Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Kai ta daga Masa tahau goge idanu

Kai ya girgiza yace Ina yaran naki

tace sun kwanta bacci tin dazu

Yace to tashi kema kitafi naki dakin kije ki kwanta ki huta kibar su Amira anasu dakin suna kwana su kadai

Tace wlh bazan iyaba tsoro nakeji da su zanna kwana
.yace to naki dakin da aka hada Miki yazaai da shi

Tace in mun kwana anan yau Ni da su walid gobe se muje Daya dakin mu kwana

Yace to tashi kije se da safe

Tashi tayi tashige inda dakin su Amira yake

Sadiya tashiga wanka tafito daga ita se tawul tayi daurin kirji tana fesa turare kala kala ajikinta taji anturo kofa anshigo ta tsorata kurawa kofar Ido tayi taga aliyune yashigo kunyace ta kamata ba Kaya ajikinta

Kallanta yatsaya Yi ahankali yace tubarkallah Daman haka surar jikinta yake tana da gashi haka

Baki na rawa sadiya tace kayi mantuwane ko wani Abu kakeso na dauko maka

Ahankali yabata amsa kamar me jin bacci yace kazarki da nasiyo Miki na manta ban kawo mikiba gashi Leda Daya Taki Daya ta yaranki se da safe

Durkusawa tayi ta karba tace angode Allah yakara Budi

Da sauri yadaga Kai Yana kallanta abin da be tabajiba abakin malika yau sadiya yabawa Yar wannan siyaiyar take Masa godiya har da durkusawa yaji Dadi sosai azuciyarshi jiyayi wani farinciki yarufeshi yajuya yafita zuwa nashi dakin

Bayan yayi wanka yai Shirin kwanciya bacci yakwanta kasa bacci yayi tinanin sadiya yahauyi daga yarufe Ido ita yake gani da daurin kirji se godiyar da Tai Masa ta tsaya Masa arai har yasamu bacci ya daukeshi

Abangaran sadiya ma hakan take daga tarufe Ido aliyu take gani tace ikwan Allah yau Kuma ko Dan inajin tausayinsa sosai Akan wuyar da yasha azamansa da maman su Amira Allah sarki Wanda yatemakeni yakaini asibiti Babu raban na ganka gashi igiyar wani tahau kaina Allah yahadaka da alheri ako inah kake baccine me nauyi yai gaba da ita

Yanbiki kowa yakoma gidansa lfy angama taro lfy gida ya koma daga umma da yaranta se su tala da yaransu

Hakama gidan ummi yanbiki kowa yakoma gidansa lfy daga abokan aliyu har Yan uwan aliyu se na jiki da suka dada komawa ganin sadiya Yan uwan aliyu Mata da sukaje gai da sadiya yanda ta karbesu hannu binbiyu abin yamusu Dadi se yabanta suke suna murna Dan uwansu yanzu yayi aure yasamu Mata tagari da suka koma gida suka gayawa ummi matar aliyu na da kirki itama taji Dadi sosai

rigimace tatashi agidan su sadiya su habi malam sukasa agaba da safiyar Allah suka hanashi sakat se yagaya musu meyasa yake nuna bambanci atsakanunsu da umma yayiwa sadiya auran gata yaransu Kuma be musuba yakashewa sadiya kudi a shagalin auranta be kashewa yaransuba

Habi tace kudin da ka kashewa sadiya Yar gwal ai sun isa kabawa yaranka samari da suke zaman banza agida su Kama jari ga gali da idi da Hadi du Basu da abinyi baka Basu kudinba ka kashewa sadiya da uwarta Ni mamakina Daman kana da uwar kudinnan ka barmu muke yini agindin murhu muna Sanaa Dan murafa maka asiri kaima kullin kana bakin titi kana sai da Kayan Miya Ashe kasan me kake kana da kudi boyesu kake

Tala tace hm bar namiji munafiki habi Kuma inda zakisan munafurcine ai ita Khadija Bata Sanaa se sai da awara itama Kuma tinda sadiya tabar gidannan aka Dena yinta Ashe Daman shi yahanata sayarwa tinda yatara Mata kudin da zata aurar da yarta sadiya kiga irin kala kalan abincin da aka dinga dafawa anabawa mutane nama kamar yai kuka da bakinsa Kuma har yanzu da sauran Kayan abincin bikin kamar ma badau komai acikiba aka dafawa mutane Kuma mu Ashe cutarmu kayi kazuba Mana Ido muka aurar da ya’yanmu mata baka hanaba Dan kasan me kataka wlh muma se kabawa ko wacce nata kudin kamar yanda ka kashewa sadiya da uwarta muma se abamu tinda muma mun aurar da ya’ya Mata kabamu namu kudin muja jari ko kabawa yaranmu maza samari su Kama Sanaa da shi

Lami tace wannan mgn haka take Yar uwa malam Kai muke jira kashiga kafito da namu kudin kabamu muma muna da hakki akanka Wai bakuga Yar mulki na daki Taki fitowaba tinda tasan me tataka bakar munafuka me bakin Hali

Kan takarasa mgnar da takeyi malam yawanke lami da Mari har sau biyu

Yace Zan jure komai awajanku Amma Banda zagin Khadija Dan Batai muku komaiba hasalima ku bakwa gabanta Bata da lokacinku harkar gabanta takeyi ita zuciya daya take zaune da ku Bata nufin kowance acikinku da mugun nufi Dan haka Allah yadubu zuciyarta yakawo Mata mafita akan Sadiya kunsa sadiya da Khadija agaba Akan sadiya tayi kwantai batai aureba du Anwa kannanta da saanninta aure ita baai mataba du abinda kuke musu nasani har Bata musu suna da kuke awajan mutane nasani ita Bata kiraku munafukaiba se ku saboda tsabar munafurcinku se da kukabi kawayan sadiya da sukayi aure da iyayansu kuka hadasu da sadiya suka koma gudun sadiya suka Dena zumunci da ita se da takai unguwarnan tagagari sadiya du wannan bemukuba se da bakin cikinku yakwantar da sadiya ciwo har hawan jinine yakamata du saboda ku Allah yadubeta yayaye Mata Allah yakawo Mata miji itama tayi aure ta huta Amma du dahaka Dan Bala,I da bakinciki Baku bar sadiya da uwartaba wannan wace irin jarabace sokuke kusan yanda akayi harkar bikin sadiya da yanda akayi aka kashe kudi da akayi bikin sadiya da su to du bazaku saniba wlh Dan Baku isa ku San yaakayi komaiba Dan Baku da wanna matsayin wlh Dan fada,mukuma bashi da anfani kudi Kuma ankashewa sadiya da Khadija ku da yaranki baa kashe mukuba kuyi abinda zakuyi du Wanda taga ancucrta taga bazata iyazama da niba tatafi gidansu Nima narabu da jaraba Zan Aiko Mata da takardarata in Kuma sauri take ta tsaya na rubuta Mata nabata tatafi da ita ahannunta Dan taji dadin tafiyar gaba daya

Kowacce kus tayi takasa mgn

Lami tace Ni malam kamara saboda Khadija

Yace eh anmareki in kinji haushi kitafi gidanku Nima nagaji

Kowacce dakinta tashige da bacin Rai azuciya Babu damar mgn

Malam dakin umma yashiga yazauna yai shuru ransa namasa Kuna

Umma tace malam Dan Allah kanayin hakuri tinda kasan halinsu tinda kayi hakuri se yanzune bazaka iyayin hakuri da suba Ni banasan tashin hankali da kamusu bayanin yanda aka samu komai nabikin Dan azauna lfy su Dena zarginka

Yace Amma Khadija wlh kema wani lokacin kamar Baki da wayo Allah kema da yarinyace Sena dokeki yanzu ke baa gayawa shedanun mutanan,nan yanda akayi akayi bikin sadiyaba sun saki agaba suna Miki bakinciki bare Kuma anmusu bayannin komai to in hakane meye anfanin rashin sanar da su harkar bikin tin farko Kuma kome Zan Gaya musu bazasu yardaba sema suyi tamiki Gori da habaice habaice yanzu Kuma nine nake tare Miki fada da su bakeba

Tace malam tashin hankalin kullin Bashi da Dadi wlh Ni na gajine shekara da shekaru Abu yakici yaki cinyewa girma muke dadayi Amma abanza munki muhada kanmu mu zauna lfy bare yaranmu Suma su hada kansu Allah malam nagaji da bala,in matanka danhaka nadena kulasu ko sun yimin

Yace komai lokacine Khadija Kita hakuri da su Allah yai Miki Albarka

Abbahne yakira aliyu awaya yazo gida yasameshi Yana zuwa bayan sun gaisa

Abbah yace abinda yasa na kiraka matan wayanda ka kulle da mazajan kawayen su malika wayanda suke ta zaryar bani hakuri sunce sunje wajanka har sau biyu kaki sauraran,su kace mgn Bata hannunka tana hannun hukuma sunce sunje can wajan yansanda Suma sunce su baruwansu kace baka hakuraba Dan haka sun hada komai kotu zasu kaisu shine suke tabani hakuri nasa Baki a mgnar ka hakura a sakesu in anje kotu mutuncin wasu daga cikinsu ze zube Dan Allah kayi hakuri kabari asakesu ka janye mgnar zuwa kotu ai Suma sunsan shayi ruwane yanzu sun wahala sun gane cewa kudi bakomai yake maganiba sun gani da idansu kafisu ta kowana fanni danhaka bazasu Kara aikata irin hakaba daga gareka Kuma me hadawa taraba malikace silar komai Kuma yanzu bakwa tare Dan Allah kayi hakuri kasa asakesu ai sun huru haka sunfada sunji kadubi darajar matan da Kuma iyalansu du kansu da suke gida hankalinsu atashe yake

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button