Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Fita sukayi

Se lokacin aliyu yaiwa ummi mgn yace to ummi Allah yasa lfy yajinjirar take tana shan madarar ko Taki Sha

Tace lfyklau take Kuma tana shan Madara sosai ga yarinyar Bata da rigima se bacci take tinda akai Mata wanka aka Bata Madara Tasha ai Allah yadubi maraicinta

Ahankali yace alhamdulillah se Kun dawo ummi

Fita tayi ta shaga mota suka tafi zuwa gidan su sadiya aminune yakaisu mota na tsayawa akofar gidan sadiya tahau murna tana dariya

Ummi tace anzo gida zaaga umma Dole ai dariya

Kannan sadiya na kofar gida da yaran su tala se gani sukayi su sadiya sun fito daga mota dagudu kannanta sukazo suka rungumeta suna murna suna musu sannu da zuwa yaran su tala dagudu akashiga Kai rahoto wajan su lami

Sallama su sadiya sukayi da suka shiga ummi na tsakar gida sannu da zuwa tahau musu taiwa ummi jagora zuwa dakinta su habi Basuyi musu mgnba se kallan banza suke musu

Bayan sun gaisa ummi tace yau gashi Allah yahadamu Yara sun hadamu zumunci nasan mahaifin sadiya yai Miki bayanin abin slherin da mukeso ahada nazo na dada Miki bayani yanda hankalinki ze dada kwanciya

bayani Tai Mata yanda zata fahinta itama Kuma umma tambayoyi Tai Mata ummi Tai tabata amsa yanda zata gane takuma gamsu hankalinta ya kwanta da auran tayaba da mutuncin ummi tasan insha Allahu sadiya tasamu sirika tagari

Ummi tace sadiya nasan Baki gane me muke tantaunawaba yanzu zamuyi Miki bayani kin tuno alkarin da Kika daukarmin a asibiti da na Gaya Miki da alfarmar da Zan roka awajanki kin Kuma San girman alkawari Daman abinda Zan roka awajanki Ni da abbah da iyayanki mun yake shawarar zamu hadaku aure da aliyu ranar asabar da karfe goma na safe zaa daura muku aure kiyi hakuri abin yazo da sauri na miki alkawari baza,Kisha wuyaba a auran aliyu kinsan waye aliyu Kuma kinsan wuyar da yasha wani abinma a idanki akayi kiji tausayin su Amira ki yarda da auran aliyu munyanke wannan hukuncinne Dan Kar aliyu ya auro Wanda bamusan halintaba Kar tazo tana bawa su Walid wahala in Kinga bakyaso karki cuci kanki ki gayamin Ni uwace awajanki bazanji haushin,kiba

Sadiya mgnar jinta tayi kamar amafarki Wai yau ita ake roka ta auri mutun me kima da daraja da mutunci ita da ko Kare be taba zuwa yace yanasoba Kuma tana ganin darajar ummi tana Kuma Jin tausayin su walid bazata iya cewa batasoba zata yarda da auran aliyu duda tasan yafi karfinta bakuma ajinta bane tasan ko ya,aureta Bata isheshi kalloba zata zauna takula da su walid tana kaunar yaran tana Jin tausayinsu

Tace ummi ku iyayenane du hukuncin da kuka yanke akaina bazanki yardaba Zan muku biyaiya na amince

Baki suka hada ita da umma sukace alhamdulillah Allah yaimiki Albarka

Kayan gyaran jiki da na Sha ummi ta mikowa umma awata katuwar jaka tace gashi daga yanzu afara yiwa sadiya anfani da su Wanda yarage tatafi da shi gidan mijinta da matar da Zan turo kullin zatana zuwa Nan gidan da gyaran da zatana yiwa sadiya har ranar asabar har kwalliya tanayi ranar asabar ma itace zatai wa sadiya da kawayanta kwalliya har da Yan uwanta du Wanda yazo in yanaso ai Masa nasa andinka Kayan anko da yawa du Wanda yazo bikin abashi yasaka kyauta da na maza da na Mata ankwan na kannan amarya da yaiyunta Wanda suke uwa daya uba Daya nasu kalar ankwan daban nasa akai musu ke kuma uwar amarya uwar ango naki Kayan fitar biki da ban du agobe in Allah ya kaimu Zan turo akawo bikin Yar gata da Dan gata Kuma bayin Allah zaayi

 

 

 

 

 

 

Du Wanda ta juyamin labari ko yajuyamin na barshi da Allah du Wanda yacire sunana ko tacire sunana tasa nata ko yasa nashi Allah ya,Isa bazan yafeba littafina bana kudi bane du Wanda yasayar min ko ta sayarmin na bar ku da Allah bazan yafeba anyiminne banji dadiba har yanzu in natina abin na konamin Rai Kuma Wanda yaimin yasan kansa na Kuma barshi da Allah Dan wlh ban yafe masaba labarin da nafi Shan wuyar rubutashi yacire sunana yasa nashi har yanzu abin na konamin Rai bazan yafe masaba

 

 

 

 

 

New writer’s

Hakan take

*Husba’ahfama* ????????????

*Yar* *kwaliya* ???? ????????

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????????
????????????

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????

????????????????
????????????
????????????

 

 

???????? *HALEEMATUS* *SADEEYA* ????????

 

Written by *HUSBA’AHFAMA*

 

IG **officiall_husba’ahfama*
Facebook *Real* *husba’ahfama*

Follow me on Wattpad @ *Real* *husba’ahfama*

 

 

*Bismillahir* *Rahamanir* *Rahim*

 

 

 

 

27-28

 

 

 

 

Umma takasa mgn bin ummi da Ido take tana mamakinta wace irin uwar mijice wanna ita da kanta takawo Kayan da zaa gyara matar da danta ze aura har ta dau nauyin irin wannan Kayan da talissafa zaayi biki da su lanlai Allah yadubi sadiya yadubi irin bakincikin da Tasha na dadewar da tayi batayi aureba maganar ummice ta dawo da umma daga zancan ,zucin da takeyi

Ummi tace iyayan aliyu maza da sukazo neman auran sadiya dazu sun turo da sako Kayan abincin da zaa dafane abikin suka bayar zaa kawo muku yanzu Kan natafi motar Kayan zata karaso Dan Allah Kar kuce komai sunma ce suna da number malam zasu kirashi suyi Masa bayani

Umma tace gaskiya hidimar tayi yawa bazamu karbi kayanba ko malam,ma ba karba zeyiba wannanma da kikayi angode Allah yasaka da alheri Allah yabasu zaman lfy

Kafin ummi tabata amsa aka kirata awaya tace Kun karaso daga Daya bangaran aka Bata amsa to Bari na fadawa uwar amaryar tabada izinin shigowa se ku shigo da Kayan

Ummi takalli umma sun karaso zasu Fara shigo da Kaya

Shuru umma tayi can tace Dan Allah hajiya akoma da Kayan wlh sunyi yawa du da banga kayanba hidimar tayi yawa in na karba malam zeyi fada

Sallamar malam sukaji yashigo dakin suka gaisa da ummi

Yace yanzu su alhaji suka kirani awaya Kun karo ke da su sadiya Kuma sukemin wani bayani na Kayan abincin biki nace musu Dan Allah su barshi bazamu karbi kayanba har turo Nima ayomin siyaiyar Kayan abincin biki Kuma Suma suka turo da nasu Babu yanda ban dasuba bazan karbi kayanba wlh sunki yarda sun kulleni sun tahadani da Allah Ni yau nake tsoro Kuma Albarkar aure muke nema ba kashe Mata kudiba

Umma tace mgnar da nakewa hajiya kenan kashigo

Ummi tace mudai addua da Albarka mukeso kutasa musu azaman auransu wlh Dan munyi wannan hidimar abikin aliyu da sadiya ba komai bane Suma su alhaji sunsan halin da sadiya tashiga na rayuwa gakuma shi aliyu dukansu abin tausayine mudai fatanmu Allah yasa daga sadiya har aliyu karshan wahalarsu kenan Allah yasa farinciki yarufe rayuwarsu ta gaba da zasuyi azaman auransu yanzu kuba da izini afara shigo da Kayan Akira Yan uwa sufara aiki tin yau Kar aiki yai musu yawa

Malam da umma godiya sukai taiwa ummi suna mamakin wana irin mutanene haka masu karamci

izini malam yabawa masu kawo Kayan suka Fara shigowa da buhunhunan Kayan abinci irin su shinkafa taliya kwali kwali manyan bahonane wajan goda shida du cike suke da danyan Naman sah agyaransa kakaji Suma masu yawa du anyanka angyara dafawa kawai yarage ayi jarka jarkar Mai du wani Abu da zaa bukata sun kawo harta maggi gishiri anhado akayan ga lemuka kala kala akwali akai ta shigowa da su har da katan firij akashigo da shi Wanda zaa zuba lemuka suyi sanyi har da ruwan da zaasha du ankawo komai awadace har agama bikin Babu abinda zeyi kadan komai se yaragu kallan ikwan Allah malam da umma suke sunma kasa mgn se dai Ido

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button