Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Amira tace daddy kabawa mommy magani Tasha kafin mudawo bamaso tayi rashin lfy ko Walid

Yace eh daddy kabata kafin mudawo zomuje Amira sannu mommy suka fice zuwa wajan su abbah

Murmushi aliyu yayi shi tausayi su Amira suke Bashi kallan sadiya yayi yaja numfashi yace ummu Walid meyake damunki ko tinanin rabuwa da umma da Yan uwane yake damunki Kinga Zaki dagawa yaranki hankali Dan Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Babu abinda ze faru daga wajena Bari na Kira Dr muna tare dashi yazo yadubaki yabaki magani

Kiran Dr yayi yashigo yaduba sadiya yace zazzabine yake damunta allura zanmata Dan yai saurin sauka ke amarya yau ranarkicefa kike kwance

Murmushi aliyu yayi

Allura Dr yaciro ze Mata sadiya tace Dan Allah karkaimin banaso magani zaka bani Nasha wlh banasan allura tashi tayi zata gudu

Aliyu yarikota yace Dr zokai Mata wata Kara tasaka tarungume aliyu dakyau haka Dr yai Mata allurar aliyu bemasan lokacin da akagamaba

mgnar Dr yaji Yana cewa Ni zantafi nagama Allah yabata lfy kafin aliyu yayi mgn Dr yafice Yana dariya Dan halin da yaga aliyu yashiga lokaci Daya yabashi dariya

Sun Dade ahaka kafin sadiya tatina a inda take cikin kunya tazame jikinta daga nashi ta kwanta Akan gado baadau wani lokaci me tsawoba bacci yakwasheta

Ido aliyu yakura Mata ahankali yafara mgn yace Allah kenan yaukuma wannance matata itakuma koya nata halin yake Allah masani Ina ganin kimarki da girmanki Ina Kuma jin tausayinki bansan meyasaba na yanke aure arayuwata saboda Banga matar da zata birgeniba Kuma Dan du Mata kallan Hali Daya nake musu natsani Mata saboda malika se gashi su abbah sun hadani aure da ke sun daureni sun bani amnarki tinda na dauka dolena na kula da ke Amma badan hakaba da wulakancin da zanwa matar da aka auramin da dakanta zatabar min gidana Allah yatemakeki Ina ganin kimarki saboda su Walid bazan iya wulakan,takiba kina da daraja a idona se kin tare kema zanga kalar naki halin zanga da zabina da nayi abaya yabani wuya da zabin iyayena wannene yafi kwanciyar hankali Allah gani gareka wannan lokacin bazan iya daukan wulakancin ya’maceba

Animune yashigo da sallama yace yallabai ana kiranka awaje

Yace kiramin umma

Yace to

Dasauri yafita yakirata suka shigo tare

Aliyu na ganinta yadurkusa yadada gaisheta yace Dan Allah umma Kar abar kowa yashigo dakinnan Dr yace abarta tayi bacci Kar Wanda yatasheta zuwa anjima in tatashi zazzabin ze sake

Umma tace to Babu me tashinta insha Allahu yallabai Ina maka kallan sani ko nace na sanka Kaine Ali Wanda kataba temakwanmu lokacin da yarinyata tasuma abakin titi kakaimu asibiti aka kula damu kyauta kaima Kai ta hidima damu har direba kasa yakawomu gida

Shuru aliyu yayi Yana tinani can yace eh hakane umma natina

Umma tace to yarinyar da ka temaka itace sadiya gatanan yau Allah yanufa Kaine mijinta nikuma mahaifiyartace

Da sauri aliyu yadaga Kai Yana kallan umma can yace ikwan Allah haka Allah yake ikwanshi da raban zamuyi rayuwa cikin inuwa daya umma Daman Ni tin ranar da naganki uwa na daukeki

Murmushi umma tayi tace alhamdulillah yanzu hankalina yadada kwanciya tinda nasan inda ya’ta take aure nasan hannu nagari tashiga tasamu miji adali alhaji aliyu ga amanar ya’ta sadiya na baka ka rikemin ita tsakaninka da Allah

Yace insha Allahu na dauka Zan riketa tsakanina da Allah

Umma tace alhamdulillah ngd alhaji Allah yaiwa rayuwuwar auranku Albarka

Aminu yace Ameeen

Fita sukayi zuwa kofar gida abokan aliyu na ta kiranshi yazo Dole yabi aminu suka fita

Bikifa yayi biki gidan su sadiya yakacame da jamaa har wayanda baa gaiyacesuba du sunzo gane kwarkwatar idansu sadiya tayi goshin da Babu Yar da tataba yin irinsa acikin unguwarsu kowa mgnar shagalin auranta yake anci ansha Yan zaman banzan unguwa maza Nan aka tare akofar gidan su sadiya se fito musu da abinci ake kalla kala sunaci kowa yaci yakoshi har da meguziri da shi zuwa gida matan unguwa haka suke ta jidar abinci da fanfe suna kaiwa gida kowa yaci yakoshi harta almajirai sun,san ana auran sadiya baiwar Allah Albarka kuwa tashashi da fatan alheri wajan jamaa

su tala se Ido du akunyace suke gani suke kowa yasan irin zaman da sukeyi da umma da sadiya du sun tsargu dasuka karewa aliyu kallo sunyi mugun Raina kansu dagasu har yaransu sun,san sadiya tariga tamusu nisa Babu yanda zasuyi gawani mugun kwarjini da aliyu yaimusu Kayan da sukaga umma da yaranta na ta canjawa da sadiya bakaramin Kona musu Rai yaiba suka dada,jin tsanar umma da yaranta aransu

Sadiya wajan karfe biyu tatashi zazzabin jikinta yasauka garau tajita wani wankan Yaya tasata tayi aka Kuma tsantsara Mata wata kwalliyar tana saka Kaya mitin ashirin ajikinta cikanke basayi take canja wasu kayan kawaye har wayanda tamanta dasu sunzo wajanta ranar kawayanta da sukayi aure suka gujeta du ranar tagansu se borin kunya suke tamata suna Bata hakuri itadai murmushine nata kowance yanzu sotake ace itama kawar sadiyace

su Amira ana manne da sadiya har tsokanarsu mutane sukeyi kowa yagane ya’Yan mijintane har su tala da sukaji yaran mijintane sunji kunya su azatansu ya’Yan da tahaifane tintini ayawan da suke Mata kazafi na karuwanci ta haifesu daga baya sukaji ba haka bane

 

 

 

 

 

 

Kuyi hakuri ba sosai zakuna jina da wuriba abubuwanne se ahankali

 

 

 

Liltafina bana kudi bane du Wanda yasayarmin Allah ya,isa banyafeba ko ta siyarmin Allah ya,Isa ban yafeba du Wanda yacire sunana anovel Dina yasa nasu Allah ya’isa

 

 

 

 

 

 

New writer’s

Hakan take

*Husba’ahfama* ????????????

*Yar* *kwaliya* ???? ????????

 

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????????
????????????

????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????

????????????????
????????????
????????????

 

 

???????? *HALEEMATUS* *SADEEYA* ????????

 

Written by *HUSBA’AHFAMA*

 

IG **officiall_husba’ahfama*
Facebook *Real* *husba’ahfama*

Follow me on Wattpad @ *Real* *husba’ahfama*

 

 

*Bismillahir* *Rahamanir* *Rahim*

 

 

 

29-30

 

 

 

 

 

 

Karfe biyar na yamma motocin daukan amarya sukazo Yan biki kowacce burinta aje da ita Kai amarya Dan su gano irin daular da zaakai sadiya du jikin umma yamutu ganin kukan da sadiya take na rabuwa da iyaye Tasha nasiha da Kar aka rabasu da umma malam shima yayi Mata nasiha sosai malam da umma har mota suka raka sadiya motar da zaa dauki sadiya sabuwace dal aliyu yasiyota ko shiga be tabayiba sadiyace zata Fara budeta haka su malam suka,sata amota tana kuka abin tausayi Yan rakiya Suma suka shiga motocin sukaja suka tafi

du hadamar Yan Kai amarya motoci sun ragu wasu haka suka koma bakowa aciki gidan ummi aka Fara Kai sadiya aka Bata amanarta sannan aka shige da ita gidan aliyu ummi ba haka tasoba taso abar sadiya se dare ita da su Abbah su,rakata har gidanta wani tinani tayi ta canja raayi saboda su tala tace aje akai ta gidan mijinta kowa yagani

Gidan su ummi kadai da Yan Kai amarya suka gani da su tala sun girgiza da ganin kalar tsaruwar da gidan sirikan sadiya yayi abin yatsoratasu Basu Gama girgizaba se da sukaga kalar gidan mijin sadiya tindaga waje suka tsorata ana shiga cikin gidan sun girgiza tindaga Kan masu gadi da suka bu de musu suka shiga da jamian tsaro sukasan sadiya tagama warkewa tin Kan ashiga ainahin cikin gidan kowa yafara tofa albarkacin bakinshi da surutun tsaruwar gidan Basu Gama tsinkewaba se da aka shiga falan gidan aka bude musu dakuna sukaga aljannar duniya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button