku mamaki wannan Karan Allah yabawa aliyu lfy
Abbah ne yakewa daddy mgn yaji daddy be amsa masaba yawaiga yaga Babu daddy yana baya yajingina da bango yadafe kirji dasauri yakoma wajansa yarikoshi
Yace haba alhaji abubakar meyai zafi bayan komai yazo karshe kafa Dade kana hakuri shine zaka kasa daure wannan matsalar da Dr yafada Mana Dan Allah kasaki ranka kacire komai aranka Kar wani ciwo yakuma kamaka Kuma kaimafa baka da lfy kasani Akan magani kake shine zakasa wata damuwar aranka yanzu in muka karasa wajan su Fatima kasan itama hankalinta tashi zeyi mu mazane zamu iya daurewa ita macace tana da rauni yanzu zata tada Mana hankiki itama
Daddy yace wlh na daure na daure Ina neman nakasa yanzu wlh kunyar aliyu nake Kuma kunyarku nakeji da wasune da ko kulamu baza suyiba da sun zagemu sun kaimu Kara Dan Allah kuyi hakuri wlh ba irin tarbiyar da naba malika kenanba Dan Allah ku yafemin
Abbah yace haba Dan Allah mubar mgnar baka da lefi ba Kaine kayiba ai munsan komai kaima hakuri kake taho mutafi Kar fatima taji shuru ta biyomu
Hannunsa yakama suka karasa wajan da su ummi suke
Da sauri ummi tace Yaya Dr yace muku
Abbah yace alhamdulillah Babu wata matsala ki kwantar da hankalinki yace anjima kadan ze tashi Amma yace Kar adameshi Yana bacci mutun Daya zaa Bari awajansa kuzo muje mu ganshi mu yanzu muna fitowa Ni da alhaji Garba da idanda zamu keko sadiya wani yazauna da shi ko acikin yaransa wani yakula da shi tinda sadiya ma Bata da lfy ke se ki zauna wajan su sadiya Kinga Babu Wanda na gayawa a yanwanshi hankalinsu tashi zeyi
Shiga sukayi suka samu aliyu na bacci har yadada fadawa tausayinsa sukeji sosai fita su abbah sukayi zuwa inda zasu nana tabisu tace itama gida zata Allah yabashi lfy godiya ummi Tai Mata suka fice
Daga sadiya har ummi ba me mgn shuru sukayi kowa da abinda yake tinani
ummi tace sadiya Dole na nemar muku sallama tinda Naga jikin naku da sauki ko Dan jinjirarnan aje gida akula da ita Ni Zan zauna wajan aliyu ke da su Amira se kuje gida ku huta in da matsalama Dr yazo gida yakara yimuku komai
Sadiya tace Ni nawarke ummi Zan zauna da yallabai ke kije gida da yaran kici gaba da kula da jinjirar kafin mu dawo na tayaki da kula da ita
Shuru ummi Tai tana tinani kome ta tuna se Tai murmushi tace to ba komai Allah yai Miki Albarka Bari na Kira direba yakaini gida wayarki na jakata muje nabaki tin jiya aliyu yabani na rike Miki su ummi sun Kira na dauka mun gaisa kina bacci likacin nace musu bacci kike can anjima ki kirasu ku gaisa Dan Allah karki nuna musu da wata matsala hankalinsu ze tashi
Tace to ummi
Ummi sallama ta nemarwa su sadiya awajan Dr tai Mai bayani yanda ze gane yakuma yarda suka shige gida ita da su Amira saboda jinjirar se kuka take tana Jin yunwa da Kar su Walid suka yarda suka tafi Babu sadiya
Abbah da daddy gidan su sadiya sukasa aminu direban abbah kuma Dan uwa ga sadiya yakaisu sun,kuwa ci sa,a malam na gida yazo cin abinci ya koma akace ana sallama da shi Yara sukace Masa har da aminu akazo da sauri yafito Yana tinanin Babu lfy wani abinne yasamu sadiya tinda har da aminu Kuma Yara sunce da wasu manyan alhazai yazo acikin mota me tsada Yana fitowa yaga su daddy atsaye suna jiran fitowarsa suna ganinshi suka saki fuska suka,hau gaisawa
Malam yace aminu na ganka da Baki se dai ban sheda,suba Ina fatadai lfy Ina sadiya ko wani abune yasameta ko wani lefin tayi Dan Allah ku gayamin
Abbah yace malam ka kwantar da hankalinka Babu lefin da sadiya tayi Kuma lfyarta klau tacema mu gaisheku ko yanzu Kan mutaho muna tare wajanka mukazo da kokwan bararmu se dai mgnar ta zamace ba ta tsayeba
Malam yace alhamdulillah ku Dan jirani Ina zuwa
Cikin gida kuwa Yaran su tala sunje sun tsekuntawa su habi wasu alhazawa sunzo wajan malam da mota me tsada shewa su tala suka saki suka,hau Buda anzo neman auran yaransu
Murna asiya tafarayi Yar tala tace wlh nasan alhaji nane yaturo neman aurena Daman yace bazata zemin
Lata tace se mu masu ya’ya,mata masu farin jini daga Allah wasu kuwa masu bakin jini aure se dai suga anayi ai Daman in kaga manya masu kudi sunzo sunyi sallama da malam kowa yasan neman auran yaranmu Mata akazo yi ko sirikansane da yabawa ya’ya suka sukazo gai sheshi masu kudi ai se yaranmu wasuma ko talakan su samu yazo yarufa musu asiri yace yanaso anrasa babu me cewa yanaso saboda mugun halinsu uwa munafurci ya’ munafurci Allah yasa Kar yau bakinciki yakashe wasu tinda ba neman auran yarsu akazoyiba
Shewa sukasa har da tafawa suka,saki Buda
Umma na jinsu Bata fitoba ita batasu tskeba kewar sadiyace take damunta sotake tasan halin da take ciki Dan tin mafarkin da tayi akan Sadiya yau kwana uku kenan hankalinta yatashi gashi takira wayarta ummice ta dauka tace Mata tana bacci hankalinta be kwantaba har yanzu
Ashafin baya nayi mantuwa wajan Reza da Yar gidan habi ba asiya baceYar habi faridace Yar habi hauwa Yar lami asiya Yar tala ayihakuri da mantuwar da nayi abinne se ahankali ga hidimar iyali gakuma tsufa????????
Ashe kome su tala suke fada akunnen malam yajisu lokacin yazo bude shagwan samarin gidan bekula su lamiba saboda bakin da yayi karasa bude shagwan yayi yaleka kofar gida yacewa su abbah kushigo bisimilah bin bayanshi sukayi zuwa cikin shagwan yashin fida musu tabarma suka zanzauna suka dada gaishawa kannan sadiya ne suka shiga da sallama suka kawo musu ruwa suka durkusa suka gai da su Abba amsawa sukayi
Abbah yace tubarkallah daga gani kannan sadiya ne ko
Malam yace eh
Abbah yace Allah yaimuku Albarka
Bayan kannan sadiya sun fita
Abbah yace malam mgnce me mahimmanci ke tafe da mu da Kuma kokwan bararmu iri mukazo nema agidanka Allah yasa abamu Ni mahaifin baban yaran da sadiya take kula da sune Kuma uban gidan aminu Dan Allah Dana nazo nemarwa auran sadiya mahaifin yaran da take kula da su shuru abbah yayi yanajin kunyar yiwa malam bayani saboda daddy da yake wajan
Murmushi daddy yayi yace ya kayi shuru alhaji idiris nito Bari na karasa
Bayanin irin halin da aliyu yake ciki yayiwa malam har matsalar da Dr yagaya musu Akan aliyu da Kuma kalar matar da aliyu yake aure har suka rabu da yanda take kyamar su Amira da sakinta da aliyu yayi da bashi jinjirar da tahaifa du yagaya Masa se dai be Gaya,Masa wulakancin da su malika suka,yiwa sadiya ba saboda Kar hankalin malam yatashi yaji tsoro yahanasu sadiya har shakuwar da su Amira sukayi da sadiya yagaya masa yakuma Gaya Masa suna Jin dadin Zama da sadiya saboda yarinyar tana da tarbiya