Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

su tala hawayene ke ta zuba a idansu suna gogewa har da su zilai su asiya akazo kawo sadiya bakin ciki sun kunsa iya kunsa Dan sunyi mamaki Wai sadiyace a irin wannan arzikin lanlai in Basu dau matakiba se tamusu nisa

lami taiwa tala rada akunne wlh sadiya bata Dace da kalar gidannanba yaranmune suka Dace da irin gidan hutunnan kiga shegiyar yarinya a Ina ita da uwarta suka samo masu kudi haka malam ka tsokano Bala,I bakai Babu zaman lfy agama komai mutane su ragu wlh Kai da kwanciyar hankali yakare acikin gidanka yanzufa gudunmu yake bashima da lokacinmu se na matar me kudi sadiya da uwarta kiga yanda kowa yake San sadiya da Khadija da Yan uwanta Dan sun samu masu kudi wlh Dole mudau mataki mucire sadiya daga cikin gidannan Dole mijin sadiya da iyayan mijinta su dawo hannunmu itama sadiyar munafuka Taki yarda mu jata ajiki wani hade Mana Rai take

Tala tace kedai yishuru Kar mutane suji mu Kar ace bakin ciki muke kedai muyi ta washe Baki muna faraa Dan ace muma farinciki muke tayata mubar komai se mun koma gida mayi acan wlh bakiji zuciyataba niyar bugawa take karfin Hali kawai nakeyi

Habi tace hm akwai tashin hankali Bari Yan biki su watse

Yan Kai amarya sunsha kallo sunyi mamakin irin gidan da sadiya take ciki haka suka taho suka barta daga ita se su Amira

Daddy asibiti yaje wajan Malika da mommy llokacin yakira ummi yaji ko ankawo sadiya gidan
mijinta

ummi tace eh ankawota

yace alhamdulillah

Kai tsaye dakin da su malika suke yashiga Yana murmushi suna ganinshi sun San Yana cikin farinciki yace alhamdulillah alhamdulillah burina yaca yau Ina cikin farinciki du da naso kina gidansa Zan aiwatar da abinda nai niya in kin haihu se ma Allah yakawo me rabawa gaba daya yaraba Dana aliyu Allah yaimasa canjin alheri Allah yahadashi da zabinsa Wanda tadace da shi albishir nazo nai muku Dan haka nahana asallameku yanzu ina fada muku zaku tafi gida Dr ze Baku sallama albishir din shine yanzu Zan fada muku ga goro da alwa ku Shaida ga hotinan daurin aurenan ku gani ku sheda Amma gani kawai zakuyi kubani hotinana Dan suna da mahimmanci awajena

Mika musu hotinan yayi suka Fara kallah sadiya suka gani da aliyu sunsha kyau wani yasunkuyo kamar Yana Mata rada Daya suna kallan juna hotinane kala kala yabasu har da nasu abbah da suke kofar gida lokacin ana daura aure yaciro wayarshi yakunna musu video na daurin auran sadiya da aliyu alokacin ana daura auran yadauka duka yabasu suka gani

Gabansu yayi mugun faduwa sun girgiza sosai da ganin sadiya da aliyu Kuma suka tambatar aure aliyu yadaura Kuma sadiya yaaura

wani Kara malika tasaki tace daddy me hakan yake nufi kenan zargina Kan yarinyarnan gaskiyane Daman nemanta yake har takai ya aureta Ni aliyu yaci Amana daga sakina yaje yai aure wani irin kuka tafashe da shi na bakinciki

itama mommy jikinta yamutu tayi bakinciki da jin auran aliyu Kuma da Yar aikinsa auran da ko malika bewa hidima hakaba tace yanzu alhaji abinda kukayi kun kyauta aiwannan cin amanane karara yarinyar Yar aikin yarka kabari mijin yarka ya aureta Kuma baka hanaba na sanma ka temaka Akan auran yanzu wanna kucakar yarinyar yaaura yakashe Mata uwar dukiya haka ko malika be kashewa dukiya hakaba da ze aureta se kace Yar sarauta har da sisin gwal asadakinta ko malika bewa hakaba Allah ya,Isa mudai ancumu mun barshi da Allah malika Kuma se yayi mamaki akanta Nan gaba seyaga Wanda zata aura itama Nan da Dan lokaci se yaji labarin auran malika

Wata dariya daddy yayi yace tin yanzu har Kun Fara tsorata toku ina ruwanku da auransa da yayi ai bakwa kaunarsa bakwasan ko jininsa to Dan yayi aure me yashafeku aure dai an daura shi da HALIMATUS SADIYA Yar Albarka me hakuri da tarbiya da biyaiya yarinyarnan tamin abinda Yar cikina bataminba wannan yarinya na dauketa kamar Yar cikina da nahaifa Dan tafimin ke malika da kema uwar Malika tafiku sau dubu awajena albishir nagaba ke hajiya shine Allah yayarda Nima na angwance andauramin aure da Yar uwata tajini me Miki aiki Wanda tatashi da kaunata tin tana yarinya har Tai aure mijinta yarasu tadawo gidana da dazama take Miki aiki konace Kika maidata baiwa kike azaftar da ita da aiyuka kala kala Dan azaba ta isheta tagudu tabar Miki gida Dan karfin San da take min tajure tacigaba da Zama kina Bata wahala kinmai data kamar baiwa ga aiki ga zagi da cin mutunci du nasani na sharekine kawai lokaci nake jira Kuma yazo nayi aure da Yar uwata Aisha kema kije na sakeki saki biyu Allah yahada kowa da rabansa na alheri in Dr yasallameku bagidana zakuyiba Daya gidan nawa zaku koma can na kwashe kayanki gaba Daya nakai Miki kizauna da yarki da kikafi so fiye da kowa kema malika na kwaso Miki kayanki na gidan aliyu na Kai Miki can gidan da nabawa uwarki hajiya nabaki wannan gidanne Dan darajar yaran da muka Haifa tare da ke nabaki kinci Albarkacinsu Suma zasusan namiki adalci tinda da nasakeki har gidan da Zaki zauna nabaki ko dawasa Karku kuskura kuzomin gida in bahakaba hukumace zata rabamu da ku ke malika bani bake har abada kije duniya ta koya Miki hankali ko dawasa karki taba tunawa nine mahaifinki in kintunoni azuciyarki ban yafeba hajiya ga takardarki tasaki Ni natafi se wataran

Haka daddy yafice yabarsu da bakinciki azuciya

Wani ihu suka hada Baki suka kurma suka saki wani kukan bakinciki me cin Rai

mommy tace alhaji Ni ka wulakanta haka Kai da aliyu Kun wulakantamu yau Ni alhaji yasaka har saki biyu Kuma Wai Yar aikina ya aura Kuma Yar uwarshi Ashe shegiya mijina takeso tazo ta zaunemin agida wlh se Allah yasaka Mana Ni da ya’ta

Haka suka tantara kayansu suka fice daga asibitin suna koke koke

Yankai amarya sun koma gida da gidan sadiya abakinsu umma Tasha labari ita wata mgnar ma gani take karyane ba agidan sadiya ba se da su Yaya suka Bata labari sannnan tayarda

tace ba kyan gidaba kwanciyar hankalin ya’ta nakeso Kuma nake fata tasamu

Yaya take tagama samu insha Allahu

Ummi da abbah da daddy gidan aliyu sukaje sukai musu nasiha sosai shi da sadiya sannan sukai musu fatan alheri suka tafi gida har kofar gida aliyu yarakosu se da yaga tafiyarsu sannan yakoma cikin gida

Sadiya yagani azaune akasan kafet inda yabarta ta sunkuyar da Kai kasa har gabanta yatako yazo hannunta yakama yadagota daga inda take yamai dota Kan kujera shima yazauna kusa da ita kamshinta yashaka Me dadi Ido yarufe yaja numfashi sannan yadada bude idansa yasauka Akan sadiya da yaga hawaye na zuba a idanta

Yace ikwan Allah har yanzu kukanne be kareba amaryata gidanfa ba bakwanki bane kukan na menene ko kukan an hadaki da tsoho kikeyi ummu Walid ki fadamin gaskiya karki boyemin

Kai Tai saurin girgizawa

Yace to menene in ba hakanba ki fadamin kinji

Tace ba umma bace Babu rokwan da ban mataba tabarni ko sati na Kara agida Taki yarda kamarma yanzu basona takeba haka tasa aka taho Dani takara mgnar tana kuka

Kura Mata Ido aliyu yayi Yana murmushi yace tofa ummi Daman yar’taki Bata Gama girmaba kikai Mata aure kiyi hakuri to umma na sanki saboda mutane da sukeso suga gidanki tace kitafi naki gidan in ankwana biyu mutane sun Gama zuwa ganin gidanki Zan kaiki wajan umma kiyi sati biyu shikenan ko kuka yakare

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button