Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Dan Allah kayi temako ka temaki bawan Allah muhadu mu ceto rayuwarsa da ta yaransa mun maka alkawari Babu abinda ze faru mun San halin danmu zakayi alfahari da auran sadiya da danmu aliyu insha Allahu

Malam shuru yayi yakasa mgn can yace gaskiya Ina tsoro nasan halin yau da halinku masu kudi Ni gaskiya bazan iya wannan kasadarba daga ganinku yau nabawa danku auran ya’ta sekace neman Kai nake da ita kenanma sayar muku da ita zanyi tinda ku masu kudine Toni bahaka nakeba na yarda na bawa danku auran sadiya yaje ya wulakantamin ita auran yanzuma yaro yaga yarinya yace yanaso yaaka Kare bare hadasu akayi Babu soyaiya atsakaninsu shi bayaso ita bataso yaje ya karasamin ya’ta bafa ishanshiyar lfyne da itaba har hawan jini take da shi Bakuma yarinya bace Dan bazan kirata yarinya irin Yar shekara shatakwanba tafi haka Dan takusa tslatin ashekara talatin kadanne Babu acikin shekarunta Ni kullin adduata sadiya tayi rayuwar farinciki saboda da halin da tashiga banaso tabar bakinciki ta koma wani bakincikin tsarina Babu auran Dole ayarana bazanyiwa yarana auran Doleba nayi wannan alkawarin

 

Aminu yace wlh malam du abinda kake tinani ba haka bane wlh tinda kaga da kaina nai musu jagora zuwa wajanka baza asamu matsalaba na yarda da yallabai wlh mutunne me mutunci da sanin yakamata zaka ganshi da kansa shima zezo kaganshi Kuma sadiya Yar uwatace baza ahada Baki da niba acucetaba nasan halin da take ciki su abbah sunsan halin da sadiya take ciki Dan Allah ka temaka kayi temako na maka alkawari wlh Babu abinda zefaru se alheri kayarda ayi aurannan ba sai da sadiya zakayiba temako zakayi

Rokwansa sukai tayi suna hadashi da Allah babu yanda ya iya Dole ya yarda saboda su abbah sun cika Masa Ido tsai da ranar daurin aure akayi saboda su abbah sunce da wuri sukeso ayi komai

Daddy yace mu in ka yarda yau alhamis gobe juma,a jibi asabar munaso adaura auran sadiya da aliyu ranar asabar kaga daga yau saura kwana biyu kenan karka damu bamasan komai naka amatsayinmu na iyayan augo da amarya mun dau nauyin komai na Kayan dakin sadiya du zamuyi Mata Kuma gobe zaa kawo lefe da karfe goma na safe in Allah yakaimu mahaifiyar aliyu zatazo yau da yamma tare da sadiya Dan mahaifiyarta ta ganta da yaran da take kula da su zasuzo Suma suga kakanninsu su da Yan uwansu Dan su Saba sosai

Shuru malam yayi yace gunga

Abbah yace Dan Allah karkace kamai nasan me zaka fada ka yarda damu zuciya daya wlh bazamu cucekuba muma iyayene baza muso aiwa ya’yanmu Mata abinda kake tinani munyiwa sadiya Kayan dakine azamanta na yarmu me biyaiya agaremu tafi karfin hakama awajanmu tamana abinda tamu Yar batai Manba wato uwar yaran da take kula da su

Malam yace to shikenan Allah yasanya alheri Allah yabasu zaman lfy ngd Allah yakara Budi

Sukace ameeeen

Daddy yace ga kudin auran sadiya dubu dari saura sadaki ran daurin aure zamuzo da shi

Karba malam yayi yasa Albarka sannan sukayi sallama suka tafi

Cikin gida malam yashiga su tala suka hau yimasa sannu da zuwa Babu Wanda yaamsa acikinsu yashige dakin umma da sallama

Waje yanema kusa da umma yazauna yadade be Mata mgnba Yana tinanin yanda zata dau mgnar da ze Gaya Mata can dai yadaure yace Khadija

Tace naam

Malam yace Dan Allah Zan Gaya Miki wata mgn ko nace nazo Miki da wata mgn Dan Allah ki fahimceni Kuma komai nufin allahne lokacine yazo babu me hanawa ayishi damancan haka Allah yatsara

Nan yahau yimata bayanin yanda sukayi da su abbah Babu abinda yaboye Mata yakuma Bata kudin da suka bada na auran sadiya

Salati umma tahau yi tana hawaye tace malam banki tatakaba nakuma ji du abinda kafada nakuma gane tsorona sadiya tasan da mgnar takuma yarda da izininta akazo neman auranta ko Yaya karfa mukai yarinyarmu inda zata wahala awulakanta Mana yarmu abanza ai aure abin sone bazan kiba matsala nake gudu

Hankali ya kwantar Mata du da shima atsorace yake karfin Hali kawai yake yakuma Gaya Mata da yamma sadiya zatazo da su amira sirikartace zata kawosu sadiya da su Amira bazasu komaba se an daura aure ranar zaa tafi da su

Umma tace to in tazo Zan tambayi sadiya naji in tana sanshi in bataso baza ai Mata doleba amaidq musu da kudinsu Zan Kuma yiwa uwar yaran da zata aura tambayoyi Dan hankalina yafi kwanciya in sunzo tare Allah yasanya alheri Ni adduar da zanyi kenan

Malam yace Ameeen Khadija Allah yaimiki Albarka kina da fahimta Akan mgn in nazo Miki da ita Allah yatsara komai Akan sadiya tin tini bamu Isa mu canzaba sedai muyi Mata fatan alheri yanzu zanje na boye kudinnan Kan sadiya tazo muji ta bakinta Ni Zan koma wajan sanaata

Sukai sallama yafice su lami se zare Ido suke suna hura hanci su gamasu ya’ya Mata suna jira suji malam yace neman auran su hauwa akazo se sukaga malam yafice bece musu komaiba sun Kuma kasa Jin me yashiga yagayawa umma du se jikinsu yai sanyi suka shiga da muwa Baki yamutu sun kasa mgn murna ta koma ciki

Dan malam yayi alkawari du ranar da auran sadiya yatashi se dai su lami suga ana daura aure babu zato Babu tsammani yaga yazasuyi Dan bakin ciki

Su abbah asibiti suka koma Dan suga ya aliyu yake sunje sun tarar yatashi har yatashi yazauna sunji dadin ganinshi da sukayi yatashi yajiki suke Tai Masa sadiya na gefe kanta asunkuye

Daddy yace sadiya sannu da kokari Allah yaimiki albarka yajikin naki

tace da sauki daddy

Abbah yace to aliyu mu zamu tafi gida se zuwa dare in Allah yakaiyaimu zamu dawo muga yajikin naka tinda sadiya na tare da Kai zatana kula da Kai Allah yakara sauki

Ahankali yace Ameeen Dan Allah abbah kutafi da ita Ni Zan kula da kaina naji sauki me zata zauna Tai min da girmana Kuma su usuman nanan kome nakeso zasuyi min base ta zauna da niba itama taje ta huta ngd

Daddy yace Babu inda zata inkayi hakurima anjima hajiya Fatima zatazo ta dauketa zata rakata gida taga iyayanta Kuma da su Amira zata,tafi Suma su Saba da Yan uwanta

Shuru yayi can yace bayau din zasu je su dawoba daddy

Yace bayau zasu dawoba

Suka fice suka tafi

Ido yakura Mata yadade Yana kallanta ita dai kanta na sunkuye Dadi yacika zuciyarta zataje taga su umma tsaki yaja ahankali yafara mgn yanda bazata jiba

yace narasa meyasa ke na kasa tsanarki sema tausayinki da nakeji in na kalleki ke banajin tsanarki da Jin haushinki kamar yanda na tsani sauran Mata ko Dan tana kula da yarana Kuma tana kaunarsu

Tashi tayi ta zuba masa abinci ta kawo Masa tace yallabai ga abinci kaci

Karba yayi bece komaiba yafara ci ahankali

Sadiya ita du atakure take saboda kwarjini da yake Mata indai Yana waje Bata iya sakewa

Se Amma wajan karfe biyar na yamma ummi tazo duba aliyu daganan tadau sadiya su tafi da su Amira suka shigo dakin da aliyu yake da gudu su Amira sukayi Kan sadiya suka rungumeta suna murnar ganinta dariya ita dai take ta musu sannan sukeji wajan babansu suna Masa yajiki

Aliyu yace se da kuka Fara zuwa wajan mamanku sannan kuka Tina Dani ko kunaji mommy sosaifa

Ummi tace ba Dole suji da itaba tinda tana kaunarsu to aliyu tinda Naga jikinka da sauki Zan dau sadiya na kaita gidansu zataje ta gaisa da iyayanta da su Amira zamu tafi nasan su alhaji sun maka bayani in nadawo Nan Zan biyo lokacin su alhaji sun zo Suma da mgnar da zamuyi da Kai sadiya tashi kuje mota ganinan fitowa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button