Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Tala tace wlh wlh wlh kunji na rantse har sau uku indai Ina numfashi se nayi abinda sadiya tafito daga wannan daular da tasamu se nayi abinda mijinta ze saketa yanda kaf yaranmu Babu Wanda ta auri me kudi irin mijin sadiya dolene itama ta fito ai nayi alkawari ita da aure har abada se dai ta gani anayi andai daura aure ko har aka wulakantamu hmm wlh se mun rama ba se gabanta abudeba mijin nata ze sadu da ita har yaji dadin zaman aure da ita Kuma base da wajanba zata haihu hm muzuba mugani Khadija indai Ni tala inah Raye babuke Babu kwanciyar hankali Kai acikin yanmatan da na haifa se Daya ta aure mijin sadiya indai nice tala malam Ni da Kaine badai Khadijace a idankaba itace mace a idanka hm zakuga me zanwa malam wlh sun tabo Bala,I

Habi tace malam malam munafikin Allah da taalah wlh malam yabani mamaki malam yau shine yanuna bambanci atsakaninmu yanuna uwar gidansa da ya’yanta su yafiso Akan mu da ya’yanmu ko kunSan kudin da na kashe Akan sadiya da Khadija har wata karamar gonata na siyar naba da kudin Akan wani aiki da nasa akayiwa sadiya amma kuga abanza Wai me Khadija take takama dashi wana malami tarike yake wargaza Mana aiki haka wlh gobe ko jibi zanje kauyenmu zakuga me Zan bankowa sadiya da uwarta se gidan mijin sadiya yazame Mata kamar wuta se dakin sadiya da zatayi rayuwa aciki yazame Mata dodo Dole tabar gidan mijinta tashiga duniya

Babu zato Babu tsammani suna ta tantauna yanda zasuga bayan umma da yaranta sukaji sallamar umma tashigo dakin sun tsorata sosai sun dabarbarce gatsoronan a cikin idansu Kuma umma taji me suke fada Dan tadade da zuwa bakin kofar zata shiga dakin taji suna wannan mgnar karfin Hali kawai tayi tashiga wajansu tanuna bataji me suke fadaba tasaki fuskarta

Tace Ashe kunanan ku nake ta nema kwadawo daki ku zauna azamanku na iyayan amarya gaskiya ban yardaba kufito Kuma ayi da ku ga kayanku na auko nakawo muku malam yatura su zilai da marka da zuwaira da suke gidan miji yace suzo ana bikin yayarsu angayawa mazajansu sun barsu har sun tahoma sun kusa karasowa mazajansu sunzo daurin aure ko nace daurin auran yayarsu Kuma yayar matansu Wanda tayi kwantai Taki auruwa dayake mun rike Allah dashi muke takama mun riga mutun munce Allah se gashi sadiya tasamu miji tayi aure miji na kece raini Allah mun godemaka kome ze samu mutun se Allah yanufa kome ze samu bawa se da yardar Allah ze sameshi Allah mungode maka dakai muka dogara Allah Kaine abin godiya koba,hakaba Yan uwana ga Kayan naku da na yaranku gakuma na su zilai suna shigowa abasu Susa sutaya yayarsu farinciki gakuma kudin liki inji augo dubu ashirin kuyi liki dasu kuyi maza kushirya augo da abokansa zasu shigo ku gaisa tinda angama daura aure zasu shigo godiya kuyi maza ku shirya karsu shigo su ganku kacakaca Bari naje naji da baki

Tala tace tafa jimu du abinda muke fada mgnfa ta yada Mana tatafi wlh inaga taji abinda muka fada zamuyi musu Dan haka Tai Mana wannan habaicin kuga Salan munafurci Wai mu aka kawowa Kaya Musa Karku damu Musa mununa muma muna cikin farinciki bayan biki se mu ida nufi

Lami tace Kai Bata jimuba da tajimu da Bazata bamu kayannanba kunsan wawuyace Bata da wayo Musa Kaya kawai mu maze in ma taji ita tasani ayi farinciki damu harkai amarya se anyi damu Dan mu gane gidan muje mu binne abinda zamu binne agidan bayan biki har sadiyar mu badawa ta tsallaka kuyi maza kusa kufito natafi shiryawa

Masu kidan kwaryane suke ta doka kwarya suna Waka se rawa ake cashewa fili aka bawa Yaya uwar amarya tashiga ta dinga takawa ana Mata liki mustafa sojane yashigo yake gayawa Yaya angwaye zasu shigo gaisuwa

aikuwa maroka Mata naji suka amshe suna sanarwa da kyau kowa ya shirya ga augonan shigowa dagudu su tala suka fito ganin augo su zilai jiki narawa aka fito aga wah sadiya ta aura

Shigowarsu ma abin kallone masu daukar hoto se daukansu suke tayi ga masu gidan TV Suma suna ta dauka kana ganinsu kasan nera tazauna

su tala se da suka Raina kansu ganin mijin sadiya Dan Yaya tanuna musu shi gaisawa ake tayi da su aminu na gefe yanawa aliyu bayanin kowa ahankali su lami yanuna Masa yace sune kishiyoyin umma Kuma makiyan umma da sadiya

kallansu aliyu yayi, yayi murmushi yakarasa wajansu abokansa da yaransa suka take Masa baya yasunkuya yagaishesu Suma sauran sunkuyawa sukayi suna gaishesu aliyu kallan yaransa nasuru yayi da Ido yai Masa mgn aikuwa yaciro Yan nera dubu na dubu hamsin yahau raba musu ko wacce daga Kan tala lami habi zilai marka zuwaira ko wacce se da aliyu yasa akabasu aliyu yakalli yaran nasa da Ido

da sauri yaran aliyu yace kyautace daga hajiya sadiya tace abaku sakwan mijinta Kuma zakuji Nan da kwana biyu zakuga abin arziki har gida zaa kawo muku

aminu yace godiya suke ai masoyan sadiyane Yan farin gidane ba bakin gidaba

lami tace kwarai kuwa nicema na Nagoya sadiya tin tana yarinya nake rainanta

tala tace hakane nikuma nice na yaye sadiya tin daga Yaye nake dawainiya da ita tafashe da kuka

habi tace ai Sadiya Yar dakinace komai adakina takeyi

aminu yace dafa ranmu da lfyarmu har sadiya da umma du suna da Rai

tala tace Babu kyau tonan asiri Allah yahana taface hanci

Girgiza Kai aliyu yayi daga bayanan su tala da yanda aminu yake maida musu da mgn cikin mgn yagane sadiya da mahaifiyarta basajin dadin Zama da su lami Dan haka yasa abasu kudi sufaracin albarkacin sadiya da umma

Maroka se kirari sukewa aliyu da abokansa kudi abokan suke tabasu Yan kidan kwaryama haka suke tarera Waka abokan aliyu namusu ruwan kudi

dakin umma suka shiga gaisheta suka gaisa da umma Ido umma ta kurawa aliyu ta ganeshi mamaki abin yabata Daman shine mijin sadiya ikwan Allah aliyu be gane ummaba tashi sukayi suka fita tsakar gida abokan augo suka Fara Ina amarya tafito adau hoto da ita

Dole Yaya tasa sadiya tafito abar kallo takoma masu daukar hoto kanta suka koma daukanta kawai suke tayi Ido aliyu yakura Mata ganin irin kyan da tayi tacanja sosai ahankali yace tubarkallah Shanda iri daya sukasa da aliyu sunyi kyau sosai sundace da juna sosai kasa karasowa tayi Ido yamata yawa se tatsaya ta sunkuyar da Kai kasa aliyune yatako cikin Isa yakaraso har gabanta yakama hannunta suka karasa wajan abokansa yanda abokan aliyu suke ta yaban kyan sadiya aliyu seyaji badadi

dedai kunnanta yasunkuya yace ummu Walid meyasa Baki yafa mayafi babba,ba gashi se kallanki ake tayi aminu yakira yace kakarbo mata mayafi babba wannan yayi karami Wanda ta yafa

murmushi aminu yayi yace angama yallabai

dasauri yakarbo Mata katan mayafi mekyau aliyu yakarba yayafa Mata tafi abokan aliyu suka,hauyi suna ta tsokanarsa Wai kinshinsa yayi yawa shidai dariya yake tayi hotina sukai tayi da sadiya du inda sadiya tasa kafarta Walid da Amira nawajan Suma sunsha kyau sosai kana ganinsu kaga yaran amarya da augo dauriya kawai sadiya takeyi zazzabine jikinta rawar sanyi take tayi aliyu yakula da halin da take ciki hannunta yakama yakaita dakin umma abokansa se tsiya suke Masa suka fice kofar gida suna ta dariyar aliyu suna cewa yafiya kishi da yawa

suna shiga daki su walid nabiye dasu Kai aliyu yagirgiza yakalli su walid yanzu bazaku bar maman nakuba tahuta bakuga Bata da lfyba kuje abbah da daddy suna kiranku tindazu nemanku suke maza kuje waje kusamesu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button