Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Suna wanan zaman Allah yabawa Malika ciki lokacin da tagano tana da ciki bakaramin tashin hankali tashigaba har aliyu yagane ahin da take ciki inda tace Masa ita Bata shirya haihuwa yanzuba zubar da cikin zatayi inda aliyu yace be yardaba yarufe Ido yaci Mata mutunci sosai sannan ta hakura du iyashegenta in aliyu yabirkice Mata mugun tsoransa take kulawa ta musamman aliyu yake Bata inda ita Malika Bata gani kulin cikin zagin cikin take yatakura Mata aliyu irin mutanannanne masu hakuri se ankaisu bango yake mgn in ranshi yabaci kafin kashawo kansa se anwahala wani saban iskanci Malika ta tsira in tafita aiki tin safe bazata dawo gidaba se dare yayi ko tausayin cikin jikinta batayi kawaye takebi yawo daga gidan wannan kawa se gidan wancan kawa se zuwa fati dedai sauransu ko dangin aliyu sunsan irin zaman hakurin da yake da matarsa kullin shine zuwa gida cin abinci wajan mahaifiyarsa hajiya rukaiya in be zoba ze turo direba yakarbar Masa

Cikin Malika yacika wata Tara inda Allah yabata haihuwa me sauki ta haifi santalelen danta namiji kyaukyawa me Kama da mahaifinsa inda ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Malika inda suke kiransa da Walid shekarar Walid Daya Allah yakuma bawa Malika wani cikin inda tayi yunkurin zubar da shi Amma yaki zubewa Tasha maganin zubarwa ta zubar da jini sosai har tana murna ciki yazube Ashe be zubeba se da yai wata biyar sannan tagano Ashe befitaba tayi kuka tayi hauka inda tadau alkawarin tana haihuwa zaa yanke Mata mahaifa Allah yasauketa lfy tasamu yamace inda ranar suna taci sunan mahaifiyar aliyu ana kiranta da amira nannefa ta bijirowa da aliyu maganar zuwa kasar waje yanke mahaifa ita tagaji da haihuwa aliyune yai ta rarrashinta Kan tayi hakuri karta yanke batasan me Allah zeyi nan gababa ama Taki dakyar yashawo kanta tare da Mata alkawarin bazata Kara haihuwaba zekula ko ciki baze Kara shigartaba

Bayan ta sakankance bazata Kara haihuwaba se ga wani cikin yashiga lokacin shekarar Amira Daya da rabi aliyu be saniba taje tazubar ata kaice dai se da Malika tazubar da ciki sau uku daga baya aliyu yakejin labari ranshi yayi mugun baci har kuka se da yayi haka yahakura Dole

yanzu Kuma wannan rigimar da akeyi Akan wani cikin da takara samu in da tayi yunkurin zubar da shi likitoci suka Gaya Mata zata iya samun matsala in tazubar tace ta yarda acire mata likitan da zeyi aikin yasan aliyu shine yakirashi yake fadamasa abinda matarsa take niyar yi shine yacewa Dr Kar ayi Mata aikin gashinan zuwa da Malika tagane aliyu ne yahana azubar Mata da ciki shinefa tin Yana Dubai tahanashi saket har yadawo gida se da yakira mahaifinta sannan yasamu lfy ga Malika Bata da hakuri wajan Zama da Yan aiki Duda ba Zama takeba Amma azabar da take Basu da wulakanci basa iya Zama da ita har su Dade tare bataki takaiwa Dan aiki mariba in yabata Mata Rai du girman mace Dan haka kullin cikin canja Yan aiki take ita yaran natama Bata da lokacinsu kamar ba itaceba ta haifesu ko kwana awajanta yaran basayi sedai sukwana adakinsu da ban Yan aikine zasuna zuwa dubasu da dandare da Basu abinda sukeso

 

Cigaban labarin

 

 

Sadiyace tadawo daga suyar awara daga kofar gida tashigo gida kenan aka kwala sallama Wai ana sallama da hauwa lokacin Matan gidan du suna tsakar gida

Buda suka saki atare sukace kaji inda farin jini yake ko baafita kofar gida tallar kaiba anazuwa har gida ai sallama da su sunfi masu fita da sunan ana Sai da Abu akofar gida yar’albarka maza zokije ana kiranki

Fitowa yarinyar tayi tana wani rangwada tana kararraya adole ita ga me farin jini tafi yayarta farinjini tazo fita lokacin sadiya zata shiga ban daki ta bangaje sadiya ko sannu Tai ficewarta girgiza Kai sadiya tayi tashige bandaki du abinda kishiyoyin ke fada Akan yarta umma tana jinsu ko kala Bata fito tace musuba

 

WACECE SADEEYA DA MAHAIFANTA

 

 

Sadiya yace ga malam Musa da Khadija dukansu haifanfun Yan garin kanone matan mahaifin sadiya hudu da mahaifiyar sadiya wato Khadija itace uwargida ita malam Musa yafara aurowa sunyi auran soyaiya tin saurayi da budurwa mahaifiyar sadiya tana da Yara takwas akwai maza bakwai se mace Daya sadiya kadai Allah yabawa yamace ayaranta sauran duka mazane sadiyace ta uku ayaranta se masu biye Mata

amatan malam Musa lamice tabiyu yaranta bakwai akai akai take haihuwa tana da Mata biyar maza biyu se tabiyu amatan malam Musa tala ita Kuma yaranta shida duka Mata se ta hudu amatansa habi yaranta shida Mata biyar namiji Daya Dan haka suka,dau tsanar duniya suka dorawa mahaifiyar sadiya saboda tana haihuwar Yara maza sun hade kansu sun wareta gefe du abinda suke Mata na bacin,Rai basosai take mayar musuba se sun kaita bango take mayarwa Duda kansu ahade yake Suma atsakaninsu tana hadosu suyi tafada kamar zasu cinye juna zaman taciki naciki tabaka na baka suke wani lokacinma ummuce me fitowa ta rabasu ko malam in Yana gida atsakanin yaransuma Babu hadin Kai bawata tarbaiyar kirki sukaba yaransuba

Du ayaran su lami sadiya itace banba du tagirmi yaran su lami

Lami ta aurar da mace Daya ayaranta Mata talama ta aurar da mace Daya yanzu haka habice take niyar aurar da Tata yarinyar se yanmata biyu da akasawa Rana Yar lami Daya Yar tala Daya

Sadiya har yanzu Babu Wanda yataba zuwa wajanta da sunan zance du kannanta anmusu aure gawasu ana niyar aurarwa Dan haka suka sata agaba da ita da mahaifiyarta da Gori ko zance akazo wajan yaransu se sun yada musu habaici lami da tala sunje wajan wani boka sun karbo maganin bakin jini Dan Kar sadiya Tai aure har abada sun binne wani Kuma sun bada wani ahanya sadiya ta tsallaka Bata saniba itama habi taje tayi nata shinefa hankalinsu yakwanta ahaka sadiya zata kare Babu aure har dariya suke in suka tuna su sukai Mata asiri

Umma mahaifiyar sadiya ta aurar da maza biyu Duda bawani babban aiki sukeba haka cikin rufin asiri suke zaune da matansu babban wan sadiya Wanda yafara aure sunanshi jabir se nabiyu me auren kwanannan yai aure sunansa sunusi se Wanda daga sadiya seshi mesuna mustafa yazama soja kwanannan yashiga bawani babba bane Dan haka su lami suka dada tsanar umma har mazan yaran umma su lami Basu bariba har asiri suke banko musu dayake Allah yafisu Babu abinda yake samunsu ko sadiya da batayi aureba basusan komai nufin Allah bane lokacin tane be zoba in lokaci yayi zatai aure

Malam musu ada Yana da babban shaguna har guda hudu Babu abinda Babu nakayan abinci ba lefi zaa,iya kiranshi me kudi daga,baya karayar arziki tazo Masa komai nashi yakare gidan da yake dashima seda ya saida ga iyali Yana da su yakoma yawan gidan haya daga,baya malam musu akaraba musu gadan mahaifansu da suka rasu shinefa yasamu yasai Dan karamin gida suke zaune da iyalinshi aciki

Har yanzu malam musu bawata Sana,a yakeyi me karfiba Kayan Miya yake siyarwa abakin titin unguwarsu da ke gandun albasa Kuma barike Masa iyalinsa sanaar takeba yanayine kawai Dan rufin asiri Kuma yafi Zama haka Dan haka ko wance amatansa tatashi tafara Sana,a Dan ta tsira da kanta su samu abinda zasuci malam musu abincin dare kawai yake kokari yabawa iyalinsa saboda yawansu masarace zeturo da ita kullin in yafita da kudin hadin Miya wataranma masararce kawai ze turo me girkice zatai cefane da kanta itace zaaci da dandare aci sauran dumame da safe narana sedai ko wance taci da kanta da yaranta Dan haka ko wance takama Sana,a kamar hauka Babu hutu su da yaransu ko wance sotake tafi yar,wanta samu ko,wancansu tana Sana,a wajan kala biyar arana wani su saida agida wani Kuma su dorawa yaransu talla su fits dashi su sukewa kansu komai na rayuwa da yaransu da kudin sanar da sukeyi Amma du da halin da suke ciki sundau bakin kishi sun dorawa kansu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button